Sashe 20
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta kan Abba ba, mikewa Mumy tayi ta fice daga palon, shi ma ya mike xai fita, Abba yayi masa wani mugun tsawa, juyowa yayi yana kallonsa a hankali yace "Abba xan je in dawo" Karfe hudu da rabi Junaid yyi parking a parking area din gidansu, ya dade xaune cikin mota yana danne dannensa a waya har sai da Humainah ta leko daga part din Mumy, ganin haka ya kashe motar ya fito ya kulle, wuce ta yayi ya bude kofa ya shiga, ta bi bayansa tace "Me kake cikin motar ya Ahmad?" Yace "Abinda kika sa ni" dariya tayi ta bi bayansa, ya xauna Palo yana kallon Mumy a hankali yace "Sannu da gida Mumy" tace "Welcome, kai dadin xaman mota kawae kake" murmushi yayi ganin Mumy ta huce gaba daya yace "Na gaji ne Mum" Humainah ta xauna kasa kusa da shi tace "Sannu da dawowa ya Ahmad" banxa yayi mata, fatima dake palon ma tace "Sannu da dawowa yaya" yace "Yauwa" sannan ya mike yace "Bari in je in yi wanka Mumy" Mumy tace "Ba gaisheka Humainah yi ba" yace "Gulma ce fa Mumy, da tana gaishe ni ne" Mumy ta hararesa yyi murmushi kawae ya nufi kofa, Humainah ma ta bi sa da harara, Yana shiga part dinsa yayi wanka ya dawo Palo yayi kwanciyarsa, yana son xuwa gidan El-Ameen amma bai ma san inda xae ce ma Mumy xai je gashi yana ta kiransa tun a gun aiki ya ki dagawa, ashe akwai ranan da xai ga disadvantage din rashin fitarsa, don da yana fita da Mumy baxa ta dinga querying dinsa ba idan yace xae fita yanxu, mikewa xaune yayi jin an bude kofar parlour, Humainah ta shigo ta tsaya daga bakin kofa tace "Mumy tace ka xo ka ci abinci" dauke kai yayi yace "Naji" ta karaso cikin parlour'n tace "ni da ita muka yi girkin, tuwo da vegetable soup" ya hade rai yace "Who ask yhu" dariya tayi tace "Toh don ma na gaya maka" ya tabe baki ya mike ya dauki wayarsa ya nufi kofa, mikewa tayi ta bi bayansa da sauri, sai da suka fita yace "Hajja fa?" Tace "Bata nan taje gidan kawarta yau, kasan gobe xa mu koma" ya kalleta yace "Wa yace maki tare xa ku koma, bayan Abban ki yace ya ba mu ke" hade rai tayi tana kallonsa tace "Wa yace maka haka" murmushi yayi ya bude kofar parlour'n Mumy ya shiga ta bi bayansa. Kasa ta xauna tana kallon Mumy tace "Mumy wae ba da ni Hajja xata tafi ba gobe?" Mumy tace "ba tace nan xata bar ki ba" hawaye ne ya cika idonta tace "A'a ae ni ban ce xan xauna ba" Mumy tayi dariya tace "Toh bari idan ta dawo sae ki gaya mata, Meye abun kuka" dariya Junaid yayi yace "Ae sai dai tayi na jini nan xata xauna ita da fatima da khadija" ta fashe da kuka tana kallon Mumy, Mumy ta hararesa tace "kaga wuce dinning ka ci abincin ka bana son haka" mikewa yayi ya nufi dinning yace "Yi hakuri Mumy" mikewa Humainah tayi xata fita daga parlour'n Mumy tace "Ina xa ki" tana goge fuskarta tace "Xan je in jira Hajja" Mumy tayi dariya tace "Ai yanxu xata dawo, xo kiyi xaman ki a nan ki jirata" bata tsaya ba tayi ficewarta a palon. Har aka kira Magrib Junaid na kwance palon Mumy duk ya rasa yanda xae ce mata xai fita, mikewa yayi ya nufi toilet din palon yayi alwala ya fita xuwa masallaci, yana dawowa ya nufi part din Abba sanin ya shiga yanxu, Hajiya ce a parlour'n tana jera masa abincin supper a kasan lallausan rug din tsakar parlour, ya karasa ciki kansa a kasa yace "Ina yini?" Hade rai tayi tace "Ka fita don Allah abinci xai ci ynxu" tsayawa kallonta yayi, dai dai lkcn da Abba ya fito daga bedroom dinsa, Abba ya karaso cikin palon yana kallonsa, karasawa yayi inda Abba ya xauna, ya xauna daga kasa shi ma, a hankali yace "sannu da dawowa Abba" Abba yace "yauwa sannu, ya aikin?" Har lokacin bai dago ba yace "Alhmdllh!" Abba yace "Gud! Daxu baka shigo gaishe ni da safe ba" shafa kansa yayi yace "Na shigo Umma tace kana bacci" Abba yace "Ohk, amma baka karasa bedroom ba" junaid ya gyada kai kawae, Abba yace "kafi kowa sanin bana baccin safe ae" shiru Junaid yayi bai kuma cewa komai ba, kallonsu kawae Hajiya keyi ta gefen ido tana jera abincin da take rai ba dadi don bata so haka ba, Abba ya sauko kasa ya jawo babban food warmer, ya dau plate xai dibi shinkafa, Junaid ya karba yace "Bari in xuba maka Abba" sake masa spoon din Abba yayi, ya dibi shinkafar da stew a gefe da cow meats, snn ya xuba masa vegetables a kai kamar yanda ake masa, Abba ya dauki wani spoon din yace "Bismillah" sai da Abba ya fara ci sannan Junaid ya debi shinkafar a hankali ya kai bakinsa, Hajiya kamar ta hadiye xuciya ganin ko ta kanta Abba bae bi ba, taunar abincin kawae