← Book details Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 104

Sashe 2

Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read

ganin ko xata iya kuncewa, hawaye ne ke sakkowa daga idonta, jikinsa ne yyi sanyi yana kallonta, lkci daya tausayinta ya ratsa sa, a hnkli ya shiga kakkabe hannunsa, idonsa ya kai kan goshinta da har ya gaji da fidda jinin da yake ya daskare, ya girgixa kai yana kallon samarin yace "Ku taimaka a sa min ita a mota in kai ta a duba goshinta" 'yar dattijuwar daxu tayi wani k'ara tace "Wani asibitin yaro? Ynda Duniyar nn ta dawo ba gskya ynxu, kai waye? Kuma d'aga wani anguwa kake?" Nan jama'a suka fara cece kuce a wajen ana kallonsa, shiru yyi bae ce komae ba, can ya sauke ajiyar xuciya ya juya ya nufi motarsa cikin rashin kuxari, nn aka bi sa da kallo ana cewa "Kun ga rashin gskyar knn, don da yana da ita da dole xae tsaya ya amsa tambayoyin da aka yi masa, kaiii Allah ya raba mu da sharrin mutum" shi kam motarsa ya shiga ya ja ya bar wajen, nan aka fara watsewa kowa na fadin albarkacin bakin sa, wani tsoho ne ya karasa ya kunce mata daurin yana d'an ja da baya kadda ta cafkesa har ya gama ya bar wajen bata d'ago ba bare ta kallesa. *Haske Writers Association* *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 2.... Junaid na isa gidan su El-Ameen yyi parking daga waje ya shiga, Sumayya kanwar El-Ameen ya samu xaune falo da kawayenta biyu, ya karasa cikin falon cikin tafiyarsa ta k'asaita, yi tayi kmr bata gansa ba ta ci gaba da ba kawayenta labarin da take, gaida shi kawayen nata suka yi suna kallonsa, don Capt Junaid ko namiji bae masa kallo daya, ya amsa gaisuwar su ba tare da ya dube su ba yana kallon Sumayyar yace "Ke yayanki na gida?" Ba tare da ta kallesa ba tana yatsine fuska tace "Nima bn sani ba" wayarsa ya ciro aljihunsa ya shiga kiransa, Kawayen nata biyu duk suka xuba masa ido, El-Ameen na d'agawa Junaid yace "are yhu at home?" El-Ameen yace "Yea are you coming?" Wani kallo ya watsa ma Sumayya ya katse wayar ya nufi dakin El-Ameen, Husnah ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Kai Sumayya waye shi, ya hadu wllh, don Allah ni dae ki hada ni da shi, yyi min ni dae plss" Sumayya tayi dariyar rainin hnkli tace "Uhm Kinga gayen nn irin mace masa da nake a da, na so shi kmr raina amma he looked into my face nd told me baya sona, I cried my life dat day, gashi i downgraded my sef telling him I love him" bude baki duk suka yi suna kallonta, Fiddausi tace "Tabdi! Toh meye hadin ku da shi? D'an uwanku ne?" Tsaki Sumayya ta ja ta dauki lemon gabanta ta shiga sa. Xaune ya samu El-Ameen kan laptop da siririn farin glass a idonsa yana danne danne, El-Ameen ya kallesa yace "Uhnn! Our great Capt Ahmad Junaid Murnai, kaga yanda ka kara kyau ka koma kamar wani Egyptian kuwa" Junaid ya tabe baki ya xauna gefen makeken gadon dakin yace "You will neva change" El-Ameen yyi murmushi ya tura laptop din gabansa ya juya yana fuskantarsa yace "I missed you a lot frnd, am glad you are back" Junaid ya shafa kansa yace "Sai