Sashe 49
A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya zaban min shi ne zabina nikam ba ni da zabi. Duk inda aka ce Allah angama magana gaba daya takashe musu jiki dole suka kyaleta. A DAREN FARKO 41 A wannan daren fatima *wana tayi tana kai kukanta ga Allh tana rokon yazaba mata mijin da zai fi alheri a tare da ita, da mutum biyun nan takwana a zuciyarta amma da usman ta tashi ba brriater b. Shi taji ya fi kwanciya mata a rai duk da cewa shi yana da mata amma hakan taji shi taji tafiao, don haka kai tsaye ta sanar da babanta cewa yab barrister hakuri ta tsaglyar da Usman a matsayin mijinta,suka sanya mata albarka tare da fatan Allah yasa hakan shi ne mafi alheri a tare dasu. Duk yan gdansu usman fatansu ftima ta ami? ce ta auri usman sbda ba karamar damuwa bace dashi a gdansa, ba kamar jidda wadda duk tafi kowa tsanar farida ko gaisuwa ba ta hadasu har faridan ta daina zuwa komi na danginsu itama ba mai zuwa inda take dama ba haihuwa ba ta mike kafa ne tana abinda taga dama. Lokacin daya samu tabbas daga mahaifin fatima cewa an bashi ita yaturo manyanaa, hannu yadaga yana wa Allah godiya, nan da nan aka kai kudin aure aka sa ranar aure nan da sati hudu daurin aure da biki gaba daya. Ya shiryawa fatima gda da lefe mai ban mamaki, har aka kusan biki farida bata sani ba domin yanzu yawonta ya kara kaimi tunda juma'a kawai usman ke zuwa kano yakoma abuja ran lahadi, sai da yarage saura kwana uku kachal daurin aure wata kawarta nafisa tazo gdan da yamma tace da ita. 'Farida anya kuwa kin san me ke faruwa dake naga kiba ma kikeyi ba kisan tashin hankalin daya tunkaro ki ba ko? Farida tayi mata wani irin kallo na rashin fahimta tace "me kike nufi. Nafisa tabude jaka tafidda katin daurin auren usman da fatima ta dora mata a cinya ya ta ce. "Karanta anan za ki fahimci me nake nufi. Farida ta tashi zaune hannu na rawa ta dauki kati ganin sunan mijinta yasa ta gwalalo idanu tace "nafisa a ina kika samu wannan katin? Tace "a gari mana ana nan ana ta rabawa jama'a na gayyata ni nasan tunda baki mana zancan ba jiya a gdan hajiya ladidi na san baki sani ba. Gumi yadinga ketowa farida ta kasa motsi sai numfashi take fitarwa da kyar dga bisani tatashi tace "nsfisa bar masa gdansa zanyi. Nafisa tace "wannan shi ne aikin banza harara a duhu, kina zaton yanzu kina gaban usman ne, idan ma kin tafi cewa zaiyi ya huta, tashi zakiyi yanzu muje gdansu amaryar mu ci mutumcin su muyi musu kaca kaca mu firgitasu ta ydda ba xa tayi sha'awar shigo miki gida ba, shi kuwa bakin munafikin idan yadawo ki nuna ki nuna mai hauka ki ganar dashi kuransa ta yadda zai shiga taitayin sa dole a fasa auran. Farida tazauna daram a kan wannan shawarar don jin zuciyarta take kamar za ta fashe. **** A ckin motar da usman ya siyawa farida suka fito tare da nafisa, farida ce ke tukawa fuskarta a tamke kamar za ta fashe tana ci gaba da daukar shawarar nafisa har suka isa kofar gdansu fatima kasancewar nafisan ta binciko komai. Cike da isa suka shiga, sukayi sa'a fatima ce kadai a tsakar gda tana wanke wanke. Mamaki ya kamata ganin mutane sun shigo musu gda ba sallama. Farida ta nunata da yatsa tace "ke ce fatima? Tace "eh ni ce lfya. Kawai fatin bata ankara ba taji farida ta cafko mata wuyar riga da karfi ta jijjiga ta tace "ni ce farida matar usman idan ma baki sanni ba yau ki sanni ganina ya fi ji na. Inna tafito dagudu daga bandaki tana salati tace "ke yar nan lfya za ki zo har gda kiyi mana tijara? Farida tasaki fatima tanuna inna da yatsa tace "ke yi min ahiru munafuka idan kina neman kai da wannan figigiyar 'yar taki ne ki kawota gdana kusha mamaki kwadayayyu kawai. Fatima tayi tsalle itama za tadamki farida, inna tariketa tace "kyaleta fatima duniya ce suk abinda kayi za ayi maka, kishiya dai duk bala'in ta za amata gda dai sai kin shiga takashe ki jahilar banza da wofi. Nafisa tace "ai ba cewa mukayi karta shigo ba, mun fi so ma tashigo mu nuna mununa muku su waye mu shi yasa yanzu muka fara zuwa har gda mu sanar daku. Farida tace "ga ku ga gdan usman nan daidai kushigo kugani idan idan kuna tsammanin barazana muke muku. Suka fice a fusace suka shiga mota, farida ta fizga da karfi suka fita daga layin suna kyakyata dariya. Karfe ukun yamma uaman yashigo gdan a gajiye yake sosai sbda yau shi yatuko kansa, tun daga hanya yake tunanin yadda zai fuskanci farida da maganar auransa, duk abinda ake ciki, ya sha alwashin yau zai sanar da farida, tun da aka fara batun auran tunanin dayake knan bai san tashin hankali gashi ita kuma anan takware. A falo ya sameta