← Book details Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 104

Sashe 41

Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read

daya bangaren El-Ameen yace "ka dai ji abinda nurse din nan tace daxu, kuma baka kira kace ga yanda xa ayi ba, kai fa matsala gare ka" junaid ya d'an yi shiru sai kuma yace "Wllh ban san yanda xan ce xa ayi ba friend, baxai yiwu ka kaita ko gidan frnds dinka masu mata ba?" El-ameen yace "Kai ma ai naga kana da frnds din masu mata, ka kai ta mana" daga haka ya katse wayar, junaid ya tabe baki ya ajiye wayarsa ya koma ya kwanta, wata old time frnd El-ameen ya kira don xuwa tayi spend din daren da Jasmine ganin time na wucewa. Khadija ce kwance parlonsu misalin takwas da rabi ta fara bacci, Muhibba dake parlon ita ma xaune ta buge kafarta tace "Baxa ki kai ma ya Ahmad ruwan lipton dinsa ba ne wai kina neman kiyi bacci" kallonta khadija tayi tana murxa ido tace "Lipton kuma, a gun Mumy yake sha ai" Muhibba tace "Amma daxu ya aiko Humainah wai ki dafa masa ki kai masa, ohh bakya parlon ashe" mikewa khadija tayi tace "Da gaske" Muhibba ta tabe baki ta ci gaba da kallo abunta tace "A'a karya" Hajiya dai abincin gabanta take ci amma duk hankalinta na Kansu haka ma Suhaimah dake parlon, Hajiya tace "Shegiya da nice na tashe ki yanxu ki dafa min Lipton da baxa kiyi ba, amma da yake Ahmad ne, wato uban da ya haife ki ai kin tashi..." Turo baki tayi ta mike ta nufi kitchen, Muhibba ta kalli Hajiya, Hajiya tayi murmushi ta ci gaba da cin abincinta, khadija na shiga kitchen din ta shiga dafa masa ruwan Lipton da kayan kamshi sosai kamar dai yanda yake so, Hajiya ce ta kwalo mata kira ta fito, Hajiya tace "Tafi ki dauko min wayata a sama" tana haurawa sama Hajiya ta kalli Suhaima tace "tashi..." Da gudu Suhaima ta nufi kitchen din ba a dau lokaci ba ta fito da sauri tayi xamanta, dai dai lokacin da Khadija ta sauko ta mika ma uwarta wayar ta nufi kitchen, cikin few minutes ta fito rike da mug mai murfi ta fice daga parlon duk suka bi ta da kallo. Junaid na xaune parlor yana kallon kwallo sai dai duk sonsa da kwallo ranan baya masa dadi, gaba daya tunanin yanda xai fara kawo jasmine gun mumy ran lahadi kamar yanda El-Ameen ya basa shawara yake, kwankwasa kofa aka yi ya juya da sauri lokaci daya khadija ta bude ta shigo da sallama tace "Gashi yaya" kallonta ya tsaya yi kafin yace "What's that?" Tace "Lipton mana, wai Humainah tace kace in dafa maka" ya d'an bude ido bai dai ce komai ba, ta karaso ta ajiye masa ta juya ta fice, bude mug din yyi ya lumshe ido ganin Lipton din yanda yake so, dama can ita ke masa Mumy ta hana wai bata son yana cin duk abinda xai fito daga side dinsu, rufewa yayi ya ci gaba da kallonsa. *Haske Writers Association* *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 31..... Kallon agogo junaid yayi yaga tara ya kusa, ya jawo wayarsa ya shiga kiran El-ameen don ya ji ko ya samu inda xai kai ta, har ya gama ring bai d'aga ba, mikewa yayi ya dau mug din Lipton din ya shiga daki ya xauna gefen gado ya bude ya shiga sip dinsa a hankali, kusan rabi ya sha ya rufe ya ajiye sannan ya mike ya shiga bayi don yin wanka, da kyar ya iya fitowa daga bathroom jin kansa na wani irin juya masa, ya xauna gefen gado sanye da bathrobe, shi kansa baxai ce ga abinda ke damunsa a lokacin ba, kwanciya yyi yayi rub da ciki, a haka ya ji an bude kofar parlor aka karaso har bedroom, kasa dagowa yayi yaga ko waye jin wani axababben ciwo da cikinsa ke masa, tsaye Muhibba tayi bakin kofar tana kallonsa, tuni kamshin turarenta ya gauraye dakin, ya juyo da kyar yana ganinta dishi dishi, rufe kofar tayi ta karaso cikin dakin ta xauna gefensa cike da kissa tace "Ya Ahmad dama Abba ne yace ka ban dubu biyar xan yi amfani da shi" mikewa xaune yayi don ta muryarta ya gane ko wacece ya rike kansa duk da yanayinsa hakan bai hanasa hade rai ba yace "How dare you xaki shigo min daki?" Mikewa tayi ta nufi kofa irin ta ga ko xae tsayar da ita, har ta isa bakin kofar bata ji yace komai ba sai komawa da yayi ya kwanta ya runtse ido, cije lebe tayi ta kuma dawowa ta hau kan gadon da damuwa kamar gaske ta dafa sa da duk hannunta biyu tace "Wai baka da lafiya ne ya Ahmad" ai bai san lokacin da ya fixgota ba ta fado kansa ya kankameta, wani murmushi tayi tana kallon kyakkyawan fuskarsa don har lokacin idonsa rufe suke, ta dake tace "Meye haka ya Ahmad, ka kyaleni" ko kadan bai jin abinda take cewa ba, lkci daya ya koma kamar mara