Sashe 27
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya gyara mata kwanciya ya mike ya shiga bayi, duk wannan abun Junaid na kallonsu, ya dawo dakin rike da bowl din ruwan sanyi ya bude closet ya ciro towel karami da babba ya saka karamin cikin ruwan bowl din ya dawo kan gadon ya ajiye bowl din kan bedside drawer, ya dagota yana kallonta don idonta biyu, ya dawo da bowl din ruwan gefensa ya matse ruwan towel din a hankali yana goge mata forehead dinta da shi, kara ta saki xata sauka ya hade rai yace "Wait!" Bata kuma yunkurin saukan ba, haka ya ci gaba da goge jikinta da yayi xafi sosai da towel din yana mata sorry, mikewa Junaid yayi, El-Ameen ya juya da sauri ya kallesa sannan yayi saurin rufeta da bargo yace "Ohh you weren't sleeping dama" Junaid bai tanka sa ba ya dauke bargon da ya shimfida kasa ya mayar cikin closet, El-Ameen ya tabe baki yace "Ni ban ma yi tunanin xan dawo in same ka ba Mumy's boy, theatre muka shiga da Abba and we came out few minutes ago, saboda nasan condition din patient dinka shi yasa na fito cikin daren nan, I ought to...." jin anyi banging kofa El-Ameen ya kalli kofar da sauri don dama yana magana ne yana matse towel a ruwa, murmushi yayi ganin ficewa yayi, ya ci gaba da abinda yake, har sai da yayi make sure temperature dinta ya dawo dai dai, still yayi ganin hawaye idonta, ya sunkuya a hankali ya goge mata fuskar yace "Am sorry Jewel, am only helping" sauka yayi daga kan gadon yaje ya xubar da ruwan ya shanya towel din a bayi ya fito, bacci ya sameta tana yi a yanda ya barta, ya gyara mata kwanciya sannan ya hada allura yayi mata da kyar don a tsorace ta farka ta fara kokuwa da shi, sai da yaga ta koma bacci sannan ya fita dakin ya shiga master bedroom duk a tunaninsa xae tarda junaid nan, sae yaga otherwise, tabe baki yayi sanin yana parlor knn, ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya canxa kaya yayi kwanciyarsa dakin, sai dai before dawn yaje dubata ya fi sau goma duk da a shigowarsa na uku ya tarda mama jummai a dakin, Karfe biyar da minti arba'in ya sauko parlor ya tarda Junaid xaune kan darduma, xaunawa yayi kan kujera yana kallonsa yace "A parlor ka kwana kenan?" Junaid ba tare da ya kallesa ba yace "Yea!" El-Ameen yace "Ohk, gud morning, yanxu dai you need to transfer some money into my account xuwa later akwae drugs din da na mata prescribing, and you know wat? Suna da tsada gaskiya or I shud just text you their names, tell you where to get them, kaje da kanka ka siyo, if you need my assistance let me know" El-Ameen ya kare maganar yana d'aga kafada, Junaid ya mike ya dauke darduman da yayi sallah yace "nawa ne kudin?" El-Ameen yace "100 nd 50k will be enough" Junaid yace "Alryt" ajiye darduman yayi kan kujera ya kalli El-Ameen yace "Na tafi, I will transfer it later in the day" bai jira cewarsa ba ya nufi kofa ya fice daga parlorn, makullin motarsa ya ciro a aljihu ya fita waje inda ya ajiye motarsa ya bude ya shiga ya kama hanyar gida, driving kawae yake amma gaba daya hankalinsa ba ya tare da shi, bai san yanda xa su kwashe da Mumy ba, toh ina ma xai ce mata ya je, gidansu El-Ameen? No yasan xata iya kiran Ummi, murmushi yayi yana tunanin randa xae samu freedom, don ya fara damunsa yanxu on like before, a waje yayi parking ya fito, gabansa ne ya fadi ganin Abbansa alamar daga masallaci yake, da kyar ya ja kafa ya isa gun gate ganin Abba ya tsaya har ya risina xai gaida Abba, Abba ya dakatar da shi yace "Daga ina kake?" Yayi kasa da kai zai yi magana Abba ya juya ya shiga cikin compound, bin bayansa yayi har suka isa part din Abba, Hajiya ke ta goge goge a parlon, Abba ya xauna kujera yana kallon Junaid, a hankali ya xauna kasa ya juya yana kallon Hajiya dake kallonsa da d'an murmushi mai wuyar fassara a fuskarta yace "Ina kwana Hajiya" tace "Lfya lau Ahmad" sunkuyar da kai yayi, Abba yace "Daga ina kake Ahmad?" A hankali yace "Tare muke da El-Ameen Abba" Abba yace "Tare a ina?" Hajiya ta dawo cikin parlon tana girgixa kai tace "kwata kwata ni hankalina bai kwanta da abotansa da yaron nan wai El-Ameen ba, yaron da bai da nutsuwa ko maganan iyayensa bai ji, kusan duk dare sai ya shigo ya fita da shi, Ahmad baxae dawo gidan nan sai kusan sha biyu wani lokacin har daya, duk ina lura da yake ni ba mai nauyin bacci bace ka sani Alhaji, to amma kar mutum yayi magana ace hassada ko kuma ace don ba d'an sa bane, amma kwata kwata Ahmad ya sauya hali a gidan nan, jiya