← Book details Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 104

Sashe 26

Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya ce masa ya siya ready made din fura da nono sannan ya nufi gidan, Mama kadai ce kwance parlor kan darduma, ya gaisheta ya bata nata fruits din da fura tayi ta masa Godiya yayi murmushi kawai ya haura sama. Xaune ya samu El-Ameen yana danna laptop, ita kuma tana tsaye can jikin bango ta jingina, El-Ameen yace "Sae da ka ga dama kenan" Junaid bai tanka sa ba ya ajiye ledan hannunsa ya xauna gefen gado, El-Ameen ya ya juya yana kallonta yace "Ba dai baki ji ba, wait in tashi xa ki ga abinda xan maki a wajen nan" Junaid ya kallesa kafin ya girgixa kai a xuciyarsa yace ae Kaine mahaukacin ma, takowa tayi ta karaso kusa da ledan da junaid ya ajiye ta durkusa, El-Ameen ya daka mata tsawa yace "c'mon ance maki naki ne" mikewa tayi da sauri, Junaid ya dauki ledan ya mika mata ta karba, El-Ameen ya mike tana ganin haka ta sake ledan ta koma jikin bangon da take, dariya yayi yana kallonta yace "kai! Yarinyar nan ba dai tsoro ba" shi dai Junaid ko kallonsa bai yi ba, Karasowa yayi ya dau ledan ya bude ya fito da bunch din Ayaba ya mika mata, ta karaso da sauri ta karba, xata juya ya fixgota ya xaunar da ita gabansa, da kansa ya shiga bude mata ayabar yana mika mata, tana karba tana ci, ana uku ne taki ci, ta kalli Junaid dake danna wayarsa sae dae gaba daya hankalinsa na kansu, ta matsa kusa da shi a hankali ta kama hannunsa ta sa mashi Ayaban, tabe baki El-Ameen yyi ya kuma bare mata wani ta karba ta kuma kama hannun Junaid ta basa, El-ameen ya hade rai ya kuma bare wani ya bata xata ba Junaid yayi mata tsawa, a tsorace ta juyo, yace "I will knock you yanxu, ina shan wahala ina bare maki abu kina kyauta da shi, da xan bar ki yanxu da peel din xaki hade ki cinye," kafa masa manyan idonta tayi ko kiftawa bata yi, junaid yayi murmushi ya girgixa kai, wayar El-Ameen ne ya fara ring ya dauka, xaro ido yayi ganin Abbansa ne ke kiransa, ya kalli Junaid yace "Kasan kuwa ban je clinic throughout yau ba" ko kallonsa Junaid bai yi ba, ya daga a hankali ya kai wayar kunne, daga daya bangaren Abban nasa yace "ka taho clinic ka sameni yanxu Ahmad, clear?" yayi kasa da kai yace "Toh Abba" daga haka ya ajiye wayar yana kallon Junaid yace "Look! Xan je clinic yanxun in dawo, wait har sai na dawo don't go plss, kaga bata da lafiya karfin hali kawae gareta she just finished vomiting kafin ka shigo, dats why nake nan har yanxu, am giving her her drugs before leaving yanxu" Junaid ya xaro ido yace "Idan Mumy ta kira ni fa, beside 8:30 tace in dawo gida, nd this is almost 8 o clock" Kallonsa El-Ameen ya tsaya yi sae kuma ya girgixa kai yace "Tashi ka tafi toh, wato nine bansan darajan parent dina ba koh Captain, nine na iya karya kai baka iya ba, you know am doing this goddam job for ur sake if you provoke me wllh sae in fasa kawai ka kaita asibiti, kullum safiya sai na xo nan sbda drugs dinta da injections, at mid day ma I have to leave whatever i am doing in xo nan bata magani, haka da yamma ma, sannan da daddare bana barin gidan nan sai kusan sha daya, Haba!" kallonsa kawae junaid yake bai ce komai ba, tsaki yayi ya mike ya dauko maganinta da cup yayi diluting da ruwa ya xauna kusa da ita xai bata tana ganin haka ta fara kokarin mikewa ya fixgota, bbu gardama ta shanye maganin duk jikinta na rawa, ya mike ya dau makulli da wayarsa yana kallon junaid on a serious note yace "Look! In har ka bar gidan nan kafin in dawo wllh wllh kaji rantsuwan musulmi koh, toh sai dai ka san yanda da xakayi da yarinyar nan don ba fina biyayya kayi ba, I am taking my hands of her case" daga haka ya fice daga dakin, Junaid da ya bi sa da kallo yana murmushi snn ya juya yana kallonta, yatsine fuska kawae take, ta matso kusa da shi ta mika masa Ayabar hannunta, a hankali ya sauko daga kan gadon ya karba ya kai mata baki yana kallonta yace "Eat!" Ta kauda kai da sauri, kallon Ayabar yake yana son ci amma ya kasa, ajiyewa yayi ya dau Apple ya mika mata, Kin karba tayi, yayi murmushi ya ajiye shi ma, a hankali ta kwanta nan gefensa, ya tsura mata ido, kamar warce aka tsikara ta mike xaune da sauri, ya koma baya yana kallonta. *Haske writers Association* *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 18..... Amai ta shiga kwararowa a gurin, ya mike yana kallonta har ta gama ta koma xata kwanta yayi saurin riketa, kara ta saki ta turasa