← Book details A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 50

Sashe 10

A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sa ba sai na ubansa? dama me muke nema ne? burin mu dama aibai wuce musamu wani ba ko d'an wani, to bamu samu wanda yake wanin ba ai a karan kansa sai dan wani to dawani da d'an wani in dai za mu shaki dukiya ai mu burinmu ya cika. Hajiya saude tayi ajiyar zuciya tace "to in banda abinki saude taya za mu iya mallakar wannan yaron mai masifar girman kan tsiya, zancan danake miki fa a satin dazai kama idan Allah ya kaimu zai tafi germany karatu sai ya yi shekaru hudu zai dawo, na ji uban abban hajiya yana gayawa jummai wai so yake yazama cikakken likitan mata, don haka karatu yakeso yayi a germany mai zurfi. wlh saude idan kinji kudin da muhammadu yakashe akan wannan tafiyar na khalifa sai kin rike baki sai hankalina ya kasa karba inda zai zauna ma tsawon wannan shekarun hudun da aka zuba akan su ya ishe irin mu mumore mun gama arziki a duniya dai. Wai amma jummai maimakon tai mashi fada yarage kashe kudi haka akan khalifa sai fadi take ya yi daidsi. Hajiya saude tayi murmushi tace "to ko anan za kisan lallai auran ummi da khalifa shi zaisa mu mallake dukiyar alhaji muhammadu cikin sauki kinsan ana cewa daka haifa gwamna gwara kahaifi matar gwamna saita kawo maka gwamna har gida sai ka shekara kana yawan neman ganin gwamna ma baka ganshi ba amma idan kabi takan matarsa lokaci guda sai kaganshi ba tare da ka samu matsala ba sbda ita mace mace ce daban take, yanzu idan muka bi duk hanyar data dace gun cusa ummi a zuciyar khalifa shikenan mun mallaki khalifa, idan muka mallaki khalifa sai yadda mukayi dashi ko uwarsa bata isa tayi yadda takeso ba sai mu din dai. Da ba a so muci arzikin slhaji muhammadu kinga munci dan bakin ciki sai dai yamutu. Kuma anan ne za mu fanshe haushin da mukeji na hajiya maijidda uwar khalifa, tana ji tana gani za mu aurawa khalifa ummi za mu mallake shi 'kaf shi da dukiyar uban na sa tunda dama alhaji muhammad ba shi da tunani sai khalifa, idan ummi ta auri khalifa shi kuma zai kasance ba shi da tunani sai na ummi sai yadda mukayi dashi da dukiyar ta shi, hajiya maijidda tazama yar kallo yadda tamaida mu yan kallo mu da dukiyar dan uwanmu ba mu da iko akanta muna gefe sai abinda aka sammana me zai hana muyi farin ciki akan soyaygar da ummi ke wa khalifa, wannan itace hanya daya tilo da burinmu zai cika kuma za mu nunawa maijidda ita ba komi bace hancin gauta ce bata isa komi a miya ba. Hajiya hauwa tace "tabdijam amma fa kinyi tunani saude shi yasa ake cewa mai shawara ba ya aikin banza, tabbas gaskiya kika fada sai dai abinda nake jinjinawa shi ne tayaya za mu mallaki khalifa kidinga tuna masifar jin kansa fa. Hajiya saude tace "kash yaya hauwa ni kunya nakeji kamarki wannan maganar kalaman nuna karaya da gazawa suna fitowa daga bakinki, khalifan banza khalifan wofi har meye shi, wa yayi ma ballantana yafi wani ko za murasa zanin daurawa sai mun mallaki khalifa, sai mun shiga ko ina zamu shiga dan mu tura ummi gdan khalifa, matakin farko dazamu fara dauka shi ne ummi za takoma gdansu khalifa dazama, hikimar yin hakan shi ne a matsayinta tamace wadda takai mace muka dade muna koyar da ita kissa da kisisinar jan hankalin namiji tabi hanyar duk data dace tafara kafa gwamnatin ta a zuciyar khalifa kafin tafiyarsa germany a wadannan gajerun kwanakin 'kididdigaggu, ko yaya ne mu tabbatr khalifa ya bar kasar nan ne da tunanin ummi ba wai soyayyarta ba. Kafa soyayya a zuciyar wanda kwata kwata hankalinka ba ya kansa abu ne mai wahala sai a hankali, lamari ne da ba ayi masa gaggawa a cikin lamari irin wannan to ko shakka babu ba zai ci nasara ba, ana kaddara cewa mutanen dasuke cin nasarar abubuwan dasuka sa gaba na rayuwa su ne masu hakuri a dukkan lamarinsu. Sbda ita nasara kafad'a da kafad'a suke tafiya da hakuri, ballantana lamari irin wannan ba abu bane mai wahala amma fa ga mace datasan abinda take wadda takaranci halayyar d'a namiji, kada ki jinjinawa ummi jin kan khalifa har jikinta yayi sanyi, ki kashe mata guiwar taji cewa ba za ta iya ba ,ko da tanajin cewa ita d'iya mace ce da za ta iya jan hankalin d'a namiji ko waye shi, idan kika jinjina al'amarin itama girmama zaiyi a zuciyarta daga nan sai ta kasa yin komi sai asarar tashafe mu baki d'aya. Amma idan kika nuna mata ba kowane khalifa face namiji kamar kowa shikenan saita ka ra samun kwarin guiwar kokarin janyo hankalinsa har muyi nasara. Yadda za ayi takoma gdansu khalifa da zama kuwa wannan sai idan Allah ya kaimu wayewar gari gobe lfya idan nazo sai musan abin yi. *************** Ba kowa a gidan sai fatima ita kadai, sauran kannanta suna makaranta yayin da goggonsu Abu tatafi barkan haihuwa da