← Book details Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 104

Sashe 61

Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya ji jikinta yayi xafi, ta dago jajayen idonta tana kallonsa ta fashe da kuka tana rike da cikinta, ai bai san lokacin da ya hade ta da jikinsa ba, ba shiri ta hadiye kukan da take, xame jikinta tayi, ya mike da kyar yace "Am am sorry jasmine...." Kasa dagowa tayi sai hawaye, ya kama hannunta ta mike ta shiga bayi ta wanke bakinta ta fito ta kwanta, ya gyara gun aman ya dawo dakin yana kallon agogo, ya dawo kusa da ita yace tashi mu je asibiti, girgixa masa kai tayi da kyar tace "No ka kira uncle" hade rai yayi ya dau hijab dinta yace "tashi mu je nace" hawaye cike idonta ta mike xaune ta karba hijab din ta sa, kasa tashi tsaye tayi, hawaye na sakko mata tace "Baxan iya tashi ba captain" kallonta yake cike da tausayinta ya durkusa kusa da ita yace "Ina ke maki ciwo ne?" Cikinta ta nuna masa, sai kuma ta fashe da kuka ta koma ta kwanta, mikewa yayi ya fita xuwa dakin Humainah, har ta kwanta ya karasa ya kunna bedside lamp ta bude ido da sauri tana kallonsa ta mike xaune tace "Me ya faru?" Ya dan shafa kai yace "Plss asibiti xa ki raka mu in kai yarinyar nan amai take ta yi" hade rai tayi tace "Bacci ni xan yi, ka kira mata El-ameen mana" yace "No it's late yanxu kar a shiga hakinsa" wani kallo tayi masa tace "I see" ta koma xata kwanta ya rikota ta buge hannunsa tace "Leave me joor" rungumeta yayi yace "Haba wife taimako fa xa kiyi" turasa ta shiga yi tace "Ka rabu dani don Allah ni baccina xan yi" ganin kiss dinta yake son yi tace "Ohk naji naji, mu je" murmushi yayi ya saketa ta mike fuskarta daure ta dau hijab har kasa tasa ta fita ya bi bayanta, ba laifi ita ma ta tausaya ma Jasmine don da ganinta kasan tana jin jiki, tana rike da ita suka shiga motar, wani private hospital suka tafi, basu sha wahalan ganin likita ba, likitan na ta kallonsu har ya xaunar da ita sannan shi ma ya xauna, yayi murmushi yace "Couples?" Kallonta Junaid yayi da sauri ita ma ta kallesa suka hada ido ta dauke kai, ya dan wara ido yace "Ohh No! We are not" Likitan yace "Ohh sorry!" Murmushi kawai junaid yayi ya d'an saci kallonta, tambayoyi likitan ya fara mata junaid na bada amsa don kin cewa komai tayi, nan dai ya duba ta ya rubuta mata magunguna da allura sai test da ya rubuta xa a mata gobe da safe, malt junaid ya siya mata ta sha kafin a mata alluran sanin bata ci komai ba, fir taki yarda ayi mata tana kuka a rikice, junaid ya hade rai yace "Xaki sha mari fa, Meye a alluran" fixgota yayi ganin taki yin shirun, ya hade rai yana kallonta, da kyar ta yarda aka mata shima a cinya yana tsaye kanta, ta dinga ihu tana rusa kuka, yana rike da hannunta yana kallon yanda take kukan suka fito reception, dariya ma take basa, Humainah da dama bata bi su ba tana reception din xaune ta hade rai ganin yanda ya rike ta yana kallo, har suka shiga mota kuka jasmine take sosai, shi dai Junaid bai ce mata komai ba haka Humainah, ta gaji don kanta tayi shiru, suna isa guda Humainah ta bude motar ta fice, bin ta da kallo yyi sannan ya xaga ya bude motar ya ga shirun bacci tayi ashe, kiranta yayi murya can kasa ta bude ido a hankali yace "Fito" fitowa take son yi amma ta kasa, ta nuna masa cinyarta cikin tsarkewar murya tace "It's aching" kallon balcony yayi ya ga har Humainah ta shige, hannu ya mika mata ta kama sannan ya fito da ita, yana rike da ita suka shiga parlon, bai bari sun hada ido da Humainah dake parlon ba ya haura sama da ita, magungunanta ya bata ta karba ta sha yace "Toh kwanta ki yi bacci" girgixa masa kai tayi tace "Xan cire kaya" yace "Toh cire" mikewa tayi ta sauka ta cire hijab xata cire doguwar rigar jikinta yace "Noo tafi bayi ki cire" tace "Toh" sannan ta shiga bayin, kasa fita yayi daga dakin, har ta fito daga ita sai inner, xaro ido yayi ya kasa cewa komai bai kuma daina kallonta ba, tace "towel din...." Ai bai tsaya saurarenta ba ya fice daga dakin da sauri. Kayan baccinta ta dauka a closet ta sa sannan ta kwanta. Downstairs ya sauka ya kashe kayan wuta ya koma daki. Wanka yayi ya daura alwala ya shirya ya kwanta, sai dai ya kasa bacci har kusan sha biyu ya mike daga karshe ganin he's just deceiving his self ya fita, dakin Humainah ya shiga ya kunna wutan dakin, yayi mamakin ganinta xaune kan gado ta hade kai da gwiwa, dagowa tayi tana kallonsa da rinannun idonta, ya kashe wutan ya karasa da kyar ya xauna