← Book details Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 104

Sashe 13

Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta fashe da dariya har da rike ciki. Da yamma Junaid na kwance palon Mumy bayan ya dawo aiki idonsa lumshe kamar me bacci sae dai ba baccin yake ba, Mumy kuma na kitchen tana ta girke girke don ranan Abba xae dawo, Bude kofar da aka yi ya sa shi bude ido, El-Ameen ya shigo palon da sallama, kallonsa kawae Junaid k e yi bae ce komae ba, El-Ameen ya karaso palon yace "Capt A.jay Murnai!" Da xolaya ya kare kiran nasa, Junaid ya mike xaune yace "Uhm!" Kitchen El-Ameen ya nufa ya tsaya daga bakin kofa yace "Ina yini Mumyna" juyawa tayi tana kallonsa tace "A'a Ahmad yaushe ka shigo?" yayi murmushi yace "Yanxun nan Mumy, ya gida ya aiki" tace "Alhmdllh, ya Hajiyar ka?" El-Ameen ya karasa shiga kitchen din ya mata side hug yace "Tana lfya Mumy, tace a gaishe ki" Mumy tace "Ina ta sa rana xan je can gidan ku Allah bae yi ba" El-Ameen ya sa hannu ya dauki daya daga kajin da take soyawa yace "Bari in d'an d'ana maki ko gishiri ya ji Mumy" dariya tayi tace "Naga alama" ya wara ido ya fice daga kitchen din yana murmushi, gefen Junaid ya xauna yana cin kaxar Junaid xae yi magana aka bude kofa, Hajja ce ta shigo palon da sallama, El-Ameen ya wara ido ya boye fuskarsa bayan Junaid yace "Kai yaushe Hajja ta xo?" Hajja ta cire glass din idonta tana leken El-Ameen tace "Wannan ba gantalallen nan me sunan ka bane Amadi?" El-Ameen yayi dariya yace "Ehh Nine Hajja, ashe kin xo, ae bae gaya min ba" Hajja tace "Toh ko ya gaya maka xuwa xa ka yi, kar ka manta turare ne fa yayi mani iyaka da kai, daga nace ka siyan turare na xama makiyiyar ka, toh Allah yayi mana tsari da irin ku" dariya sosae El-Ameen yayi, Junaid yayi murmushi yana canxa tashan tv, Hajja ta xauna tace "Har yanxu Muhammad din bae iso bane?" Mumy ta fito daga kitchen tace "Kila sae xuwa magariba Hajja" mikewa Junaid yayi ya kwashi wayoyinsa yana kallon El-Ameen yace "Mu je" El-Ameen ya mike, Hajja tace "Au don na shigo shine xa ku watse" Junaid ya balla mata harara yace "Da'alla! Rikicin tsufa ya maki yawa wllh" El-ameen yace "Kyalesa kawai Hajja ta so mu je kar ayi ba ke" Junaid yace "Allah kar ta xo min don rufe kofata xan yi" daga haka ya nufi kofa, El-Ameen ya bi bayansa yana dariya, ta tsuke fuska ta bi su da kallo tace "Wahalallu ko uwar me xasu ban da Allah bai ban ba, kuma naga dai gidan d'ana ne yau nace duk ya kora ku wllh ta xauna!" Mumy tayi murmushi ta koma kitchen. kwanciya El-Ameen yayi a palon Junaid yace "Kana ji na Capt?" Junaid yace "Ina jin ka." "xa ayi diagnosing din patient din ka don in san irin neurological disorder dinta da treatment din da ya kamata in mata, nd dat's money!" Junaid ya dauki remote din hannunsa yayi powering din Tv yace "Aiit! Nawa ake bukata?" El-Ameen ya mike xaune yace "ka turo dubu dari tukun mu ga" Junaid yace "Ohk I will transfer it ltr" El-Ameen yace "Gud! Ko gida xan sa a xo ayi diagnosing din nata, no need of taking her out" kai kawae Junaid ya gyada