wllh wllh khadija ca tayi min mace ta gani a motarsa da magariban nan da ya fita, to ina yaje yake dawowa yanxu, kuma duk Hajiya Amina tana ganin abinda yake baxata ce komai ba saboda ta dauki son duniya ta daura ma yaro, meye amfanin haka, in ma aure yake so ba sai yayi magana ba, ae ba wae bai isa bane" tunda ta fara magana Junaid ya kafeta da ido ko kiftawa bai yi, Abba kuwa sai kallonsa yake bacin rai karara a fuskarsa. *Haske writers Association* *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 19..... Junaid ya sauke ajiyar xuciya ya lumshe ido a hankali bai dai ce komai ba, Abba ya kalli Hajiya yace "A kira min Aminar" da sauri Junaid ya bude ido ya marairaice masa yace "Don Allah don annabi Abba ka min duk abinda xaka min, amma bbu ruwan Mumy bata ma san bana nan ba, plss..." wani tsawa Abba ya daka masa, babu shiri yayi tsit, Hajiya ta juya ta nufi kofa lebbenta dauke da wani murmushi, ba a dau lkci ba ta dawo tace "Suhaima ta tafi kiranta" Abba bai ce komai ba ta nemi waje ta xauna tana girgixa kafa tana tabe baki, ba a dau lkci ba Mumy ta shigo parlon da sallama, sai dai duk jikinta yayi sanyi ganin junaid xaune parlon tasan ba abun arxiki ya sa aka kira ta ba, kujera ta samu ta xauna tare da gaida Abba. Bbu yabo bbu fallasa ya amsa, junaid ya k'asa dago kai ya kalleta duk jikinsa yayi sanyi, Abba yace "Ke a tunanin ki so kike nuna ma yaron nan koh Amina, har ya kai matsayin da Ahmad baya kwana gida yanxu shi ba nyt duty ba kika xuba masa ido koh, toh dama an sha gaya min ban yarda ba amma yau idona ya gane min komai, don haka ni baxan bari ya dauko min abun kunya ba ina xaman xama na, just few weeks na basa ya fito da mata idan ba haka ba xai sha mamaki na wllh....." Mumy da har idonta sun cicciko ta kallesa cike da takaici tace "Alhaji kar ka manta Ahmad ba mace bane da har kake tsoron ya dauko maka abun kunya, kuma mace ake ma kulle ba namiji ba, ko yau ya ga bai son xaman gidan nan yana iya barin sa ya koma duk inda yake so don namiji yake ba mace ba kuma ya mallaki hankalin kansa, ni na haifi Ahmad na kuma fi kowa sanin halinsa ko rantsuwa nayi baxan yi kaffara ba baxai aika ta mugun kaxamin kaxafin da ake son lika masa ba, I know my son" hawaye na bin kuncinta ta kare maganan, Hajiya ta bude baki ta saki salati tana tafe hannu, Abba ya mike fuskar nan tasa a murtuke yana kallonta yace "lallai Amina wato ni ke masa kaxafi kenan koh, to bari ki ji, wllh sati uku na basa yayi aure ya bar min gidana idan ko ba haka ba xai gane matsayina a gun sa" mikewa Mumy tayi tana kallonsa tace "Toh sai me, bai isa auren bane!" wani kallon Allah wadaran shaidanin mutum ta jefa ma Hajiya ta fice daga parlon, Hajiya ta dinga salati tana cewa "kiri kiri mutum yasan gaskiya ya danne don bai son laifin d'an sa, Allah sarki duniya" Abba ya kalli Junaid yace "Ka dai ji me nace maka, sati uku na baka wllh, get away" mikewa Junaid yayi da kyar ya fita daga parlon kansa na juya masa, part din Mumy ya shiga ganin bata parlor ya shiga bedroom dinta, xaune ya sameta gefen gado tayi tagumi, ya durkushe gabanta, ya daura kansa bisa kafarta cikin sanyin murya yace "Don Allah forgive me mum, it wasn't my intention disobeying you yesterday, I.. I am sorry mother forgive me plss" jin bata ce komai ba ya dago idanuwansa da suka kada yana kallonta, kamar xae sakar mata kuka yace "Plss Mumy kiyi hakuri!" "Ina ka tafi jiya?" Ta jefo masa tambayar tana kallonsa, rasa abinda xai ce mata yayi Cause he is not dat gud at lying, yanxun nan sae ta gano sa, ya kalli agogo, kallon agogon tayi ita ma taga bakwai saura ta d'an sauke boyayyen ajiyar xuciya tace "Tashi ka tafi" a hankali ya kamo hannunta yace "Plss Mumy kiyi hakuri nace" a nutse tace "Leave!" Ya kusa minti biyu durkushe gun sannan ya sake hannunta ya mike a hankali ya juya ya fita daga dakin ya shiga part dinsa. Cikin minti ashirin yyi wanka ya gama shirinsa, ya fito sae dai da ganinsa kasan bashi da nutsuwa, part din Mumy ya koma, ya sameta tsaye dinning tana jera masa breakfast, karasawa yayi yana rike da hularsa, Mumy ta bar dinning din, sosai jikinsa yayi sanyi ya ja kujera a hankali ya xauna ya dau mug din tea'n da ta hada masa ya shiga sha ba don yana jin sha ba, tea kawae ya iya sha ya mike ya dawo parlor yana kallonta yace "Xan tafi aiki Mumy" tace "baka ci dankalin ba, wa ka bar ma? go back and eat it yanxu" ba musu ya koma ya d'an ci kadan sannan ya kurbi ruwa ya dawo yace "Na ci