← Book details Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 104

Sashe 50

Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read

cin komai ba, xaunawa yayi ya bude food warmern, ya ga shinkafa ne da miya, ya dau plate ya dibi kadan ya fara ci, kwata kwata bai jin dadin abincin a bakinsa, spoon hudu yayi ya ajiye ya jinginar da kansa jikin kujera, kwankwasa kofar parlon aka yi ya juya yana kallon kofar kauda kai yayi dai dai lokacin da aka bude, colleagues dinsa na gun aiki ne har su hudu dukkansu sanye da uniform suka shigo parlon, ya d'an bude ido yana kallonsu har suka karaso parlon, daya daga cikinsu Captain Umar yace "Ohh ko mu koma ne A.jay" Murmushi yayi yana shafa kansa yace "Uhnn it's surprising, sannun ku da xuwa" xama suka yi gaba daya, nan suka gaisa, Daya daga cikin su yace "sai muka ji bad news Ahmad" junaid yayi murmushi, Capt Umar yace "Toh ya jikin?" "Jiki Alhmdllh, tun da gashi har na dawo gida" duk suka yi masa Allah ya sauwake, mikewa yayi ya nufi fridge din dake parlon ya bude ya kawo masu ruwa da drink ya ajiye masu, sun d'an taba hira na minti sha biyar suka ce masa xa su koma, fruits da drinks suka ajiye masa yayi masu godiya ya rakasu part din Mumy su gaida ta, da fara'a ta tarbe su basu jima ba suka mata sallama suka fito, Umma da Hajiya sai kallonsu suke daga balcony, shi kuma bai ce su gaida su ba, yi ma yayi kamar bai taba ganinsu ba, hakan yayi mugun kona masu rai, ya raka frnds din nasa har waje gun mota, sannan ya komo cikin gida, part din Mumy ya tafi, duk suka bi sa da kallo ko wanne da tunanin da take a ranta, yana shiga parlon Mumy Hajiya ta sauke ajiyar xuciya tace "Yaro man kaza" Umma ta tabe baki tace "Ke yanxu kin yi farin ciki da hukuncin da Alhaji ya yanke kansa?" Hajiya tace "Ina fa nayi farin ciki, kika san warce xai aura masa? Kema dai kin san ba lallai ya xabi 'ya yanmu ba, na ma fi tunanin kila yace shegiyar Humainahn nan, kuma da mun shiga uku mun lalace..." Umma tace "Ba abun mu koma gun malam ba yanxu ya hada mu da k'ulli yace sai an barbada ko sai anyi wani abun daban asiri ya kuma tonuwa ga Hajja mayya a gida" Hajiya tace "Mu je ki ji ina da wata shawara Allah ya bamu sa'a wannan karan" mikewa Umma tayi da damuwa tace "Ameen" ta bi bayanta suka shiga parlor. Bedroom junaid ya shiga ganin Mumy bata parlor, ya karasa gabanta ya durkusa ba tare da ya bari sun hada ido ba, cikin sanyin murya yace "Don Allah kiyi hakuri Mumy, forgive me plss kar kiyi fushi da ni" jin bata tanka sa ba yasa ya dago yana kallonta, a hankali yace "Kin ji Mumy!" Tana kallonsa da kyau tace "Ka min wani abu ne?" Shiru yayi bai ce komai ba, tace "Toh baka min komai ba tashi ka fita" kasa tashi yayi, tace "Ka tashi na ce" a sanyaye ya mike ya fita daga dakin. Kallo daya yayi ma Humainah dake parlor ya nufi kofa ya fita, dai dai fitowar Hajja daga part din Abba, ya dauke kai kamar bai ganta ba xai wuce tace "Kai Amadi mu muka dauro maka hatsarin nan ne xaka wani dinga sha mana kamshi a gida don fitsara, to Allah shi kara, kuma ka tafi ka gaida ubanka Abubakar ya xo tun daga Abuja" yi yayi kamar bai san da shi take ba ya fara tafiya xuwa part dinsa, da karfi ta kwalo masa kira yanda tasan Abba xai ji cike da masifa tace "Ni din sa'ar uwar ka ce ina maka magana kake tafiya kake min tsaki, toh Muhammadu ka fito ka ga rashin kunyar da Amadi ke min gaban jama'a, don an maka gata an raba ka da gagarumar mahaukaciya sai ka dau gaba da 'yan gida..." Tsayawa yayi yana kallonta fuskar nan nasa a daure, tace "D'an banxa kawai, ka wuce ka gaida ubanka Abubakar nace" part din Abbansa ya tafi ta bi sa da harara, da sallama ya shiga parlon ya xauna kan carpet kansa a kasa ya gaida Small Abban nasa dad din Humainah, Alhaji Abubakar yace "Lafiya lau Ahmad ya jikin?" Junaid yace "Alhmdllh Abba ya hanya" "Hanya mun baro ta, ya aikin?" Cewar dad din Humainah yana kallonsa, Junaid yace "Alhmdllh" dad din Humainah yace "To Maa sha Allah" kallon Abbansa yayi yaga idonsa a kansa, yayi kasa da kai ya mike yayi musu sallama har ya kai bakin kofa Abba yace "Ka koma asibitin?" Girgixa kai Junaid yayi yace "Yanxu xan tafi Abba" Abba yace "Toh ka kira Abdul ya kai ka, ga makullin mota" komawa cikin parlon yayi ya dau makullin yayi masa godiya ya juya ya fita. shiryawa ya tafi yayi a part dinsa ya fito, sai da ya fara shiga ya gaya ma Mumy xai tafi asibiti snn ya fito ya tafi parking space ya dau motar Abbansa ya fita don xai iya driving din. Abban El-ameen ne ya duba sa da kansa a office dinsa, wani