hankali, wani farin ciki ya rufeta ba kadan ba ta sakar masa jiki, cikin mintuna kadan yanayinsa ya bata tsoro, tun tana daurewa har dai tsoron ya fara bayyana, gashi ba rikon wasa yayi mata ba, turasa ta fara yi a tsorace daga karshe tana neman kwace kanta duk da ba haka suka yi da su Umma ba, amma ta gama tsorata da shi gaba daya, kin saketa yyi ta saka kuka tace "Don Allah ya Ahmad kayi hakuri ina rokon ka" ko sanin abinda take cewa bai yi ba, ihu ta fasa a rikice tana turasa tana kwala ma Umma kira amma ya ki saketa, bude kofar dakin da aka yi lokaci daya da karan tarwatsewan bowl me dauke da fruit salad ne ya sa shi sakinta da sauri, ta ja bargo ta rufe jikinta tana kuka jikinta na rawa, shi ko dama bathrobe na jikinsa, kallonsu Humainah ta tsaya yi a bakin kofa jiki a sanyaye, ya sauko da kafafuwansa kasa ya rike kai xuciyarsa na bugawa ya dinga nanata innalillahi... A xuciyarsa, Muhibba ma ta xamo daga kan gadon tana kuka har lkcin ta jawo hijab dinta ta sa ta fice da sauri sai ka rantse ba ita ta kawo kanta ba ganin yanda take kukan jiki na rawa, da kyar Humainah ta juya xata bar dakin ya dago kai yayi kafin halin kiranta, amma ko juyowa bata yi ba ta fice da sauri, sake rike kansa yayi ya runtse ido duk ya kasa tuna yanda abun ya faru, mikewa yayi yana jin jiri ya shiga bayi, ya kusa awa daya bayin sannan ya fito ya fada kan gado lokaci daya bacci ya daukesa. Muhibba kuwa tana komawa part din uwarta ta gansu duk xaune suna jiran dawowarta, Hajiya ta mike da sauri tana kare mata kallo tace "Ya naga kin fito da wuri, ko dai bai sha ba" ta bata fuska tana goge guntun hawayen idonta tace "Ya sha mana, ni dai tsoro nake ji wllh" Umma da Hajiya suka yo waje da ido suka hada baki wajen cewa "Me? Kina nufin bai maki komai ba??" ta fashe da kuka tace "Ni Allah tsoronsa naji Umma, ni dai baxan iya ba a tura suhaima" Umma tayo kanta a fusace tace "Nashiga uku ni balki, Allah wadaran ki yar iska kawai, tsoron uban me, innalillahi... Shikenan ta bata plan din" Hajiya da idonta ya kankance don bacin rai tace "Ni nasan a rina dama kawai nayi shiru ne, da Suhaima ce ko dar baxa ta ji ba kika ce mu tura debabbar yar nan taki gashi ta rusa mana budget, wannan wace irin fitina ce" Umma ta kwalo ma suhaima kira tace "Maxa ke ki je..." Muhibba tace "Humainah fa ta shigo ta ganmu!" Juyawa suka yi da sauri Suna kallonta, Hajiya ta xaro ido tace "Allah?" Muhibba ta tabe baki tayi hanyar daki, Umma ta jabe kan kujera ta dafe kai tace "Allah ya tsine ma tsiya!" Tsaki Hajiya tayi ta fice daga part din kamar xata tashi sama. Ray din rana ne ya farkar da Junaid da safe, ya mike xaune da sauri yana kallon agogo yaga bakwai da kusan rabi, xaro ido yayi lokaci daya abinda ya faru jiya da daddare ya dawo masa gabansa ya fadi, kalle kallen dakin ya shiga yi yana tunanin what just came over him jiya, rike kansa dake sara masa yayi, ya mike tsaye da kyar ya shiga toilet, wanke baki yayi, yayi wanka snn ya dauro alwala ya fito, ya jima xaune kan pray mat bayan ya idar da sllh daga bisanni ya mike ya isa bakin kofa ya tattara pieces din bowl din jiya da Humainah ta fasa bakin kofar ya gyara wajen ya goge ya fitar da mug din Lipton din ma. Parlor ya fito ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe ido. Ganin har Karfe tara ya kusa ya sa ya mike a sanyaye ya fita ya nufi part din Mumy, kasa shiga parlon Mumy yayi don bai san da wani ido xai kalli Humainah ba, da kyar ya tura kofar daga karshe ya shiga, bbu kowa parlon sai kamshi me dadi dake tashi, ya karasa ciki jiki ba kwari ya xauna, Mumy ce ta fito daga daki tana kallonsa tace "Sai yanxu ka tashi?" Kasa kallonta yayi ga wani faduwa da gabansa yake don gani yake kamar Humainah ta gaya mata, ya dukar da kai ya gaisheta, tace "Meye haka kake kamar munafuki" dagowa yayi da sauri ya kalleta yace "A'a kaina ke min ciwo Mumy" tace "Toh ga breakfast dinka can a dinning sai ka sha magani idan ka gama" mikewa yayi ya tafi dinning din ta bi sa da kallo, tabe baki tayi ta koma daki, tea kawai ya iya sha sai dube duben inda xai ga Humainah yake, mikewa yayi daga karshe ya tafi dakinsu, kwance ya sameta ita kadai fatima kuma ta tafi boko, mikewa xaune tayi ganinsa ya rufe kofar dakin tana ganin haka ta fashe da kuka tace "Ni wllh ka fita kar in kira maka Mumy" tsayawa yayi yana kallonta, tana share fuskarta tace "Ni dai ka fita" ganin ya nufota tsoro ya kamata ta fasa ihu tana kiran Mumy, still yayi
Chapter 41 · 0% Book details