Sashe 60
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
iso balcony din xata shiga ciki Junaid da ya wani hade rai yace "Come back here" dawowa tayi tana kallonsa, yace "Cire abun nan na hannun ki ki fita a nan" kallonsa take kamar bata gane me yace ba, ya mike yace "Nace ki cire" komawa baya tayi a d'an tsorace ta cire plastern ta jefar yace "Leave" parlon ta shiga ya koma ya xauna. Kuka tayi ba kadan ba a bedroom daga nan bacci ya dauketa. Sha daya saura junaid ya shiga parlor ya haura xuwa dakinsa, wanka yayi ya shirya ya fito yayi kwanciyarsa a parlor, can kuma ya mike ya koma sama, ya dde tsaye a corridor kafin ya tura kofar dakin da Jasmine take a hankali, kwance ya ganta tana bacci, ya shiga dakin ya karasa kan gadon ya durkusa yana kallonta, yatsanta ya kamo yana kallon inda ta yanken, ta bude ido a hankali, tana sauke idon kansa ta mike xaune da sauri, kamar bai son magana yace "Is it still paining you?" Girgixa masa kai tayi yace "Ohk! Sorry!" Ta gyada masa kai, yace "Toh kwanta" ba musu ta koma ta kwanta ya mike tsaye yana kallonta, wanda hakan yasa ta rufe ido da sauri. Kasa barin dakin yayi har bayan kusan minti goma ya ji an danna bell, ta bude ido tana kallonsa, murmushi yayi ya juya ya nufi kofa ya fita ya kulle sannan ya sauka downstairs, still yayi bakin kofa bayan ya bude yana kallon Mumynsa, ta hade rai tace "Meye haka?" Murmushi ya kirkira yana shafa kai yace "I i i was surprise ne" shigowa parlon tayi ya bi bayanta gabansa na faduwa. Tana xaunawa ya xube nan gabanta yace "Sannu da xuwa Mumy, ina yini?" Tace "Lafiya lau, ya kuke" yace "Alhmdllh wllh Mumy" yana yi ne yana kallon stairs kamar munafuki, can ya mike da sauri yace "Bari in kirata" ita dai bata ce komai ba ta bi sa da kallo don ko ba a gaya mata ba ta san bai da gaskiya wannan kame kamen, yana haura wa sama ya bude dakin Jasmine suka kusa cin karo tana kokarin fitowa, xaro ido yayi ya ja ta suka koma dakin yace "Ina xaki?" Tace "Ruwa" ya xaunar da ita xuciyarsa na bugawa yace "No xan kawo maki anjima, you know what kar ki sake ki fito yanxu kin ji koh?" Shiru tayi tana kallonsa, yace "Jasmine!" Tace "Uhm!" Yace "I said kar ki fito plss kin ji, kwanta kiyi baccin ki," toh kawai tace ta koma ta kwanta ya mike ya fita ya kulle dakin, dakin Humainah ya shiga ya duba ya ga ba ta, ya jima tsaye kafin ya juya ya fita ya koma parlor, xaune ya ganta kusa da Mumy kamar xata shige jikinta, Mumy na kallonsa tace "Da ina ka tafi" ya buda ido yace "Na je kiranta ban ganta ba Mumy" Mumy ta dauke kai tace "Kaji da abinda kake kullawa, kawai mutum ya maida kansa munafuki, ya dauko wasu halayyen da ba nasa ba" murmushi Humainah tayi don abun ya bata dariya ta mike ta tafi kitchen don dauko ma Mumy drinks, shi kam kasa karasawa cikin parlon yayi don gani yake kamar ta gano sa ne, tana kallonsa strictly tace "What are you up to Ahmad?" Kamar zai mata kuka yace "Nothing mum, just xuwa aikin da bana yi kwana biyu ne naji daban" hararan shi kawai take yayi murmushi ya karaso cikin parlon ya xauna gefenta ya mata side hug yace "I miss you Mumy, har xaxxabin rashin ki fa nake" kallonsa kawai take ganin yanda ya rame idanuwansa suka fito, ya langwabar da kai yace "Mumy" tace "Baka cin abinci ne?" Girgixa mata kai yayi yace "Ina ci Mumy, kewar ki ne kawai" tace "Toh ku koma can gidan" wara ido yayi yace "Koh Mumy? Toh xa mu koma" a zahirin gaskiya kawai ya fadi haka ne don xancen ya wuce kuma gaba daya hankalinsa na kan Jasmine, Humainah na shigowa parlon da drinks ya mike yace "ina xuwa Mumy" daga haka ya haura sama, a hankali ya bude dakin ya ganta xaune a kasa, ya karasa da sauri yana kallonta ya durkusa yace "Me kike a nan?" A hankali tace "Ruwa xan sha" yace "Yi hakuri bari in kawo maki yanxu" mikewa yayi ya fita ya shiga nasa dakin ya dauko goran ruwa ya fito ya dawo dakin, da kansa ya bata ta sha, yace "Toh koma kan gado" ta mike ta koma gadon. [1/14, 9:17 AM] Elhajj: *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 52___53 Jasmine ta bude ido tana kallon El-ameen tace "Uncle ya tafi" El-ameen bai ce komai ba sai bin motar junaid da yayi da ido, can yayi murmushi ya kalli gate din gidansu sannan ya kalleta yace "Mu je" tafiya ya fara yi ta bi bayansa yana yi yana kallonta har suka iso titi, ya tsaida adai daita ya sa ta shiga sannan shi ma ya shiga, tara da 'Yan mintuna Mai adai daitan yayi parking bakin gate kamar yanda El-ameen ya umarce sa, fitowa yayi ita ma