← Book details Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 104

Sashe 51

Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read

xa ayi ma aure, auren ma na dole kamar wani mace kuma har lokacin bai san matar ba dariya ma kawai abun ke basa, ana saura sati bikin ya dawo aiki da yamma yana kwance sai dai gaba daya tunaninsa na gun Jasmine yana son sanin halin da take ciki yana kuma son ganinta, kiran El-ameen ne ya shigo wayarsa ya daga, daga daya bangaren El-ameen yace "Uhm duk xumudin xama angon ne yasa ka mance da patient dinka captain?" Junaid yace "If that's what you are thinking...." El-ameen yace "Toh yayi kyau, amma idan baka manta the very first day da ka fara xuwa min da batun ta sai da na baka shawarar ka raba kanka ka ki, yanxu ka xo kayi abinda ya dame ka, ka bar ni da 'yar mutane, ko irin ka dinga kira ka tambayi lafiyarta babu, to Dr sumayya dai ina a week time xa su yi tafiya da mai gidanta wai..." Junaid yace "Yea! Then an min auren sai ta dawo gidana kamar yanda ka ce" El-ameen ya tabe baki ya katse wayar. Karfe biyar da wani abu Junaid ya shirya ya tafi part din Mumy yace mata xai dan fita, sabuwar motar da Abba ya basa ya dauka ya fita daga gidan, a hanya ya kira El-ameen, yana dagawa yace "Kana ina?" El-ameen yace "Me xan maka?" Tsaki Junaid yayi yace "Dalla ni ka gaya min" katse wayar El-ameen yayi, junaid yayi parking ya ji kamar ya juya, sai dai baxai iya ba sbda son ganin jasmine da yake, sake kiransa yayi yana dagawa yace "How dare you xaka katse min waya daga tambaya" El-ameen yace "Ashe ba dadi kai kake ma mutane, ni da ma kai ka haukacen wllh kayi loosing memory ko xaka rabu da wnn worst attitude din naka, gashi it's getting worst nowadayz, ni ina gida anything?" Katse wayar junaid yayi hade da yin kwafa, ya kusa minti goma xaune motar ya kuma yin wani kwafan ya ja motar ya nufi gidan nasu, Ummi dake parlor ya gaida tace "Ni ban ga kai da abokin naka kuna shirin bikin nan ba Ahmad" junaid yayi yake yana shafa kai yace "Ae abinda ya kawo ni kenan" Ummi tace "Toh yayi kyau, da an gama naka da sati biyu in an huta xan kai nasa lefen kauye" Junaid ya fashe da dariya yace "Wllh xan maki driving din" Ummi ta hade rai tace "Am serious, dan ma ka gaya masa nake gaya maka" dakin El-ameen ya nufa yana dariya, El-ameen ya tura laptop din gabansa yace "What is making him laugh" Junaid ya buda ido yace "Baka ji a bakin Captain ba, yanzu dai tashi ka kai ni in duba yarinyar nan tunda gori ka min daxu" El-ameen yace "As you can see am busy, sai dai in baka address" junaid yace "Ba fa dadewa xa mu yi ba" "yess! ko minti daya xa muyi" cewar El-ameen yana kallonsa da kyau. Junaid ya kusa minti goma tsaye yana kallonsa kafin ya juya ya fita daga dakin, El-ameen yace "Byee!" Da daddare yana kwance bedroom Humainah ta fado masa, tabe baki yayi ya dauki wayarsa ya shiga kiranta, sai da ya kusa katsewa ta daga yace "don ma kin samu na kira ki" tace "I didn't beg for ur call" shiru yayi sannan yayi murmushi yace "True! Yaushe xa ki dawo?" Tace "Ana saura kwana biyu bikin ka xamu dawo da Hajja" yace "Bikinsu dai" daga haka ya katse wayar, Har ya ajiye wayar ya tuna Hafsat, tun ranan da abun ya faru bata kira ba bai kirata ba, numberta ya duba ya shiga kiranta bugu uku ta daga ya mata sallama ta amsa daga daya side din hade da gaishesa, ya ce "Ya kike?" Tace "Qlau" rasa me xai sake ce mata yayi, can dai yace "Am sorry for what happened Hafsat," tace "Ohh ba komai, ya wuce ai" yace "To nagode" tace "welcome! But a ina ka san yarinyar?" D'an shiru yayi kafin yace "It's a long story" tace "really?" Yace "Yeah!" Labarin yanda ya fara ganin jasmine tun daga rana ta farko ya fara bata har xuwa ranan da ya kai ta gida gun parent dinsa da abinda ya faru bayan barinsu gida, Hafsat da duk jikinta yayi sanyi tace "Yanxu kana nufin ta dawo hankalinta?" Yace "Yea, amma tayi loosing memory" Cike da damuwa Hafsat tace "Allah sarki, to yanxu tana ina?" Ya lumshe ido ya bude yace "Tana gun frnd dina, buh am getting married in a week time sai ta dawo gidana har tayi regaining memory, Hafsat tace "Dat's nyc Allah ya sanya alkhairi, ya bada xaman lafiya," Yace "Ameen thank you" shiru tayi ya kalli agogo ya ga har sha daya ya wuce, yace "Xa ki kwanta koh?" Tace "Yeah" yace "Ohk good nyt, tnx a lot ki gaida mutan gida" tace "Ayt bye!" Daga haka ya katse wayar ya ajiye yayi addu'an kwanciya. Washegari da yamma junaid na kwance bayan ya dawo daga aiki El-ameen ya shigo parlon, kallo daya ya masa ya dauke