Sashe 9
A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
inda karfina yakare xan nemi soyayyar yaya khalifa bakin raina zanyi duk abinda zan iya don ganin na mallake shi ba zanyi sakaci wata d'iya mace tarabani dashi ba ko ta halin 'ka'ka. Tami'ke a hankalin ta tsaya gaban madubin dake bango tana kallon kanta tun daga sama har kasa, doguwar rigace a jikinta wadda tafito da zahirin suffar jikinta, gashin kanta ya sauka har gadon bayanta, kamar yadda take doguwa mai kyau siffa tana daga cikin abinda yake dauker hankalin maza tare da ummi shi ne gogewar fatarta, ba fara bace 'kal 'kal amma tana da haske sosai, fuskarta tanada daukar hankalin mai kallonta, sannan tana da daukar dressing in dai za tasa kaya sai sun amsheta sbda ba zai yiwu tasa kayan dabasu dace da kalar jikinta ba, haka duk d'inkin dazatayi sai ta tabbatar zaiyi mata kyau sbda ita Allah ya yi ta da iya zabar kaya dan shi kanshi telanta daban ne shi yake mata tsala tsalan dinkuna nagani, duk kayan daza tasa sai an tabbatar an yi matching dan a birge ai kuwa tana birgewar, ko a salon iya tsara magana aka tsaya musamman ummi za tatafi da imanin mutum yatsaya yasaki baki yana kallonta yadda za kaga tana tsara xance daya bayan daya mai shiga cikin wannan ne yasa takeda mutane a gida da makaranta, hatta malamansu sun santa kan tsananin iyayinta da son gayu duk kudin da hajiyarta tasamu akan sayawa ummi sutura mai tsada da kayan kwalliya suke tafiya kowanne kya sai an hada mai mayafi, takalmi da fashion don ace dai an yi kyau. Ummi tana matukar jin kanta ba kowani d'a namiji take kulawa ba duk da dumbin masoyan dake nuna mata zahirin kauna ba wani d'a namiji daya taba burgeta sai yaya khalifa. ************** Jidda ce kawai ta 'kud da 'kud kuma aminiya ga ummi tun suna yara ba ajin kansu kasancewar katanga ce kadai taraba gdansu kafin rasuwar mahaifin ummi baida abokin shawara kamar aminin daya wuce babansu jiddah shi ne dalilin dayasa zumuncin na su yakara kwari, duka makarantun dasuke zuwa guda uku a kowacce rana duka ajinsu daya kullum tare suke wuni babu abinda yake rabasu sai bacci, kullum shawararsu daya banbancinsu shi ne jiddah ta fi ummi tanada tsiwa da jin kai da raina mutane, yayin da jiddah ke da girmama mutane da gudun zuciya. Iyayan jiddah hamshakan masu kudi ne su biyu suka haifa daga ita sai yayanta Habibullah wanda yake kasar england karatu, itama jira suke takammala secondary su fidda ita kasar waje tayi karatun ta na jami'a dukda cewa ta ce babu inda za taje sai fa in za a hadasu da aminiyarta ummi, lokacin data fadi haka mominta ta yi murmushi ne tace "jiddah manya, jiddah aminiyar ummi, idan har ummi da iyayanta sun amince za ta outside karatu mai zai hana dady dinta yabiya mata insha Allahu indai kinga ummi baku tafi tare da ita ba ,ita ko iyayanta suka ce ba za ta ba. Cikin tsananin farin ciki jiddah tashigo gdansu ummi dagudu ta isketa cikin dakin hajiya tana kwance bisa gado tana karatun littafin hausa tafisge littafin ta watsar tace "Albishirinki. Ummi ta lumshe ido tace "kina burgeni jiddah sbda koyaushe ina ganin ki cikin nishadi da wahala mutum ya fahimci