baiyi mamakin kin amsa mai sallamar datayi ba, dan haka shima bai kalleta ba yawuce da jakarsa zuwa dakinsa yashiga wanka. Farida tashigo a zafafe zu-iyarta kamar wuta don tsabar bala'i hatta idanuwanta sunyi jawur, idanuwanta suka fara dira kan wayarsa ta dauka hoton fatima ne yafara yi mata maraba ta sha ado ta yi kysu abinta har ba a magana. Wato ma har akan screen usman yake dora hoton fatima, batayi tunanin komi ba tadaga wayar ta dokata akan tayal ta tarwatse gaba daya, daidai lokacin usman yafito wanka hankalinsa yatashi dayaga barnar da farida tai masa, ya zubawa wayarsa ido mai tsaadar gaske yarasa abinda zai ce mata sai ya tsuguna zai kwashe sim din sa, ta daddage ta hankada shi tace "wa to ma ka maidani mahaukaciya ba ka a lokacin kulani ko? Ya tattara ta ya watsar gefe guda yace "Ba ki da hankali wa zai saurari marar hankali, abinda zan gaya miki ki gaggawar shiga hankalinki tun kafin ki jawa kanki abinda za ki zo kina nadama. Cikin daga murya tace "awai nadamar data wuce na aurankada nayi, ka cuceni ka ci amanata ban taba zaton kana ckin munafukan maza ba sai yau... Saukar mari mai karfi tajia. kuncinta wnda ya gigi ta tafita dagudu tadauko wuka, ,ganin haka yasa ya muedeta zai amse wukar, taja wukar da karfi tazuge mai hannu, jini yafara zuba duk da haka sai da ya karve yace "ba ki da hankali farida, ba ki da hankali. **** Tafiyar su farida da nafisa gdansu fatima akayi jugum ana tunanin wannan bakon bala'i ,fatima kuka take tana fadin "inna ba zan iya da wannan masifaffiyar matar ba na fasa auran usman don Allah ki kirashi a waya yanzu ki gaya masa na fasa auran sa yazo ya amshi komi na sa yazauna da matarsa, kina ji har cewa take sai ta zamo ajalina. Inna tace "ke ba komi irin barazana ce yau kika fara jin inda akai irin wadannan abubuwan, to ki dogara ga Allah matar usman ba kowa bace akan wasu matan don duk abinda kayi wani ya ninka naka kuma anga karshensa, haka duniya tagada, duk wannan abinda tayi ta yi ne don a tsorata ace an fasa idan an fasa din taci galaba daga nan ta samu damar takawa yadda take so, ki kwantar da hankalinki addu'ar da muku da wadda kikeyi insha Allah za tabaki kariya ba abinda zai sameki sai alheri, ba na son ki gayawa kowa ma. ***** Jikin fatima yayi sanyi sosai har dare ba ta da kuzari, lokacin da usman yazo ma haka tafito masa fuskarta ba walwala sai yaji duk abin duniya ya yi masa zafi. Yace "fatima meke faruwa ne akwai damuwa a tare dake don Allah ki gaya min,. Tadago tayi mai wani irin kallo tace "dama haka matr ka take? Gabansa yafadi yace "me yafaru? Ta labarta masa duk tijarar da farida da kawarta sukayi musu, ransa yabaci yace "na ji dadi datazo har gda ta nuna muku mugun halinta, ai da farko na fara gaya mikikikace ba kya son ji, don Allah kiyi hakuri zan dauki mataki a kanta, barazaana ce kawai don ta tsorataki babu abunda ta isa tayi miki ke ba a garin ma za ki zauna ba a ina za taganki ballantana tayi miki wani abu. Ganin fatima ta ki sakin ranta hankalinsa ya dada tashi, sai kawai gani tayi ya durkusa a gurin yana bta hakuri, tace "haaba haba usman ba girmanka bane. Yaki mikewa tsaye yace ba zai tashi ba sai ta ce ta hakura, dasauri tace "na hakura na hakura. KARSHE karfe sha daya aka tabbatar musu da cewa an daura auran usman da fatima, farida tayi kasa tana birgima tare da fadin "ahikenan na shiga uku na gama yawo. Isha ta daga ta tace tashi baki shiga uku ba, fatima abin da za ayi shi ne idan usman yadawo gdan nan kinuna masa kuranki da nadamarki, ckin ruwan sanyi sai mu gasata mu korera da kissa. Gaba daya sukayi na'am da wannn shawara. Karfe goma sha biyun dare usman ya iso gdan, har zai wuce dakinsa sai dai yafasa ya murda kofar dakin farida,. Ga mamakinsa sai yaga ta saki fuskarta ta amsa mai sallama tare da mai sannu daxuwa. Usman ya saki baki galala yana kallonta cike da mamaki da farin cki a zuciyarsa. Da gari ya waye ne take tmbayarsa ina za akai amaryar bataga anyi shirin komi a gdan ba. Yace "ai abuja za mutafi da ita anjima tunda kin ga gdan nan ya yi muku kadan. tace ai ma hakan yayi daidai kaima za kafi jin dadin zaman abujan amma dai zanyi rakiya ko tunda dama ban taba zuwa ba. Yayi dan jim bai so hakan ba amma ya daure yace "shknan sai ki shirya mutafi. **** Karfe go;a sha biyun ranar talata an gama shirya amarya fatima za a tafi abuja, shi kuwa ango da uwargda suka taho a sabuwar motarsa. Babbar hudubar hajiya itace "kin san dai baki taba budar ido kin ganni dakishiya a gdan nan ba, haka yan uwanki idan kim saki baki kin zamo wadda tarako mata