Sashe 59
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
ido yana kallo, bata sake bude idon ba kuma har daya saura, ya mike a hankali ya kashe Tvn, ya fita daga dakin ya bar kofar a bude ya shiga nasa dakin, kasa bacci yayi sai juye juye yake ya rasa dalili, daga baya dai ya gano dalilin ya kawar da shi daga ransa yayi forcing kansa yayi bacci. Washegari Monday yaji da ma kawai yayi resuming aiki duk da hutun sati biyu ya dauka but sbda Jasmine yasa bai yi haka ba, yana dawowa daga masallaci ya shiga dakin Humainah ya ganta xaune kan darduma, juyawa yayi ya fita dakin ya shiga wanda Jasmine take, har lokacin ya ga bata tashi ba, dukawa yayi dai dai fuskarta yace "Jasmine" ta bude ido da sauri mikewa yayi yace "Tashi kiyi sallah" ta gyada masa kai ta sauka daga kan gadon ta nufi toilet. Ya juya ya fita daga dakin. Karfe takwas saura Humainah ta fito ta sauka downstairs ta shiga kitchen, tsaye tayi tana tunanin abinda xata hada for breakfast, can dai ta fiddo Irish ta fara ferewa, ko da junaid ya sauko don siyo masu breakfast yayi mamakin ganinta a kitchen, ya tsaya daga bakin kofar kitchen yana kallonta, yace "Gud morning" ba tare da ta kallesa ba tace "Ina kwana" murmushi yayi ya juya ya fita daga kitchen din. Yana xauna parlo Jasmine ta sauko da alamar tayi wanka don ta canxa kayan jikinta, kusa da shi ta durkusa tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Nayi wanka" ya gyada mata kai yana nuna mata kitchen yace "Tafi ki gaisheta ki taya ta aiki" tace "Toh" sannan ta mike ta nufi kitchen din ya bi ta da kallo ganin yanda take tafiya. Kallo daya Humainah tayi mata ta dauke Kai, ta karasa kusa da ita ta durkusa a hankali tace "Ina kwana" ba tare da ta kalleta ba tace "Lafiya lau" shiru Jasmine tayi can kuma tace "I want to help you" mika mata wukar Humainah tayi ta ta tafi gun gas xata kunna, jasmine ta dau dankalin daya ta rasa yanda xata fara fere shi, kallon Humainah dake kokarin dauko mai tayi sannan ta fara fere dankalin ihu ta fasa ta jefar da wukan jin wani xafi da ya ratsa taMikewa Junaid dake xaune parlor yayi yana kallon kofar kitchen din jin Ihun, Humainah ta ajiye man hannunta ta taho da sauri tana kallonta tace "Dama baki iya ba....." Jasmine ta fashe da kuka q rikice tana yarfe hannu ganin jini a hannunta, Shigowa kitchen din junaid yayi ya hade rai yana kallon Humainah, hade ran ita ma tayi ta juya ta koma ta ci gaba da aikinta, Jasmine ta karasa kusa da shi tana kuka tace "Captain kaga blood din" kama hannunta yayi suka fita daga kitchen din Humainah ta bi su da kallo ta gefen ido. Sama ya tafi da ita xuwa dakinsa ya sa ta xauna bakin gado ya dauko tissue yana goge mata jinin dake ta xuba, ganin yanda take kuka yasa yace "Sorry!" Ta fashe da wani sabon kukan tace "It's paining me" kallon yatsan nata yake, ido ya lumshe a hankali ya sunkuyo dai dai kan yatsan yana hura mata iska, itama lusmshe idon tayi tana jin d'umin iskar da yake hura mata, har ya d'ago idonta na a lumshe, cute face d'inta da eye lashes d'inta ke kwance ya k'urawa ido, a hankali itama ta bud'e manyan idanunta ta sauk'e kan face d'inshi, cikin wani irin murya yace "Does it still hurt?", a hankali ta gyad'a mishi kai, spirit d'in da ya saka jikin wool d'in ya d'auko yasa mata kan yatsan, ido ta rintse ta saki k'ara tareda k'ank'ame mishi hannu tana haawaye. *Haske Writers association* [1/14, 9:17 AM] Elhajj: *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 51..... Sake mata hannun yayi yana kallonta ganin yanda take kuka, ta girgixa masa kai tace "Bana so" ajiye Cotton wool din yayi yace "Ita ta yanka ki?" Girgixa masa kai ta kuma yi tana hawaye tace "Knife ta bani" bai kuma cewa komai ba ya mike xai fita, tace "Ka kira min uncle ya xo" juyawa yayi ya kalleta, tana hawaye tace "Call me Uncle" wani kallo ya mata ya fice daga dakin. Haka tayi ta xama ita kadai tana kuka tana yarfe hannu, da ta ga jinin ya fara xuba sai ta goge jikin farin bedsheet din, gajiya tayi da xaman ta mike ta fita daga dakin har lokacin tana hawaye, dakin da take ta shiga ta kwanta. Karfe tara Humainah ta shigo dakin rike da cup din tea da plate din potatoe da kwai ta ajiye mata, Jasmine ta mike da sauri tana kallonta da idonta da suka rine don kuka tace "Anty ki kira min uncle" tsayawa kallonta Humainah tayi, sai da ta sake maimaitawa sannan tace "Waye Uncle?" Jasmine ta goge hawayen idonta tace "Wannan uncle din nan nawa da ya tafi" shiru Humainah tayi can dai tace "Ohk" ta juya ta fita ta shiga dakin Junaid, wayarsa ta dauka ta