wata damuwa a zuciyarki. Tace 'hakane ummi ban cika sa wani abu a azuciyata ba ballantana yadameni ina daukar raywa da sauki dan kada in dami zuciyata zuwa nayi in gaya miki insha Allahu idan mun gama secondary tae za mu tafi outside karatu. Ummi tayi shiru batace komi ba fuskarta ko walwala babu ballantana tanunawa jiddah ta ji dadin maganarta, itama jiddar gimtse far'arta ayi tace "ummi yaya ni dana taho da batu mai dadi gareki ina mai gaggawar yi miki albishir sai inga fuskarki ta ahiga damuwa kamar wadda tazo miki da labarin tashin hankali ? Ummi tayi doguwar ajiyar zuciya tace "jiddah ba wai farin cikine banyi ba ba yadda za ayi ayiwa mutum albishir irin wannan yakasa farin ciki sai dai inason kiyi hakuri jiddah na gode kwarai da gaske da kaunar dakike min wadda tasa har kike jin ba za ki iya tafiya wani gari kiyi rayuwa babu ni ba, iyayanki suka amince miki akwai haka tare Dacewa kudi za su kashe ba na wasa ba, babu inda za ayi haka sai in akwai kauna mai yawa kuma kauna wadda take ta gaskiya sbda Allah to sai dai inda gizo ke sakar shi ne jiddah kiyi hakuri, zuciyata ta yi nisan kiwo a cikin soyayyar yaya khalifa, ba zai yiwu bayan kammala secondaru din mu in bar kasar nan zuwa wata kasa ba ba tare da na san matsayina a zuciyarsa ba. Ba tare dani ba duka hanyar da ta dace nabi don in nemi soyayyarsa ba don in nemawa kaina masauki na din din din a zuciyarsa. Tagyara zama har yanzu idanuwanta na kallon jiddah taci gaba da fadin "jiddah zuciyata tana yiwa yaya khalifa wani irin so wanda ban taba tunanin akwai irin son a duniya ba, ba zan iya bayyana miki irin yadda nake jin ciwon sonsa a zuciyata ba. Kullum dashi nake kwana in tashi kullum soyyayarsa karuwa take a zuciyata ban kuma samu mafita ba akan yadda zan bullowa lamarin har gashi tafiyarsa germany ta matso. Tun a yanxu ban samu mafita ba inaga in yatafi tafiyar dazata dauke shi shekaru hudu. Ina matukar tausayawa rayuwata jiddah ban san halin da zuciyata za takasnce ba yayin dana rasa yaya khalifa.... . Jiddah takamo hannunta cikin tausaya wa tace "ki kwantar da hankalinki ummi in dai yaya khalifa mijinki ne da izinin Allah za ki aure shi, in har baki auri khalifa ba to Allah ne bai kaddara aure ba ba za ayi ba, shi ne amfanin daukar rayuwa dasauki. Ummi hakika na san yaya khalifa miji ne abin so gakowacce irin d'iya mace kowa cece ita kuwa, ko ni kaina din nan abinda yasa nake nesanta kaina daga burgewar da yake min na san ya yi min nisa ne ba zan same shi ba, ke din ma bansan za ki tsanantawa zuciyarki matsananciyar soyayyarsa har tashafi duk rayuwarki ba, da tun farko ban zungure ki da maganarsa ba, ko dacewa kina sonsa daman chan a baya tun kafin in tuntubeki da maganar amma tuntubar danyi miki ita tajefa ki a wannan damuwar. Ummi ina mai ba ki shawara ta gaskiya akan ki dauki rayuwa dasauki duk abinda kika zafafa shi zafi zaiyi gareki Kuma ba wanda zai dagawa hnkli sai ke din. Ki cigaba da fafutuka akan neman soyayyar yaya khalifa har kiga kin aure shi amma dan Allah kada kibari damuwa ta lalata miki tunani ki dogara ga Allah sai komi yazo miki dasauki. Ummi bata kara cewa da jiddah