gefenta yace "What happened?" Sharesa tayi xata kwanta ya rikota ta fashe da kuka, ya rungumeta cikin sanyin murya yace "talk to me" turasa ta shiga yi ya ki saketa hakan yasa tayi lamo jikinsa hawaye na saukowa idonta, sun kusa minti goma a haka ya dago kanta yana kallonta da idonsa da suka kada murya can kasa yace "Kina da alwala?" Kin cewa komai tayi har sai da ya kirata, tace "na me?" Yace "Toh je kiyi" tace "Ni nayi" mikewa yayi yace "Ohk let pray" wani kallo take masa kafin tace "Na me?" yyi shiru yana kallonta, can ya mike ya hau darduman dake shimfide kasa yace "Am waiting" kin tashi tayi yace "Ke fa nake jira" da kyar ta sauka duk gabanta na faduwa ta dau hijab ta sa, raka'a biyu ya ja su, suna sallamewa ta mike ta haye kan gado ta shige cikin bargo ya bi ta da kallo, ya jima xaune kan darduman yana addu'o'i kafin ya mike ya dauke darduman ya nufi kan gadon ya xauna, cire bargon yayi ta mike xaune ta hade rai tace "Meye haka?" Ya hau gadon yana kallonta yace "Ina ruwana da ke kiyi baccin ki" kin kwanciya tayi da ganinta kasan a tsorace take, yayi murmushi ya kwanta ya juya mata baya, ta kusa minti biyar xaune kafin ta kwanta nesa da shi xata ja bargo ya koma kusa da ita ya jawota, ta fashe da kuka tace "Ya A.jay bacci fa xanyi plss" a hankali yace "Naji, yi baccin ki amma a jiki na" shiru tayi gabanta na faduwa can tace "Toh ni da bargo nake kwanciya" yace "Ga ki ga shi", bbu yanda ta iya haka ta kwanta ta rufa masu bargo tayi lamo ta rufe ido, sai da ya ga ta fara bacci ya cire bargon, ranan ta fadi ma 'yan garinsu bata taba tunanin haka Ya A.jayn yake ba, ba irin rokon da bata yi masa ba, bbu wanda bata kira masa ba barin Hajja amma duk a banxa abun ka da Novice da mai dacin ran tsiya, tuni baccin wahala da tashin sense yayi gaba da ita, shi kam rasa gane abinda yake ji game da ita a ransa yayi. Da asuba bayan ya dawo daga mosque duk ta daga masa hankali da kuka ita ya kira mata Mumy, ta kuma ki barin ya xo kusa da ita, ya ma rasa abinda xai yi, kyaleta yayi ya fita daga dakin, har xai shiga dakinsa sai kuma ya bude na Jasmine durkushe ya ganta can jikin gado tana kuka ya karasa ciki yana kallonta da mamaki yace "me ya faru kuma" kasa cewa komai tayi sai hawaye, ya durkusa kusa da ita da damuwa yana kallon idonta da ya kumbura don kuka yace "Cikin ne har yanxu?" Ta fashe da kuka ta kamo hannunsa tace "Captain it's still paining me, yana min ciwo sosai" ganin yanda ta rikice yasa hankalinsa ya tashi ya mike ya fita daga dakin ya shiga nasa ya dau wayarsa yayi dialing number El-ameen. Bugu daya ya daga, junaid yace "Pls come over yanxu" El-ameen dake kwance ya mike xaune yace "Me ya faru?" Junaid yace "Hurry up plss" El-ameen ya d'an bude ido yace "Toh fah" sai kuma yayi dariya yace "Kayi aika aika kenan, ba inda xan xo sai dai in turo maku nurse" Shiru junaid yayi d'an ya so ba shi dariya, yace "kaga bana son walakanci ina jiran ka" El-ameen yace "Allah ba da ni xa ayi wannan ba, me xan maku idan na xo?" Junaid yace "Ohk naji ka turo nurse din, but kai ma ka xo don baby ma bata da lafiya tun jiya" El-ameen ya mike tsaye yace "da gaske? Me ya sameta" Junaid ya katse wayar ya xauna ya shafa kansa, murmushi yayi yana mamakin sharp thinking irin na El-ameen, mikewa yayi da sauri ya fita ya koma dakin Jasmine, yanda ya bar ta haka ya sameta ya durkusa kusa da ita cike da tausayinta duk ta rasa inda xata sa kanta sai kuka take, da kyar tace "Captain ka ce Uncle ya xo plss" hade rai yayi yace "Baxan ce ba" kai ta gyada masa hawaye na sakko mata alamar to, can kuma cikin kuka tace "Ka ban Magani captain" hannunta ya kamo yace "Xa a kawo maki yanxu kin ji" ajiyar xuciya ya sauke jin shigowar motar El-ameen, bayan 3 mint ta fara kokarin mikewa tace "Uncle I want to ease my self" hade rai yayi jin tace uncle, ta mike da kyar tana duddukawa, mikewa yayi da sauri ganin abinda ke jikinta, ita ma ta kalli inda yake kallo, ai sai ta fasa ihu a tsorace tana kokarin daga rigar dai dai lokacin da El-ameen ya bude kofa ya shigo dakin, tana ganinsa ta kuma fashe wa da kuka tayi gunsa da sauri, shi ma kallon jikinta ya shiga yi, a rikice take cewa "Uncle kaga blood" xata daga rigar ya kama hannunta, ya d'an kalli Junaid ya ga shi yake kallo, a tare suka dauke kai, Junaid ya juya ya fice daga dakin, El-ameen ya kalleta da tausayi ganin yanda take kuka a hankali yace "Yi hakuri kin ji jewel" wayarsa ya ciro ya
Chapter 61 · 0% Book details