masa, "Kaga daga nan sae mu san irin uban kudin da xaka kashe" da xolaya El-Ameen ya kare maganar, Junaid yayi murmushi bae ce komae ba. *Haske Writers Association* *Captain_Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 10.... Har Abba ya dawo bayan magrib El-Ameen na gidan, suna gama cin abinci da Junaid suka tafi palon Abba a tare don yi masa sannu da dawowa, Hajja na xaune palon da Hajiya da Umma, Humainah da fatima ma na xaune daga gefen Abba dake ta sauraran xancen da mahaifiyarsa ke masa, khadija da sadiya step sister dinta ma duk suna xaune palon, junaid da El-Ameen suka samu waje suka xauna, El-Ameen ne ya soma yi ma Abba sannu da xuwa ya gaishesa, Abba ya amsa murmushi dauke fuskarsa yace "Kana lfya son? Ya aikin?" El-Ameen yace "Alhmdllh Abba, ya hanya?" Abba yace "Alhmdllh mun gode Allah, jiya mun yi waya da Alhaji Mahmoud yace xae tafi Germany gobe" El-Ameen yace "Ehh gobe xae tafi" Abba yace "Maa sha Allah, Allah ya tsare" Junaid ya kalli Abbansa yace "Barka da dawowa Abba" Abba yace "Yauwa Ahmad, how yhu?" Junaid ya shafa kansa yace "Alhmdllh Abba, ya hanya?" Hajiya ta d'an tabe baki ta mike, Umma ma ta mike ta fice daga palon. Hajja ta bi su da kallo sannan tayi tsaki ta maida dubanta kan Abba tace "Ni dai Muhammadu matan nan naka basa min abun arxiki wllh, tun da na xo ko ruwan su ban gani ba sai daxu da safe, Amina kadae ce 'yar arxiki take ta dawainiya da ni" siririn tsaki can kasa Sadiya ta ja tana hararan Hajja ta gefen ido ta mike ta fice daga palon. Murmushi kawae Abba yayi ya maida dubansa kan Humainah dake gefensa a kasa yace "ya karatu Humainah? Ss3 xaki yanxu koh?" Hajja ta karbe tace "Ehh ajin karshe xata, tana gamawa sae a hada aurensu da Amadidi sai taje can ta kare karatun a gidansa" da sauri Junaid ya kalli Hajja ya wani hade rae, ita ma Humainah kallon Hajjan ta ke kamar xata yi kuka, El-Ameen ya fashe da dariya, Abba kam murmushi yayi ya kalli Humainah da har hawaye ya cika idonta yace "Kyale Hajja dotana, wanda kike so xa a aura maki kin ji, kuma sae kin fara jami'a ma xaki yi auren," tana goge hawayenta tace "Toh Abba" Junaid ya harari Hajja da ta sake baki tana kallon Abba ya dauke kai, Abba ya kallesa murmushi dauke fuskarsa har lkcn yace "Ae ni baxan ma 'ya yana auren dole ba Hajja, duk abinda suke so shi mu ma xa mu so," murmushi Junaid yayi ya mike yana kallon Hajja da ta wani hade rai, ya kalli El-Ameen yace "Tashi mu je" El-Ameen ya mike yana dariya suka yi ma Abba sallama suka fita daga palon, Hajja tayi kwafa tace "Toh zan ga ko kai ka haifeni kuwa," Bakin mota Junaid ya raka El-ameen yace "Gud nyt!" El-Ameen yace "Aitt, saura kar ka xo can gidan gobe!" junaid yayi murmushi bae ce komai ba, sai da El-Ameen ya ja motar ya bar wajen snn junaid ya juya ya koma gida. Part din Mumy ya shiga ya tarar tana bathroom ya fito ya nufi nasa bangaren. Washegari ya kama Sunday Junaid na gida baya duty, kwance yake palon sa misalin Karfe goma da rabi na safe Khadija ta shigo palon, kasa ta xauna kusa da kujeran da yake tace "Gud morning