komi ba har aka fara kiraye kirayen sallan magriba tayi mata sallama takoma gdansu, dakyar tatashi tayi sallah taci gaba da zama a daki kan daddumar datayi sallah tana jan carbi tayi tagumi idanunta sunyi jawur. Hajiya hauwa taahigo dakin ta sha adon ta kamar yadda tasaba kai bakace ita ta ajiye manyan samari irin su hassan ba, mace ce mai son gayu shi yasa ummi ke samun daurin gindin gayu da kece raini a gunta. Tayi sororo tana kallon diyar tata tace "ummi wai lafiya kike kuwa kwana biyun nan kin sauya ko ba ki da lfya ne? Ummi tadago ido zuciyarta ba dadi tace "hajiya zauna kiji wata magana. Dasauri tazauna ummi tace "hajiya barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa, yau zan fayyace miki damuwata dan kisamo min mafita a cikinta, hajiya zuciyata ta kamu da tsananin son yaya khalifa inaso kigaya min hanyar dazanbi yasoni. Hajiya tadafe kirji tare da fiddo ido tace "ummi kinsan maganar dakike fada kuwa? a duniya kirsa wanda za ki so sai khalifa? Kara gaya mini ko dai ba khalifan dana sani ba kika ce kina so? Ummi tamatso kusa dai tadora kanta akan cinyarta tace "hajiya babu wani khalifa dazan yi magana akansa wanda yawuce na mu ba zan iya raba zuciyata da son sa ba kuma ba na bakin ciki da son da zuciyata ke masa insha Allahu ba xanyi nadama ba mafita ce ban sani ba ita nakeso kisanar dani hajiyta. ************ Maganarta tadamu hajiya hauwa yau dai ba ta son mahaifiyar khalifa haka shi kansa khalifan ba kaunarsa take ba, a daran takira kanwarta hajiya sauda wadda ita ke binta ko gaisawa bata bari sunyi ba tace "saude tashin hankali ne ya saman a daran nan. Hajiya saude tace "har gabana ya fad'i "meya faru yaya hauwa? Tace "wai ummi tarasa wanda takeso sai wannan yaron mai shegen girman kan tsiya wanda ko kallo mutane basi ishe shi ba. Hajiya sauda tace "wai waye ne ?duk kin rikitani. Hajiya hauwa taja dogon numfashi cikin takaici tace "waye in banda khalifa. Hajiya sauda tace "to sai me dan ummi ta ce duk duniya babu wanda takeso sai khalifa, kada kibani kunya mana yaya hauwa kamar ba ke ba ko in ce kamar ba mu ba? Hajiya hauwa tace "uhm saude dole hankalina yatashi kina kallo fa yadda rayuwar yaron nan yake, ko kallo mutane basu ishe shi ba, gaisuwa da yake mana ma dan ya zama dole ne a gareshi, in banda haka khalifa bamu isa yagaidamu ba ni kam ba khalifa da uwarsa na tsanesu ba zan taba kaunarsu ba shiyasa da ummi tabudi baki tace min ba ta da gwani wanda yawuce khalifa hankali na yayi mugun tashi nayi gaggawar kiranki a waya dan musan abin yi. Hajiya sauda tayi murmushi tace "Allah sarki yaya hauwa ni ko da kika gaya min maganar nan sai naji zuciyata ta yi 'kal 'kal, na jima banji maganar data faranta min rai irin wannan ba. Hajiya hauwa tayi tsaki tace "ke da Allah ana ga yaki ke kina ga kura me za muyi khalifa, yarinyarn nan ummi duk dan abinda na samu a gun kayan kwalliya suke tafiya don dai musamu gallelen alhajin birni mu darje amma ta lalace kan khalifa, wannan sangartaccen yaron da bai san yafita neman na sa ba sai dai dukiyar ubansa dasuks jiku a ciki shi da uwarsa. Hajiya hauwa tace, "to sai me idan khalifa bai nnemi na