Sashe 6
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 5 min read
mike xata bar wajen da gudu, fixgota yyi ya rike ta gam, ta shiga kokuwa da shi tana ihu, El-Ameen na daga mota yana lekansu, ban da dariya bbu abinda yake har da kyakyatawa, ba karamin wahala ta ba Junaid ba don da kyar ya kai ta k'asa ya daure hannunta shima din ba wae dauri sosae ba don taki tsayawa ga wani karfi dake gareta, bude mota El-Ameen yyi ya fito cikin ruwan ya karasa inda suke da sauri, karban sauran igiyar yyi junaid na rike da ita ya daure ta gam, ihu ta dinga masu tana shure shure, El-Ameen ya mike yace "Ae sae ka dauketa Mr Do good" bbu musu Junaid ya dauketa, ko kadan bata da nauyi ya nufi motar da ita El-Ameen na biye da shi a baya yana 'yar dariya, ya bude baya ya saka ta ciki ya rufe, yatsine yatsine El-Ameen ya shiga yi ya nufi driver seat, muryoyi suka ji daga bayansu duk suka juya, wasu matasa suka gani tsaye da gora da adda a hannayensu, da ka gansu ka ga masu gadi, cikin tsawa suka ce "Maxa ku fito da ita ynxun nn" kallon Junaid El-Ameen yyi, El-ameen ma haka, ae kan kace me sae ga Junaid cikin mota ya rufe, El-Ameen na ganin hka shi ma ya shige motar ya tada da sauri, samarin suka taho da gudu, cikin hanxari El-Ameen ya ja motar suka bar wajen, bin motar samarin suka yi da guda suna buga ma motar gora da karfi, El-Ameen ya dinga cewa "ya Salam! ya salam! ya salam!" har suka bar anguwar abinda yake maimaitawa kenan, juyawa yyi yana kallon Junaid dake ta kallon mahaukaciyar dake fixge fixge tana son freeing kanta, a fusace ? yace "Kai ka ji irin ynda suka tarwatsa min bayan mota kuwa Junaid" Junaid ya sauke ajiyar xuciya yace "Xan gyara maka motar ka idan Allah ya yarda" kwafa El-Ameen yyi yace "Better, kuma ka dinga lura da ita kar ta cafko ni mu shiga uku, ynxu ina muka nufa?" Junaid ya gaya masa ya kama hanyar anguwar, cikin minti goma suka iso, har lkcn ruwa ake, parking El-Ameen yyi yana kallon Junaid ya bude motar ya fito, fitowa yyi shi ma suka shiga gidan a tare, gidan babba ne ba laifi, junaid har yasa anyi furnishing gidan kar ya tsaya empty, El-Ameen yyi tsaki yace "Lallai! A wannan gidan xa a ajiye mahaukaciya? ba sae ta balla windunan nn mara karfi ba ta yi ficewarta, bugu daya idan tayi ma kofar nn ficewa xae yi wllh" Junaid ya shafa kansa a hankali yace "Toh shi suka samo min ya xa ayi" El-Ameen yace "Oho, amma idan ta gudu wallahil Azim ba da ni xaka je nemota ba" da damuwa Junaid yace "Toh hw are we going to do it ynxu ga shi mun dauko ta" El-Ameen yace "Oho it's left to yhu" xama Junaid yyi ya rike kansa, can yace "Ohk, let bring her in I will stay nd guard her till 2morrow kafin nn sae a samo mata wani gidan." El-Ameen ya shiga hararansa can ya ja tsaki yana kallon agogo yaga har goma ya wuce, yace "Kaga mu je can gida na, don ni na gaji sanyi nake ji kar in yi ma kai na illa haka kawai" daga hka ya fice daga palon, junaid ya bi bayansa ya fita ya kulle gidan. Har suka isa gidan El-Ameen bbu wanda yace komai sae Junaid dake juyawa lkci lkci yana kallon mahaukaciyar, El-Ameen ya dauko makulin gidan dake motarsa ya fita ya bude gate don bbu kowa gidan, dawowa yyi cikin motar ya shiga compound din da motar, yana gama parking ya juya yana kallon Junaid yace 'Ohhw ni! yanxu mahaukaciya ce mace ta farko da xata fara shigar min gida bayan mahaifiyata maimakon matata" Junaid bae tanka sa ba, El-Ameen yyi tsaki yana girgixa kai ya fito daga motar ya nufi cikin gidan, Junaid ya fito ya bi bayansa, a balcony ya tsaya ya canxa change over din gidan don akwae wuta, ya juya yana kallon Junaid yace "Toh ni xan fito maka da mahaukaciyar?" Junaid ya girgixa kai ya juya ya koma gun motar, bae sha wahalan daukota ba don sosae El-Ameen ya daureta kuma duk tayi laushi, ihu take tana shure shure har suka shigo falon ya direta k'asa yana kallonta, El-Ameen ya rike haba yana kallonta yace "Ikon Allah, muna xaman xaman mu Junaid ya ja mana!" Juyawa Junaid yyi yana kallonsa, El-Ameen yyi tsaki ya nufi stairs, Junaid ya lumshe ido ya bude ya bi bayansa, daki ya samesa ya bude drawern kayansa da alamar kaya xae canxa, Junaid yace "It's late ynxu, muyi freeing dinta sae mu wuce koh" El-Ameen yace "wait tukun! Wae kai xaga dinga tsayawa da ita a gidan?" Junaid ya d'an yi shiru yana kallonsa, sae kuma ya sauke ajiyar xuciya yace "No, xan sa a samo min yar dattijuwa dat will be staying, nd I will hire a gate man" El-Ameen ya kyabe baki ya cire jikakken shirt din jikinsa da wando ya fiddo wasu kayansa ya sa, sae a snn ya juya ya kalli Junaid da ke xaune gefen gadon dakin yana kallonsa yace "Kai baxa ka canxa kaya ba?" Mikewa Junaid yyi ba tare da ya kallesa ba ya fice daga dakin, dariya El-Ameen yyi sanin haushin sa kawae Junaid ke ji. *Sai dai da aka rushe katangar Chinan dai, ko wani katanga xan kuma cewa Allah yayi min da su*