fito ta dawo dakin da Jasmine take, number El-ameen ta dinga nema a wayar amma bata san da sunan da ya sa ba, call log ta shiga tana dubawa taga wani number da yasa My best, dialing tayi tana sa ran shi ne, bugu uku aka daga, daga daya bangaren El-ameen yace "ya?" Mika ma Jasmine wayar Humainah tayi, Jasmine ta karba tana kallon wayar, Humainah tace "Ki sa a kunne" Kai wa kunne tayi ta ji muryar El-ameen yana cewa "Captain" ta d'an bude ido tace "Uncle!" Shiru El-ameen yayi kafin a hankali yace "Baby" fashe wa da kuka tayi ya mike xaune daga kwancen da yake yace "Me ya faru baby" tana shessheka tace "I've hurt my self" yace "Where?" Tana kallon yatsan ta tace "My finger" yace "With what?" Ta kalli Humainah da ke ta kallonta tace "Knife" shiru yayi sannan a hankali yace "Sorry, an baki magani?" Ta girgixa masa kai tace "No, and it still hurt" yace "Ina Captain din?" Ta goge hawayen idonta tace "I don't know" yace "Toh wa ya baki waya?" Ta kalli Humainah tace "That Anty" yace "Where is she?" Pointing dinta tayi kamar yana gani tace "she's here" yace "Toh bata phone din" mikewa tayi ta mika ma Humainah wayar ta karba, El-ameen yace "Kin tashi lafiya?" Humainah tace "Alhmdllh" yace "Wai yankewa tayi?" Ta kalli Jasmine tace "Eh ta yanke ne" yace "Da girma wajen?" Ta kuma kallonta tace "Not dat deep amma jinin bai tsaya ba" El-ameen yace "Toh xan xo" daga haka ya katse wayar Humainah ta juya ta fita daga dakin, Jasmine ta fashe da kuka ganin hakan ta dinga rerawa. Goma saura El-ameen ya shigo gidan, junaid dake xaune balcony tun bayan fitarsa dakinsa ya dinga kallonsa har ya karaso balconyn, El-ameen ya ja kujera ya xauna yace "Next week xaka yi resume kenan" ba tare da Junaid ya kallesa ba yace "Seem so" El-ameen ya shafa kansa yace "Ashe baby yankewa tayi wai" kallonsa Junaid yayi da sauri, can ya kauda kai yace "Who's dat?" El-ameen yace "Ka fi ni saninta ai" junaid yace "Tun safe nake nan so I don't know" El-ameen yace "Ohk, can I go in?" Junaid yace "Da can tambayata kake idan xaka shiga?" Shiru El-ameen yayi bai ce komai ba, can ya fito da wayarsa sai kuma ya tuna bai da number Humainah, number Junaid din yayi dialing, Humainah dake ta masa dube dube a wayan dake cike da texts din mata yafi 50 a ciki sai dai duk bata ga wanda yake reply ba, whtspp ma haka sai dai yayi reply da sure! yeah! Lol! Ita dariya ma abun ya dinga bata, tana d'aga kiran El-ameen yace "Humainah bring her out ina waje" Humainah tace "Ohk" ta katse wayar ta ajiye ta fita ta shiga dakin Jasmine din, kwance ta ganta inda ta barta bacci ya dauketa, karasawa tayi ta shiga tashinta, Jasmine ta bude ido a hankali tana kallonta, Humainah tace "Uncle din ya xo" mikewa tayi da sauri daga kan gadon tana kallonta, Humainah tace "Yana waje" kofa ta nufa Humainah ta bi ta da kallo har ta fita, kalle kallen parlor ta shiga yi bata gansa ba, hakan yasa ta nufi balcony kamar xata yi kuka, ido hudu suka yi da shi, ta karasa kusa da shi da gudu ta duka kusa da shi tana kallonsa tace "Uncle ka xo" kallonta kawai junaid ke yi ta gefen ido, El-ameen dake kallon hannunta ya ga inda ta yanke yace "Yeah na xo" mika masa hannun tayi kamar xata yi kuka tace "Look" ya kama hannun yana kallon yatsan murya can kasa yace "Sorry, but me kike yi da wuka" ta kalli Junaid hawaye ya cika idonta sai dai bata ce komai ba, kallon Junaid din yayi shi ma ba tare da ya ce komai ba, ya mike ita ma ta tashi tsaye, gun mota ya nufa da ita junaid ya bi su da kallo, suna isa gun motar ta wara ido cike da murna tace "Uncle are we leaving, bari in dauko jakana da hijab" bai ce komai ba ya bude motar ya dauko plaster ya fito yace "Toh shiga" ba musu ta shiga ta xauna, ya yanki plastern ya kamo hannunta ya rufe gun da ta yanken, sai kallonsa take, yyi mata murmushi yace "Xai warke kin ji" kallonsa take kamar bata gane me yace ba, ya buda ido yace "It will heal" a hankali tace "Ohk!" Magani ya dauko a motar ya mika mata ta karba yace "You take one yanxu kinji?" Kai ta gyada masa, ya koma baya yace "Toh fito" kamar xata yi kuka tace "Are we not going" yace "Anjima ne ba yanxu ba" hawaye ne ya cika idonta ta fito daga motar, yayi murmushi yace "Anjiman ma baxan xo ba idan kika min kuka" share hawayen tayi a hankali tace "Na daina" wani chocolate ya dauko a motar ya mika mata yace "Toh gashi ki tafi" ta karba ta juya ta fara tafiya ya bi ta da ido, sai a snn junaid ya dauke ido daga kallonsu da yake, El-ameen ya xaga ya shiga motarsa yayi horn aka bude masa gate ya fice, tana share hawayen ta ta