kace gaske," El-Ameen ya kura ma farin shirt din jikinsa ido yace "Wait! Ciwo ka ji Captain" Junaid ya kalli shirt dinsa da sauri ya ga jini daga gefen shirt din, El-Ameen ya mike yace "What's dat? The shirt looks dirty ma" girgixa kai Junaid yayi ya shiga unbuttoning din shirt din yace "Wata mahaukaciya ce wllh" El-Ameen ya kwalalo ido yace "Mahaukaciya kuma" Junaid yace "Yea!" Nan ya ba El-Ameen lbrin abinda ya faru a hanyarsa ta xuwa, El-Ameen yace "Eyya! Poor her, but kai me ya kai ka rike mahaukaciya ma banda abun ka" Junaid bae ce komae ba ya mike ya nufi bathroom, wanka yyi ya fito sanye da Bathrobe din El-Ameen ya goge jikinsa ya bude wardrobe ya fiddo wasu kayan abokin nasa ya sa. Bayan Magrib yace ma El-Ameen xae koma gida, El-Ameen yace "Haba frnd baxa ka raka ni gun Iman ba plss, wllh ban san me xan ce ba idan na je, gashi Mami fushi take da ni, escort me plss, dama jira nake sai ka dawo sai mu je" Junaid yyi d'an murmushi yace "Ohk buh bari in kira mumy kar taji shiru har ynxu" Bayan isha suka bar gidan bayan Capt Junaid yyi ma Ummin El-Ameen sallama, A motar Junaid suka tafi El-Ameen na tukin, El-Ameen ya lura da yanda Junaid ya kafa ma tagar motar ta inda yake xaune ido yana kallon waje, El-Ameen xae yi magana ya ji Junaid yace "Dr d'an tsaya nn don Allah in ga ko an kwance mata igiyar, it's gud ace anyi hkn" El-Ameen ya kafa masa ido sae kuma ya tabe baki ya daga shoulder ya gangara gefen titi yyi parking, Junaid ya bude motar ya fita, tana nn xaune kan bolan, rike da wani bakin Leda a hannunta, rungume hannayensa yyi yana kallonta, El-Ameen ya dafa sa yace "let move on Capt, they've freed her" juyawa Capt Junaid yyi suka koma motar suka bar wajen, suna isa gidan El-Ameen ya kira Iman da nmbr da Ummi ta basa, kanwar ta ce ta fito tayi masu iso har falo ta cika su da drink, mahaifiyarta ta fito suka gaisa ta bar palon, ba a dau lkci ba Iman ta fito sanye da wata doguwar riga me adon stone blue da gold, tayi rolling kanta da plane blue mayafin kayan, kyakkyawa ce ba kadan ba, ta karaso falon kamshin turarenta ya cika ko ina ta xauna, kallon Junaid El-Ameen yyi, Junaid ma ya kallesa, suka shiga kallan kallo, ganin El-ameen yaki cewa komai Junaid ya d'an yi gyaran murya yana kallonta yace "Ina yini Hajiya" amsawa tayi ba tare da ta kallesu ba, Junaid ya d'an taba El-ameen alamar yyi magana mans, a hnkli El-Ameen ya matso kusa da shi murya can kasa yace "Me xan ce mata plss" ae Junaid bae san lkcn da ya fashe da dariya ba, El-Ameen ya tsaya kallonsa sai shi ma ya saka dariyar, nan suka dinga dariya kamar tababbu suka yi me isan su suka yi shiru, Junaid ya shafa kai yana kallonta yana murmushi yace "Ehm dama Ummi ce tace in rako El-Ameen wajen ki.... Shine muka xo" El-Ameen yace "Eh Ummi ce tace in xo gurin ki shine ya rako ni" kala bata ce masu ba, Junaid ya mike yace "Toh shknn mu xa mu koma sai mun sake dawowa" El-Ameen ma ya mike yace "Eh xa mu koma, sae wani lkcn, mun gode kwarai" mikewa tayi tace "Allah ya kiyaye" daga haka ta haura sama ta bar su