Sashe 32
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
ina addini ya yarje mana da haka d'an nan" xaro ido yayi sai kuma yayi dariya ganin inda xancen nata ya dosa yace "kar ki manta mama ba fa lafiya gareta ba kuma shi ake kokarin ganin an nema mata, karkashin treatment take yanxu, don haka...." ta girgixa kai tace "A'a gaskiya ba wai ina maku shisshigi bane amma bai dace ba, sai dai kawae in hada kayanta mu je kuma na maku alkawarin kwana biyu xamu yi in juyo, kayi mata duk allurorin da xaka mata yanxu" El-ameen ya jinginar da kansa jikin kujera yana murmushi yace "Komai na hannun junaid mama sai yanda yace" tace "Toh kirasa" yana ciro wayarsa kiran Junaid ya shigo ya d'aga, Junaid yace "have you seen khadija?" El-ameen ya hade rai yace "Y weren't you picking my call daxu?" Bbu yabo bbu fallasa Junaid yace "Was very busy, ya ake ciki yanxu?" El-ameen yace "Zaka san you were busy ne, mama dai tace xata tafi da ita don bbu wanda xai dinga kwana da ita a nan," da sauri Junaid yace "What? No, no how can dat be, idan ta kara gaba fa, No she shud leave her xa mu san yanda xa muyi" El-ameen yace "Zaka san yanda xaka yi dai" daga haka ya katse wayar ya kalli mama jummai yace "Kin ji mama wai xai kai ta gun yayarsa ne har ki dawo" mama tace "Atoh hakan ma yayi bari inje to in hada mata kayanta" El-ameen ya bi ta da kallo har ta haura sama, ya juya yana kallon khadija dake ta kallonta ko kiftawar kirki bata yi, yace "Wannan kallon fa" ta kallesa ta sauke ajiyar xuciya a hankali tace "She's so beautiful brother" murmushi yayi bai ce komai ba ya fara danna waya, tace "wace yayar ya Ahmad yake fadi" El-ameen yayi dariya yace "Oho" Mama jummai ta sauko rike da jaka dauke da kaya tace "Ga kayan na hada" El-ameen yace "Sannu mama" kitchen ta shiga ta fito da plate dauke da potatoe da ketchup a gefe ta ajiye gabanta, El-ameen yace "Shikenan mama xa ki iya tafiya kar dare ya maki a hanya" Mama tace "Toh," ta maida dubanta ga khadija tace "Da kin ga ta nufi sama toh kilan bayi take son shiga, ko kuma tana son xuwa ta xuba ruwa jikinta, tana son tea sosai don Allah a dinga mata, sai wannan abun da na soya mata da kunu" Khadija tace "Toh" El-ameen ya ciro dubu talatin ya mika mata yace "Ga kudin mota mama sauran sai kiyi ma mai jego siyayya" dukawa tayi ta karba tana ta sa masa albarka, ta karasa ta shafa kanta tace "Sai na dawo diyata, Allah ubangiji ya yaye maki" kamar taji me tace ta mike da sauri, mama tayi murmushi ta dau jakarta bayan ta gyara kayan da ta xubar mata, tayi wa El-ameen sallama ta nufi kofa, ai da sauri ta bi bayanta El-ameen ya mike yyi dariya yace "ta fa gane tafiya xa Kiyi" shigewa jikin mama tayi, mama tayi dariya tace "Ikon Allah, baxan dade ba 'ya ta jibi xan dawo kin ji" El-ameen ya karasa ya janye ta daga jikin mama ta fasa wani kara xata kwace kanta yayi mata tsawa, tsit tayi tana kallonsa, mama ta juya ta fita cike da tausayinta, yana rike da ita suka koma parlon ya xaunar da ita gefensa hawaye ya gani idonta, khadija ta xamo kasa ganin hakan a hankali tace "She's crying" kallonta yayi yace "Tafi kitchen ki debo min ruwa" mikewa tayi ta nufi kitchen din, tana shiga ya dafata ya lumshe ido a hankali yace "Am sorry jewel, mama xata dawo soon kin ji" dogon hancinsa ya ji ta ja kamar yanda yake mata ya bude ido da sauri, sai kuma yayi murmushi ya lakaci nata hancin a hankali yace "Pretty~Jewel" *Haske Writers Association* *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 23...... A hankali ya dago kanta yana kallonta, ya ciro handkerchief aljihunsa ya share mata idonta murya can kasa yace "Am sorry jewel" yana jin fitowar khadija daga kitchen yayi saurin dauke hannunsa a shoulder dinta ya koma baya, ta karaso parlon ta mika masa cup din ruwan, ya amsa ya ajiye sannan ya saukar da ita kasa shi ma ya sauko, dankalin da mama ta ajiye parlon ya jawo ya dauka ya hada da tomatoe ketchup ya kai bakinta, ta sa hannu ta karba ya sake mata, ta lashe tomatoe din, khadija tayi murmushi ta dawo kasa d'an nesa da su ta xauna tana kallonta, haka ta dinga shan tomatoe din kanta a kasa, ya tsura mata ido yana kallo, ta d'ago manyan idonta ta sauke kan nasa, dauke nasa yayi ya mike ya koma kan kujera yace "tafi kitchen ki hado mata tea khadija" khadija ta kama hanyar kitchen yana ganin haka ya kuma saukowa ya dawo ya xauna gabanta ya dau potatoe ya kai mata baki xata kauda kai ya rike kan ya hade rai ya tura mata dankalin yace "Eat!" taunawa ta shiga yi tana kallonsa tana yamutse