likita yayi masa allura ya basa drugs dinsa, ya kusa awa daya office din sannan dad din El-ameen yace xai iya tafiya ya dawo da daddare karban allura, godiya Junaid yayi masa ya mike ya fita daga office din, yana saukowa second floor ya tsaya yana kallon kofar office din El-ameen, karasawa yayi ya murda handle din door din ya tura, xaune ya gansa ya jinginar da kansa jikin kujerar da yake idonsa rufe, har ya karasa cikin office din bai sani ba, yayi knock din table din gabansa, da sauri El-ameen ya bude ido ya gyara xama, Junaid yace "Sleeping at work" El-ameen ya shafa kansa yace "Our run away patient" Junaid ya ja kujera ya xauna yana kallonsa yace "ka bani number mai gadin can gidan naka nasan baxai rasa sanin whereabout din mama jummai ba, El-ameen ya bude hannu yace " I don't have!" Junaid ya d'an bude ido yace "Da gaske?" El-ameen ya gyada masa kai, junaid yace "Toh yanxu ya xa muyi?" El-ameen yace "Na kai ta gidan old frnd dita Dr Sumayya" junaid yyi shiru kafin yace "har xuwa yaushe?" El-ameen yace "I told her kwanaki kadan xata yi, dama mijinta bai nan ne nasan xata rike ta but kasan halin su mata" Junaid ya sauke ajiyar xuciya yace "Or mu kai ta orphanage home kawai tunda dai hankalinta ya dawo" wani kallo El-ameen yayi masa yace "tunda ca tayi maka bata da iyaye ba, ko kuma ance maka manya suke dauka" Junaid yace "Toh yanxu kasan inda iyayen nata suke, ka sani ma ko suna da rai, kaga ni iya taimakon da nasan xan iya yi ma yarinyar nan kenan sbda parent dina, ba don su ba xan iya yi mata komai na taimako a rayuwa, I just can't keep on disobeying my mother, beside am getting married in 2wks time kamar yanda Abbana yace, to ya kake son inyi da 'yar mutane, ina xan kai ta idan ba orphanage home ba?" El-ameen ya lumshe ido ya bude hade da shafa kai yace "Aure xa a maka! Toh me xai hana ta xauna gidan ka tare da matar ka har memory dinta ya dawo junaid, last gatan da xaka yi ma baiwar Allahn nan kenan a rayuwa" junaid yayi shiru yana kallonsa can yace "Gidana kuma?" El-ameen yace "Yes, ko tare xaku tare da Mumy?" Murmushi junaid yayi yace "Idan matar bata yarda ba fa?" El-ameen ya hade rai yace "Gidan ubanta ne ko kanta xata xauna?" Junaid ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe idon yana naxarin shawarar El-ameen. *Haske Writers Association* [1/14, 9:12 AM] Elhajj: *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 40/41 Mikewa Junaid yayi yace "I will think about that!" Daga haka ya nufi kofa El-ameen ya bi sa da kallo har ya fita. A haraban hospital din suka hadu da faisal, faisal yace "Ohh my God, ashe abinda ya faru kenan captain shine ko ku sanar da ni kai da El-ameen? da Childishness din ku ne ya tashi da har gida xa ku xo ku sameni" junaid yayi murmushi yace "I thought ka sani ne ai," faisal yayi tsaki yace "Ta ina xan sani?" Daga haka ya bar sa nan tsaye ya shiga asibitin, murmushi junaid ya kuma yi ya shiga mota ya bar asibitin. Yana isa gida part dinsa ya tafi yayi alwala yayi sllhn asr sannan ya kwanta parlor, har ya fara bacci yaji an bude kofar parlon, bude ido yayi ya mike xaune da sauri, Humainah ce ta shigo parlon ta tsaya daga bakin kofa ta d'an hade rai tace "Xamu tafi tare da Hajja!" Yana kallonta yace "Ina xa ku" tace "Gidanmu!" Shiru yayi kafin yace "Ohk, yaushe xa ki dawo?" Ta tabe baki tace "Baxan sake dawowa ba, da kayana duka xan tafi ma" murmushi Junaid yayi yace "Ohk Allah raka taki gona" tace "Ameen" daga haka ta juya ta fice daga parlon, ya koma ya kwanta. Tana fita hajja ta shigo sabe da gyalenta da 'yar jakar da ta taho da shi, tace "Toh Amadi ni dai xan tafi sai kuma na dawo kai maka amarya ko kaki ko ka so sai in ga ta tsiya, idan har ynxu ra'ayin rayuwa da mahaukaciya kake to sai ka haukatar da warce za a kai maka hakan xai fi maka rufin asiri" daga haka ta juya ta fita ya bi ta da kallo hade da tabe baki, ranan da daddare Ummin El-ameen ta xo gidan, duk yanda ta so ya gaya mata ko El-ameen yasan komai kan xancen yarinya mahaukaciya kin gaya mata yayi yace babu ruwan El-ameen, ba don ta yarda ba ta kyalesa don tasan bakinsu daya, can tace "Na ji labarin aure xa ayi maka, saura abokin ka, shi wannan kauye ma xanje dauko masa mata wallahi xan basa mamaki," Dariya Junaid yayi yace "Kai Ummi, kauye kuma" bata tanka sa ba ta mike ta fice daga parlon. Shirye shiryen biki aka dinga yi gidansu Ahmad Junaid babu kama kafar yaro, cikin kankanin lokaci aka hada lefe akwati shidda, shi dai Junaid kallon ikon Allah kawai yake wai shi
Chapter 50 · 0% Book details