kai, El-ameen na daga tsaye bakin kofa yace "In ka shirya ka taso mu tafi" ko kallonsa junaid bai yi ba, El-ameen yace "Ohk nayi tafiya ta" daga haka ya fice. Junaid ya mike ya shiga bedroom ya daura shirt dinsa ya dau Atm ya fita, a part din Mumy ya tarda El-ameen, ya jira har ya gama surutun sa snn yace "Mumy xa mu d'an fita yanxu mu dawo" Mumy tace "Toh Allah ya tsare" ya juya ya fita. A mota yayi ta jiran El-ameen har sai da yaga dama ya fito, El-ameen ya xaga daya side din ganin junaid a driver seat yana shiga junaid ya tada motar suka bar layin, tun a hanya El-ameen ya kira Dr sumayya ya sanar da ita xuwansu, a visitor parlor suka sauka dotan Dr Sumayya 'yar shekara sha uku ce ta kawo masu ruwa da drink ta xauna kusa da El-ameen tana ta basa labari, junaid dai makala earpiece yayi yana danna waya, bayan kusan minti biyar Dr Sumayya ta shigo parlon suka gaisa da El-ameen, El-ameen ya fixge wayar sai a sannan ya dago yana kallon Dr Sumayya yace "Ina yini!" Tace "Lafiya lau ya aiki," yace "Alhmdllh," mikewa tayi ta fita tana fita sistern ta warce xata yi mate din jasmine ta shigo parlon tare da jasmine din, xama tayi kan kujera ta nuna ma Jasmine gefenta ta xauna sannan ta gaida su El-ameen, ya amsa mata da murmushi yace "Ya sch?" Tace "Alhmdllh" kallon jasmine tayi tace "Baby baki ce masu ina yini ba" sunan da Dr Sumayya ke kiranta da shi kenan a sati daya da 'yan kwanakin da tayi a gidan, shine duk yan gidan ke kiranta da haka, shima El-Ameen dake yawan xuwa gidan sai ya dinga kiranta da haka, jasmine ta kalli farida sannan ta kalli El-ameen a hankali tace "Ina yini?" Murmushi kawai yayi mata ta sunkuyar da kai, Junaid dai sai kallonta yake ta gefen ido, El-ameen yace "Toh baki gaida wannan ba Baby" Ya fadi hakan yana nuna mata Junaid, kallonsa tayi tace "Ina yini?" Ya dago kai shi ma yana kallonta yace "Lafiya lau" daga haka ta sunkuyar da kai, El-ameen yace "Baby dawo ki xauna nan ki gaya min abubuwan da Farida ta koya maki yau" mikewa tayi ta dawo kusa da shi ta xauna kasa, Junaid ya kalli agogon wrist dinsa sannan ya ci gaba da danna wayarsa, El-ameen yace "Gaya min mana" dago kai tayi ta kallesa cikin sanyayyan muryarta tace "tace min girki ne abinda muka yi" dariya yayi yace "Da gaske, to me ku ka girka?" Ta kalli farida tace "Ya ma?" Dariya farida tayi tace "A'a tuna dai" shiru tayi kamar me naxarin sunan girkin, da sauri farida tace "Ohkk okk fried rice ne da coconut drink muka yi baby" tayi hakan ne don yanxun nan sai ta iya rike kai ta fara ihu hakan kuma zai ja Dr Sumayya ta bata mata rai, shi kansa El-ameen ya san in dai tayi stressing brain dinta wajen son tuno abu nan da nan kan xai fara mata ciwo, kuma yana daukan lokaci bai daina ba. Jasmine ta kallesa tace "Fried rice and coconut drink Mumy tace mu yi" yayi murmushi yace "Good kuma kin iya yanxu?" Girgixa masa kai tayi alamar A'a, zai yi magana junaid ya mike yace "Toh ni xan koma" El-ameen yace "ohK bani makullin motata" hade rai yayi yace "Xan yi amfani da shi ne" El-ameen ya mike ya warce makullin ya koma ya xauna, juyawa junaid yayi ya fice daga parlon. Da daddare yana kallon wani program khadija ta shigo parlon da sallama ta ajiye masa mug din hannunta, yana kallonta yace "Meye wannan?" Tace "Lipton mana" yace "Wa yace ki kawo min?" Tace "Ance kace wai in maka" yace "Ohk tnx" mikewa tayi ta fita, ya girgixa kai ya ci gaba da kallonsa, bayan kusan minti talatin yaji kamar motsi a balcony, mikewa yayi ya kashe wutan parlon ya rage na tv kadai ya dawo ya xauna, a hankali aka murda kofar parlon, ya jinginar da kansa jikin kujera idonsa na kan tv, Suhaima ce ta shigo parlon da hijab dinta har kasa, ta tsaya daga bakin kofar tana lekosa, shi dai bai juyo ba har lokacin, cikin sassarfa ta karaso cikin parlon ta na kallonsa tace "Ya Ahmad?" Bai tanka ta ba hakan yasa ta d'an yi murmushi ta xauna kusa da shi tace "Amm dama...." Mikewa yayi yana kallonta fuskar nan nasa kamar bai taba dariya ba yace "me ya shigo da ke nan?" Gabanta yayi mugun faduwa ta mike tace "Oh dama..." Juyawa tayi da sauri zata bar wajen ya fixgota, ya sauke mata wani mari me lafiya cikin tsawa yace "Nace me ya kawo ki nan" jikinta ya dau rawa tace "Wayyo kudi xa ka ban" wani marin da ya gigitata ya kuma kai mata, ya ja ta ya nufi daki da ita, kuka ta dinga yi a tsorace tana cewa "Kudi wllh na xo karba" belt ya dauka ta fasa ihu a rikice tana kiran Hajiyarsu, ya ja ta suka fito parlor ya xabga mata a jiki, wanda hakan sai da ya kusa
Chapter 51 · 0% Book details