fuska, ya kalli kofar kitchen sannan ya kalli ragowar ketchup din dake gefen bakinta, ya matso a hankali ya sa yatsa ya kwashe ketchup din ya lumshe idonsa ya kai baki, dai dai nan aka bude kofar parlon, ya koma baya da sauri yana goge bakinsa, Junaid ya shigo parlon, kallo daya yayi masu ya sunkuya ya shiga cire takalmi da safar kafarsa, El-ameen ya mike ya koma kujera yana shafa kai, karasowa cikin parlon Junaid yayi, yana sanye da trouser din uniform dinsa sai farin polo, El-ameen na kallonsa yace "Gud you came, so ya xaka yi da ita da nyt?" Xaunawa Junaid yayi bai ce komai ba, ta dauki plate din gabanta ta mike ta dawo kusa da shi ta daura kan kafarsa, murmushi ya d'an yi ya rike plate din yace "No! Thank you" El-ameen ya dauke kai hade da tabe baki, khadija ta fito rike da cup din tea ta ajiye tana kallon Junaid tace "Welcm bro" yace "Thank you, how about you telling Hajiya you will be spending the nyt at ur frnd's place?" Shiru tayi sannan ta langwabar da kai ta xauna tace "Kasan Abba yana nan" shafa kansa yayi bai ce komai ba ya dauke plate din da ta daura masa a kafa ya ajiye kasa, El-ameen ya d'aga kafada ya mike ya haura sama, kallon khadija Junaid yayi, tayi murmushi tace "Wai yaya ka ban labarin inda Ku ka ganta mana, dama kun santa ne?" Junaid yace "I donno for El-ameen" tablets dinta El-ameen ya dauko a sama ya dawo parlon, sai da ya fara shiga kitchen yayi diluting dinsu sannan ya fito, ba musu ta bude baki ya juye mata tana yatsina fuska, Khadija tayi murmushi ta daura kanta jikin Junaid a hankali tace "I like her Ya A.jay" murmushi yayi bai ce komai ba, El-ameen yace "I will be going back to clinic yanxu, nan da thirty mins xata yi bacci, duk inda ta kwanta ki kyaleta kawai" a hankali khadija tace "Ni fa ina jin tsoro, tafiya duk xa ku yi ku bar mu" El-ameen ya harareta yace "An ce maki bata komai da'alla" Junaid ya tashi shima yace "Baxata maki komai ba sister, am also leaving" shiru tayi bata ce komai ba, El-ameen yayi hanyar kofar, Junaid ya bi bayansa, da sauri ta mike ta nufe su khadija ta bi ta da kallo gabanta na faduwa, gun Junaid ta nufa, El-ameen ya juya yana kallonsu, shima Junaid kallonta ya tsaya yi, tsaki El-ameen yayi ya xaro mata ido yace "C'mon koma kar in baki knock" kara ta saki kamar ta ji abinda yace, El-ameen ya fice daga parlon, Junaid yayi murmushi ya kama hannunta suka koma parlon ya xaunar da ita yana kallonta yace "Look Jasmine xa mu dawo anjima kin ji, khadija will be staying with you har mu dawo" Khadija tace "Waow yaya sunanta Jasmine?" Da sauri ya kalleta don ya manta gaba daya tana gun, yace "Ohh! Did I call her dat" khadija tayi dariya tace "Ehh mana" ya mike yace "No I didn't" ihu ta fasa ta mike da sauri ganin ya tashi, Khadija ta langwabar da kai tace "Yaya ba ka baro gun aiki ba, stay with her plss, bata son ka tafi" yace "Am hungry, gida nake son tafiya in ci abinci" khadija tace "Ae Akwae food stuffs a nan ba sai in girka maka ba" shiru yayi sannan yace "Alryt ki min indomie kawai" tace "Toh" ta mike ta shiga kitchen, xaunawa yayi ya xaunar da ita gefensa yayi murmushi ya ja dogon hancinta yace "I will stay with you Jasmine" suna nan xaune har khadija ta dawo parlon rike da tray me dauke da indomie da fried egg a gefe sai roban ruwa da cup ta ajiye kasa tace "Gashi yaya" saukowa kasa yayi ita ma ya sauko da ita suka xauna sai kallon indomien take kamar idonta xai fito, murmushi yyi ya kalli Khadija yace "Ke baxa ki ci ba" ta girgixa masa kai tace "Na koshi" daukar fork din yayi ya debi indomie kadan ya kai mata baki bayan ya d'an huce, wani kara da yasa shi sakin fork din tayi khadija ta mike da sauri ta bar wajen, ta dinga ihu tana komawa baya tana kallon indomien duk ta ruda shi, ya riketa yana cewa "What happen jasmine, bakya so ne" ihu kawae take tana komawa baya, ya kalli khadija yace "Take it away" dauka tayi ta nufi kitchen da sauri, tsit tayi ta bi khadija da kallo, ta dawo kusa da shi ta xauna, shi kam kallon mamaki kawai yake mata, hannu ta sa ta taba long lashes dinsa, yayi murmushi ya cire hannunta yace "Indomie kike tsoro Jasmine" khadija ta fito tace "Yaya kila tsoron shi take ji, kaje kitchen ka ci" ya girgixa kai yace "no idan naje gida xan ci abincin" kallonta Junaid yayi jin ta jingina jikinsa ya ga bacci ya fara daukarta, ya mike ya kwantar da ita kan kujeran, khadija tace "Baxa ta fadi ba yaya?" Yace "Ehh, bari in tafi gida in dawo yanxu tun da tayi bacci" a hankali khadija tace "Toh amma ka dawo kafin ta tashi plss