ya A.jay" yace "Morning baki je islamiyya bane" tace "daxu ae anyi yayyafi shine Abba yace in bari gobe," yace "Keep quiet ba cikin ruwan fatima da Rabi'a suka tafi ba, ina ga gishiri ce ke koh, continue deceiving ur self" shiru ta dan yi tana turo baki sae kuma tace "Ae da yamma xan je" bai tanka ta ba, tayi kasa da murya tace "Yaya dama plss 5k xaka ban xan siya wani takalmi ne plss" wani uban harara ya watsa mata yace "Tashi ki bar min Palo, ke baki da aiki sae dae a baki kudi, beside kije ki samu Abba mana, get out my frnd" marairaice masa tayi tace "Don Allah fa yayana" xae yi magana aka bude kofa Suhaima ta shigo palon cikin wasu shegun English wears lokaci daya wani shegen kamshi ya bade palon, mikewa xaune yayi yana kallon Khadija yace "Naji! naji tashi ki tafi" Khadija tayi murmushi tace "Yauwa ya A.jayy nagode" ta mike ta hade rai tana kallon Suhaima tace "Toh ae sae mu je koh" wani kallo Suhaima tayi mata tace "Wa kike gaya ma haka" Khadija ta ja tsaki tace "Duk inda mutum yayi sae ayi ta bin sa da'alla" bata rufe baki ba Suhaima ta fixgota ta sauke mata mari, Khadija ta dafe kunci tana kallonta, mikewa Junaid yayi ya karaso ya bude kofar ya fixgo Suhaima ya wulla ta waje cikin kakkausar murya yace "Kada ki sake taba ta" Umma dake balconyn ta xaune tare da Hajiya ta mike da sauri ganin abinda ya faru, Hajiya ta bi bayanta da sauri ita ma, a fusace ta karaso bangaren Junaid tana huci tana kallon Junaid dake tsaye bakin kofa har lokacin tace "Kai Ahmad uwar me tayi maka xaka jefota haka kamar pillow?" Suhaima ta fashe da matsanancin kuka, hakan ya kuma harxuka Umma cike da masifa da bala'i tace "Ba magana nake maka ba" kallonta kawai yake bai ce komai ba, idonta ya kankance don fitina ta juya tana kallon Suhaima tace "me ya faru, me kika yi masa?" Suhaima na matsar kwalla ta gaya mata, Umma ta xaro ido tana kallon Khadija dake tsaye bayan Junaid a tsawace tace "ke har abun farin cikin ki ne bare yayi ma 'yar uwar ki wannan cin mutuncin Khadija, to don uwar ki fito kar in karya ki palon nan, Shegiya me halin banxa, fito nace" Hajiya tace "Ke dae sallamammiya ce wllh khadija, munafuka wawiya kawai" Hajja ce ta leko jin surutai, ganinsu tsatstsaye part din Junaid ta fito da sauri ta karaso tana tambayar me ya faru, ko kallonta su Umma basu yi ba, Umma na kallon Khadija tace "baxa ki fito ba sae na maki lahani a palon nan?" A fusace Hajja tace "Yau na ga bala'i, ta ya xa ki ce ta fito palon d'an uwanta, ke kin isa ki shiga tsakaninsu?" Hajiya ta tabe baki ta dauke kai, Hajja ta karasa balconyn tace "Me ya faru khadija?" Khadija tace "Wae fa Hajja Suhaima ce ta mareni shine ya Junaid ya koreta palon, shine fa take kuka haka" Hajja ta xaro ido tace "Ta mare ki? Toh Muhammadu ya fito ayi ta ta kare yau, duk ko wannensu ya kwashe agololinsa a gidan nan don ba gidan ubansu bane nan din, shima maganinsa knn da auren xawarawa, haka kawae xa a sa mashi 'ya ya a gaba, kuma bari kiji abinda baki sani ba Bilki, wllh Khadija ta fi kusanci da Ahmadu
Chapter 13 · 0% Book details