ta fito ya fiddo dari biyar ya mika masa sannan ya shiga gate din ta bi bayansa kamar xata yi kuka ganin inda suka dawo, junaid na tsaye balcony har suka iso, El-ameen ya kalli Jasmine da ta ki shiga parlon yace "Tafi ki kwanta gobe xan xo in tafi da ke" kai ta gyada masa hawaye cike idonta tana kallonsa, gyada mata kai yayi yace "Yeah", daga ita har shi bbu wanda ya kalli junaid ta juya ta shiga parlon shima ya juya ya nufi gate, wani irin kallo junaid ya bi sa da shi har ya fita, sannan yayi tsaki ya juya ya shiga parlon, yana haurawa sama ya shiga dakinsa. Washegari Tuesday misalin sha biyu yana daki yana danne dannen laptop tun bayan da ya fita sallahn asuba bai kuma sauka parlor ba kuma idonsa biyu yana jin jasmine na ta sallama bakin kofa bai tanka ba, ita kuma bata shigo ba, muryoyin da yake ji parlor ya sa shi mikewa da sauri ya fita ya sauka downstairs, tsaye yayi bakin stairs din ya wani hade rai yana kallon wa enda ke parlon, Fatima ce da khadija sai Humainah, ga kuma jasmine dake xaune kan rug da plate din abinci gabanta, gaba daya kallonta suke barin fatima da idanuwanta suka kara girma don kallo, kallo daya Humainah tayi masa ta dauke kai, fuska a daure ya karasa cikin parlon yana kallonsu khadija yace " With whose permission ku ka shigo min gida?" Khadija tace "Mumy ce tace mu xo mu taya...." Wani mugun kallon da yake mata yasa ta yin shiru ita ma ta hade rai, fatima kam dama bata dago kai ba, ya juya yana kallon Humainah yace "Kika bude masu kofa without permission dina koh?" Tabe baki tayi bata ce komai ba, kallonta ya tsaya yi na kusan second goma sannan ya juya yana kallon Jasmine da ta kasa cin indomien jin yana masifa, da ganinta kasan a tsorace take, tun kan yace komai muryarta na rawa tace "Ina jin yunwa ne shine na gaya ma Anty ta ban indomie" yace "Tashi ki bar parlon nan" mikewa tayi xata tafi sama ya dawo da ita yace "Dauki abincin" ta durkusa ta dauka ta wuce. Yana kallon kannin nasa yace "Kun san Allah if I shud hear a word daga bakin ku a kan komai na gidana xan maku abinda ban taba ba, nd I mean it" daga haka ya juya ya koma sama. Bayan Azahar su fatima suka bar gidan duk da ba haka Humainah ta so ba, sun dai samu ya basu kudin mota, sama ta haura bayan tafiyarsu ta shiga dakinta, bude kofar aka yi ta juya da sauri ta ga Jasmine, karasowa cikin dakin tayi hawaye cike idonta tana kallon Humainah a hankali tace "Anty cikina na min ciwo" ido Humainah ta xuba mata can tace "Kin ci abincin da na baki?" Girgixa kai tayi tace "Amai xan yi idan na ci" Humainah tace "A'a ki je ki ci dai....." Hawayen dake makale idonta ya gangaro tace "Anty ki kira min uncle in gaya masa" Humainah bata ce komai ba har sai da Jasmine tace "Kin ji" gado ta nuna mata tace "Toh xauna ina xuwa" Jasmine ta xauna ita kuma ta juya ta fita, dakin junaid ta shiga ta gansa kwance idonsa lumshe, lallabawa tayi ta karasa gun da wayarsa yake ta dauka ta fita, tana fita ya mike ya bi bayanta, tana tsaye dakinta tana kokarin dialing number El-ameen ya shigo, still tayi tana kallonsa sai kuma ta hade rai, kallo daya yayi ma jasmine ya fixge wayar yana kallon wanda take kira, da sauri ya katse yana mata mugun kallo yace "Kee!" Turo baki tayi tace "Toh ita ce tace in kira mata" juyawa yayi yana kallon Jasmine da tayi mugun tsorata, ya kuma kallon Humainah ya hade rai yace "Ki bar min irin haka a gidan nan, ke xata gaya ma ki kira mata shi... Are you on ur senses?" A hankali Jasmine ta mike xata fita ya fixgota, kuka ta saki tana kallonsa yace "Me xa ki ce masa?" Muryarta na rawa tace "That my tummy is aching" wani kallo yayi mata yace "Yayi abinda yafi aching din ma, fita daga nan" da sauri ta fita, shima ya juya ya fice, Humainah ta tabe baki ta rufe kofarta. Har dare Jasmine sai juye juye take a daki, tayi kukan har ta gaji, yana son xuwa gun ta amman bakin hali ya hanasa Lol, duk ya rasa sukuni har kusan karfe tara, mikewa yayi ya fita ya shiga dakin Humainah ya sameta xaune gaban mirror tana danne dannen wayarta yace "Kin bata abinci?" Ba tare da ta kallesa ba tace "yana kitchen ai" juyawa yayi ya fita xai koma dakinsa, tsaye yayi bakin kofarsa ya kasa shiga dakin yana kallon dakin da take, karasawa yayi ya tura kofar a hankali dai dai lokacin da ta mike xata bayi da saurinta, bin ta yayi da kallo sai kuma ya ga ta durkushe nan bakin kofar ta fara kwararo amai, shiga dakin yayi da sauri ya isa kusa da ita ya durkusa ya dagota yana kiranta, sosai