junaid yake ba don yayi masa ba, banda girkin Mumynsa babu na wanda yake ci, girki in ba nata bane ko kallonsa bai yi, shiyasa a ko da yaushe take bata tym dinta tayi masa girki, a tare suka gama cin abincin da Abbansa, bai yi Mamakin sakkowan Abba da wuri ba don in dai suka hada sa da shi, bai daukan lkci yake kuma jawo sa jiki, kwata kwata baya fushi mai tsayi da only son din nasa, hakan ba karamin daga ma su Hajiya hankali yake ba, sun dai rasa yanda xa su yi da Junaid a gidan, a tare suka tafi masallaci sllhn Isha da Abba, sae da suka dawo ya ba Abbansa hakuri a kan abinda ya faru jiya, Abba yace "Its Ohk, ka dai kiyaye halshan ka nan gaba" yace "In'sha Allah Abba" sun jima suna hira da Abba sannan yayi masa sai da safe ya mike ya fita ya shiga part din Mumy, tana xaune palo tana kallo, ya xauna gefenta ya dauki remote xae canxa tasha, Mumy ta karbe remote din tace "ya haka, bari a gama program din mana" kallon Humainah dake kwance kusa da fatima yayi yace "Har kin hakura xaki xaunan kenan?" ta daga kai tana kallonsa bata tanka sa ba ta dauke kai, Mumy tayi dariya tace "babban kawai" bude kofa aka yi hade da sallama, Junaid ya kalli agogo jin muryan El-Ameen, ya ga tara da rabi, Mumy tace "Kai dai baka jin fitan dare koh El-Ameen" junaid yayi murmushi yace "Kin manta likita ne Mumy" El-Ameen ya karaso parlon ya xauna yana murmushi ya gaida Mumy, da fara'a tace "lfya lau bokon turai ya aiki" yace "Alhmdllh Mumy" Fatima tace "Welcome bro" yace "Thank you sis" kallon Humainah dake xaune hankalinta na gun kallo yayi sannan ya kalli Junaid, Mumy tace "baki gaida yayanki ba Humainah" ba tare da ta kallesa ba tana ci gaba da kallonta tace "Ina yini" idonsa na kanta yace "Lfya lau" hira suka dinga yi da Mumy, ganin hiran ba me karewa bace Junaid ya mike ya nufi kofa yace "Ina part dina in ka gama karyan" dariya Humainah tayi a karo na farko ta kalli El-Ameen da ya hade rai yana kallon Junaid, Mumy ma tayi dariyar tace "Ae dae ya fi ka wllh tun da har yana daurewa yayi karyar" Junaid dake bakin kofa ya saka dariya yace "Surutun fa iyakansa a gida Mumy, mutumin da ko magana bai iya yi ma mace ba a waje sai kame kame," El-Ameen yace "Ehh ae kai naga ka iya d'an rainin hankali" banda dariya bbu abinda Humainah ke yi Mumy da fatima na taya ta, Junaid ya juya ya fice daga parlorn yana murmushi, mikewa El-Ameen yayi yace "Bari in je Mumy" Mumy tace "Toh fatima xata kawo maku abinci" toh kawae yace ya fita, Part din Junaid ya nufa ya samesa xaune a parlor ya kunna Tv, El-Ameen yace "Yau ban gan ka ba, kuma I was calling tun daxu baka responding" Junaid yace "I wasn't in a gud mood ne yau" El-Ameen yace "Wacece wannan yarinyar dake xaune parlorn Mumy" Junaid ya kallesa yace "Ya aka yi" d'an sosa kai El-Ameen yayi yace "Umm, tana da kyau ne" dariya Junaid yayi yace really?" El-Ameen yace "What's funny, Allah tana da kyau" Junaid yace "Toh bari ta shigo" ko rufe baki junaid bai yi ba sai ga ta ta shiga palon da sallamarta rike da tray din abinci, El-Ameen ya sunne Kai murya can kasa yace "Don Allah ka rufa min asiri kar kace komai Junaid, wasa nake" Junaid ya fashe da dariya yace "Humainah" ae da sauri El-Ameen ya mike ya rufe bakinsa da hannu yana xaro ido, junaid ya dinga dariya yana tura hannunsa amma yaki sake sa, tabe baki tayi ta ajiye trayn hannunta tace "Mumy tace in kawo" da karfi Junaid ya tura El-Ameen yace "ke kin yi saurayi likita" ae ko rufe baki bai yi ba, El-Ameen yayi hanyar daki da sauri ya shige ya rufe kofar, Junaid ya dinga dariya har da rike kai, hade rai tayi tana kallonsa, can tayi tsaki ta juya ta fice daga parlon, kin fitowa parlor El-Ameen yayi har kusan Karfe goma, Junaid ya shiga dakin yace "Toh wai a haka xan baka kanwar tawa kana kunyar ta!" El-Ameen dake xaune gefen gado yace "ta tafi?" Junaid yace "Aa tana parlor" shiru El-Ameen yayi sai kuma ya mike ya cire shirt din jikinsa ya nufi bathroom, junaid ya bi sa da kallo yana dariya, wanka yayi ya fito sanye da bathrobe, ya nufi closet din Junaid ya fiddo pyjamas ya sa sannan ya dawo ya xauna yana kallon Junaid yace "Amma ba nan xata kwana ba dai koh?" Junaid ya hararesa yace "Nan din xata kwana" El-Ameen ya daga kafada yace "Ohk ni kam am spending the nyt here today, its late and bana son ta gan ni, I came purposely because of ur patient, they've diagnosed her, that is an mata genetic screening, brain scans, neurological exam i.e (checking of vision, hearing, and balance) and other tests,