tsaye parlon, dariya suka dinga yi cikin motar barin Junaid, El-ameen ya ja motar suka bar anguwar daga karshe, sae da El-ameen ya kai kansa gida sannan ya fita suka yi sallama Junaid ya koma driver seat ya ja motar ya bar layin, yana isa inda mahaukaciyar take yyi parkin yana kalle kallen inda xae ganta daga cikin motar, sae bae bae ganta ba ya ja motar ya nufi gida. Yana jiran masu gadi su bude masa gate kiran mum dinsa ya shigo wayarsa, jan motar yyi ya shiga compound din ya nufi parkin lot yyi parking snn ya fito, ganin motar Abba yasa shi kallon agogon wrist dinsa ya ga har goma ya kusa, bangaren mumy ya nufa, tsaye ya sameta palo tana rike da wayarta ta rungume hannu, yyi murmushi yace "Ga ni na dawo Mum," ta hade rai tace "Daga ina kake hka Ahmad?" Ya shafa kansa yace "na gaya maki Gidansu El-Ameen na tafi mum, na raka sa xance ne" yana murmushi ya k'are maganar, mumy tace "Zance! Lallai ba ayi abun arxiki ba kenan" dariya yyi lkci daya ya hade rai yace "Allah mum mun yi magana me ma'ana, infact ni ne ma nayi don shi shiru yyi wai kunya" Mumy tayi dariya tace "Au, kace ka kora masa budurwar knn in har kai kayi magana, tab!" Dariya shi ma yyi ya mata side hug yace "Kai Mumyna ni din ne ban iya magana ba" murmushi tayi tace "Kaje gun Abba yana neman ka" ya saketa yace "Ohk Mum" kofar da xae sada sa da part din dad dinsa ya nufa, xaune ya samesa babban falonsa yana kallon news lkci daya yana shan fruit salad din dake kan d'an table gabansa, Hajiya Fatee na xaune gefensa, sae step sisters dinsa su uku gaba daya suna palon, xaunawa yyi kasan lallausan rug din yana kallon Abbansa yace "Barka da dawowa Abba" Abba yace "Yauwa daga ina kake naga baka duty ae" yace "Naje gidansu El-Ameen ne Abba," kallon Hajiya Fatee yyi yace "Ina yini Hajiya?" Tayi murmushin da bai kai ciki ba tace "Lfya lau, ya aikin" yace "Alhmdllh" Muhibbah ce ta shigo falon da sallama rike da bowl din kankana da akayi slicin, ta duka ta ajiye gefen Abba, xama tayi tana kallon junaid da ya maida hankalinsa kan Tv tace "Ina yini yaya" amsawa yyi ba tare da ya kalleta ba, Hajiya Fatee sae kallonsa ta gefen ido take, mikewa Junaid yyi yace "Sae da safe Abba" Abba yace "Yauwa ka ba Muhibbah dubu ashirin xa tayi amfani da su a makaranta gobe wae," yace "toh Abba" daga nn yyi ma Hajiya Fatee sae da safe, kanninsa ma suka yi masa sai da safe ya fice daga falon rai a bace, mikewa Muhibba tayi ta bi bayansa, bae tarda mumy a palo ba, hka yasa ya nufi bedroom dinta ya sameta har ta kwanta, xauna wa yyi daga gefenta yace "Kin kwanta mum?" Tace "Har ka fito?" Yace "Eh mum" peck din goshinta yyi yace "Gudnyt mum, xan tafi in kwanta" tace "Toh Allah tashe mu lfya, make sure kayi alwala kayi addu'a kafin ka kwanta" yace "In'sha Allah mum" mikewa yyi ya kashe mata wutan dakin ya rufe mata kofa ya fita, dakin da kanninsa suke ya bude, Aisha ce ke waya ita ko Fatima tayi bacci, ya rufe kofar ya fito parlor, xaune ya tarda Muhibbah tana jiransa, yyi mamakin rashin ganin Hijab a jikinta
Chapter 2 · 0% Book details