akyi musu, ta karasa tankadan garin tuwon datake takai kitchen tashare gidan tadora ruwan tuwon sannan takoma kan tabarma tadauki wani littafi na addu'a tana dubawa maisuna Du'a'ul mustajaba. Zuwa can ta ajiye ta kwantar danta kan pillow tana tunanin auran da za ayi mata da malam musbahu nan da lokaci kadan har yanzu dai malam bai yanke lokacin da za ayi bikin ba haka zalika musbahu bai taba kiranta da sunan zancan ba, kunyarta yakeji kamar yadda ita matake bala'in jin kunyarsa, kafin malam yafurta cewa zai hada su aure, malam musbahu ba wanda yafi shiri da shi a yaran gdan sai ita, tun tana karama musbahu ya fi kaunarta fiye da kowani d'a a gidan nan duk abinda yasamu kafin yaba kowa sai ya ba ta har sai da mutane suka shiga zargin ko dai son ta yakeyi, ganin bai furta ba yasa aka watsar haka itama take bala'in kaunarsa tun lokacin da bata sani ma musbahu ba dan gdansu baneballantana data mallaki hankalin kanta tagane musbahu maraya ne yahadu da zaluncin matar kawunsa har malam ya amshi ragamar rigimar rikonsa, sai tausayinsa yasa take ka ra kaunarsa suka rike shi tamkar dan gdansu, in banda wannan lokaci da malam yake gayan mata, da ya gayawa mutanensa cewa zai ba wa malam musbahu auran diyarsa fatima sannan dayawa wasu suka san ba malam bane yahaifi musbahu ba sbda yadda malam din da ita goggo Abu din da yayansu ke matukar ji da musbahu shi ma haka yazamo dan halak agaresu ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya gun soyayya a garesu, kyautata musu tamkar su suka haife shi, koda yake ako da yaushe yana gayawa malam cewa bai taba kaunarsa a matsayin iyayan riko ba kullum a matsayin mahifa yake daukarsu wanda ba shi da kamarsu a duk fadin duniyar nan kamr yadda yake da tabbacin suma haka suka dauke shi, rayuwa suke a gdan mai dadin gaske ga shi dai ba su da abin duniya sai rufin asirin Allah, abinda yakesa suke jin dadin rayuwa shi ne girmama junansu da kaunar juna da ake sbda Allah da tarbiyyar data ratsa duk d'an dayake na gidan ne, nisan da fatima tayi cikin tunani yasa har ruwan data d'ora bisa wuta ydinga tafsa tamanta dashi sannan mutum na tsaye a kanta bataji takunsa a lokacin daya shigo ba ballantana sallamar da yayi mata saida yatsuguna gabanta yace "fatima wani irin tunani kike haka kina yarinya karama mai kankantar shkaru haka ina ke ina wannan tunani? Kafin yagama rufe baki fatima tatashi dagudu jikinta na rawa za ta shige daki, musbahu ya mike shima yana murmushi yatare kofar dazata shiga yana murmushi yace "fati haka za mu zauna koda yaushe kina guduna kamar dodo tunda malam yace ya ba ni ke ban kara magana dake ba ko gaida ni ba kya zuwa kiyi ina dalili. kan fatima na kasa kamar za ta nutse a gun sbda kunya, tarufe fuskarta da tafukan hannayenta yace "je ki kigama tuwon kuma kada ki kona mana tuwo amma fa lallai yau ke za ki kawo mana tuwo ni da abokina mansur, idan har bazaki kawo mana da kanki ba ba na cin tuwon, idan kinyi kada ki aiko dashi zan kwana da yunwa, bai saurari abinda za tace ba yafice yabarta tsaye kamar an zare mata jijiyoyin jikinta tana kallon yadda ruwa ke tafarfasa akan wuta amma ta kasa tashi tayi talge, hankalin fati ya tashi kwarai da gaske idanunta suka cika da kwalla har ji tayi kirjinta ya yi mata nauyi numfashinta yana sama sama kamar zai dauke . Tun tasowar fatima babu wani d'a namiji daya taba cewa yana sonta ta amsa mai ballantana maganar soyayya ta had'a ta dashi shekarunta goma sha shida da haihuwa ajinta hudu a secondary, tun tana shekara sha biyar ake cewa ana sonta kasancewar ita yarinya ce da Allah yahorewa kyau ba na misali ba abin sai wanda yagani sannan tana da shiga rai yadda kasan wadda aka tsuma ta da maganin farin jini, in dai namiji zai ga fatima sai ya yi shaawar ace matarsa ce. sbda bayan kyaun ga natsuwa ko magana fati take ka san ta samu tarbiyya irin wanda duk d'a namijin arziki yake burin mallka a matsayin matar aure. Shigowar goggon ta Abu yasa tatashi dagudu tawuce 'yar rumfar kwanon dake gaba kitchen dinsu inda suke hura wuta, goggo tarike baki fatima yau me ya sameki sai yanzu ake talgen tuwo? kina sane dacewa ba na son ayi tuwon dare a gidan nan, fati bata saba karya ba don haka tai saurin kallon idanunta kadai, goggo dai ta san akwai abinda ke damunta yau abinka ga babba ballantana wanda yahaifeka, ta jima tana nazarin fuskar fatima sannan ta gyada kai tawuce daki. Har fati tagama tuwo a sanyaye jikinta yake ko magana akai mata dakyar take amsawa hatta shi kansa bakinta ya yi mata nauyi, bayan sun idar da sallar isha tana zaune kusa da goggo sanye da hijjabinta da charbi a hannun ta tana ja hawaye sai neman xubo mata sukeyi tana maida su dan kar goggon ta gane tayi mata tambayar da za ta gagara amsawa
Chapter 10 · 0% Book details