da karfi xata kwanta gun aman yaki saketa, nan ta shiga kokuwa da shi ita sai ta kwanta, ya rike ta gam yace "Wait Jasmine..." ta kuma sakin wani ihun da ya tsorata shi, ae da ta turasa sai da ya kusa faduwa ba shiri ya saketa, ta yi kwanciyarta nan kasa, ya sauke ajiyar xuciya ya nufi toilet, mop da bucket ya dauko ya dawo dakin, rasa ta inda xae fara gyara wajen aman yayi, ya ajiye ya fita don kira Mama jummai, tare suka shigo dakin, ta karaso kusa da ita da sauri cike da tausayinta ta dagota tana mata sannu, ihu ta sakar mata ita ma ta kwace kanta ba shiri ta saketa ta koma ta kwanta tana mayar da numfashi, girgixa kai mama tayi ta mike ta shiga gyara wajen, tana gamawa ta kuma gwada d'aga ta a kasan tiles din still taki tashi, kyaleta tayi ta fita, Junaid ya mike ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito jin kiran isha, a nan dakin yayi sallah, yana xaune kan darduma ya ga tana juye juye a kasan da take kwance. Kallonta kawae yake cike da tausayinta don da ganinta kasan tana jin jiki, ta mike xaune a hankali ta dawo inda yake tana kallonsa ta kwanta kusa da shi, dagota yayi murya can kasa yace "Sorry Jasmine" lumshe ido tayi ta kwanta nan kusa da shi lkci daya bacci ya dauketa, ya mike ya koma can jikin gado ya xauna, har Karfe tara El-Ameen bai dawo ba, duk ya kagu ya dawo ya wuce kafin Mumy fa kirasa, tara da rabi kiran Mumy ya shigo wayarsa, k'asa d'agawa yayi don bai ma san me xai ce mata ba har sai da ya kusa katsewa sannan ya daga da sauri, Mumy tace "Where are you Ahmad" kallon dakin yayi kafin a hankali yace "Mumy, am am with El-Ameen" strictly tace "You are very stupid, within the next 10 to 15 mins ka tabbatar kana cikin gida if not xaka ga bacin raina, in kuma kaya ku ka kasa a titi ku ke saidawa da daddaren nan xaka gaya min" kamar mai shirin kuka yace "Kiyi hakuri Mumy xan dawo" katse wayar tayi, ya rike kansa, layin El-Ameen ya shiga nema yana ta ring bai d'aga ba, ya lumshe ido ya jingina jikin gado, he just don't know wat to do, haka yayi ta kiran El-Ameen bai daga ba, Shivering yaga tana yi daga kwancen da take kan darduma, ya mike ya karasa inda take ya dago ta ta bude ido da sauri, kan gadon dakin ya kwantar da ita ya rufa mata bargo, ta cire xata sakko ya riketa da damuwa yace "You are shivering Jasmine" ba shiri ya saketa a dalilin kara me karfi da tayi masa a kai, ta sauka nan kasan dakin ta kuma kwanciya. Har goma El-Ameen bai dawo ba, Junaid ya rasa me ke masa dadi shi da bae taba yi ma Mumy musu ba, yasan kuma fushi tayi shi yasa bata kara kira ba, da yayi niyar tafiya sae ya tuna abinda El-Ameen yace masa, ya kuma san xai aikata, shine xaune har sha daya, Mama jummai ta shigo tace "Kai xaka kwana yau a nan kenan junaid?" D'an murmushi yayi yace "A'a ina jiran El-Ameen ne yace xai dawo" tace "Toh tafi daki can ka kwanta inda yake kwana xan kula da ita" Junaid yace "yana kwana nan ne?" Tace "Eh wani lkcn yana kwana can dakin don akwai alluran da yake mata da sassafe, toh duk ran da xai mata alluran a nan yake kwana, ni kuma tare muke kwana da ita saboda shiga bayi da daddare" Junaid ya gyada kai yace "Bari in jira sa a nan Mama ni ba kwana xan yi ba ai" tace "Toh" sannan ta juya ta fita. Lumshe ido yayi ya jinginar da kansa jikin gado, wani bacci ya ji na fixgarsa ya bude ido yana kallon agogo yaga sha biyu, kallonta yayi ya ga ta canxa position, a hankali ya mike ya isa inda take xai dagata ta bude ido da sauri, birginawa tayi ta bar gun ta juya masa baya, ya mike ya koma ya xauna kan gadon, xuwa yanxu kam ya gama sanin iskanci El-Ameen yayi masa, dole ko yaki ko ya so a nan xai kwana hakan ba karamin bata masa rai yayi ba, sha biyu da rabi ya kuma mikewa jin yana jin bacci sosai ya bude closet ya dau bargon da ya gani ya koma daya side din gadon ya shimfida a kasa ya kwanta dai dai yanda xai dinga ganinta, nan da nan bacci ya daukesa. Bude ido yayi jin an bude kofa don ko k'adan bashi da nauyin bacci, El-Ameen ne ya shigo dakin yana ganinsa ya dauke kai, kallo daya El-Ameen yayi masa yana murmushi bai ma san idonsa biyu ba ya karasa gun da take kwance a kasa, durkusawa yayi gabanta ya dagota, ta bude ido da sauri, lumshe ido yayi jin xafin jikinta a hankali yace "Sorry, Jewel" xata koma ta kwanta yaki saketa, ya mike ya dauketa ya nufi kan gado da ita ya kwantar, kokarin sauka ta shiga yi da kyar, ya hade rai yace "No" bata kuma yunkurin saukan ba,
Chapter 26 · 0% Book details