Sashe 17
A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ko ita tana gdansu suna hira, malam musbahu yana matukar jin dadin kawancen fatima da ummi sbda ta samu cigaba mai yawan gaske a cikin rayuwar fatima, hakan yasa yake mutunta ummi tazamo abokiyar shawararsa kan abin da shafi fatima, duk abinda yataso ita yake fadawa. ,kuma ckin ikon Allah sai ta nusar da fatima hanyar data dace nan da nan abubuwa suka dawo daidai kunyar nan ta fati duktazama tarihi har tana iya caba ado tatsaya suyi hira sosai da malam musbahu. ******** Yadda Anisa tashiryawa khalifa abincin safe hka ta tsara mai na dare wanda yafi na safen dadi yana can yana baccinsa ya iske an shirya tebur sai kamshi mai dadi ke tashi tana zaune kan kujera tana kallon wani fim da ake haskawa ya dubeta yana mur. mushi yace "godiya nake ranki yadade. Tace "na fika farin ciki da yabawarka Abbakar dan haka ni yafi dacewa in yi godiya gareka bisa karbar bakunci na dakayi a gdan ka, idan ka kammala zan koma masauki na abokaina na karatu suna jirana yanzu muka gama waya dasu. Ya rausayar da kai har yanzu da murmushi a fuskarsa yace "bakiyi laifi ba idan kin tafi dole in barki ki tafi domin bansan zan sameki ba na hadu dake amma dai va zan ji dadin tafiyarki yau ba me zai hana ki daure ki tayani kwana. Ta lumshe ido tare da ajiyar zuciya takwantar da kanta tana kare mai kallo lokacin daya zauna yabude abincin yana fadin "A bisa ra'ayinki za ki kwana a hidan nan idan gari yawaye sai muje nima inga na ki masaukin, amma idan kinga da takura sai muje yanzu ba na son inyi abinda xan matsawa mutum. Bai jira abinda za tace ba yafara cin abincinsa, idanunta a lumshe taje tunanin abi ? da kwananta a gidan zai haifar, har yau idan sunyi waya da mominta rokon da take mata shi ne tarike mutuncin kanta kada tayarda wani ya yaudareta ya lalata mata kuka yaja mata abinda za tayi kukan da ba ranar karewa., ance idan mace da namiji suka kebenta a wuri daya su biyu na ukun su shaidan ne, soyayyat da takewa khalifa ita kanta har tsoro yake ba tazuciyar ta ta tsananta da ciwon so mai zafi da tsanani shin akwai abinda zai nema a gareta ta hanashi. Bayan ya kammala cin abincin ya wuce dakinsa ya zuba wasu kananan kaya da suka kama jikinsa kam kam sun mai kyau abin har ba a magana, kamshin turarensa ne yafara baibaye Anisa kafin yabayyana gareta, hawaye suka taru a ido? ta Allah ya taimaketa suka koma ba tare da sun zubo ba amma duk da haka idanuwan ta sunyi jawur zuciyarta ta kuntata tunda take rayuwa da ciwon sonsa dake hana zuciyarta sakat bata taba jin abinda taji yau yana mata yawo a zuciyarta ba, hakan ne yasa tamike dasauri tace "bari in dakko jakata muje in wa sisters di na bayani sai mudawo. Yanayin muryarta yakarantar dashi wasu abubuwan game da ita, ko da yake yana sane dacewa tana son shi duk wasu alamu ta nuna masa ya dai ki nuna mata ya fahimci inda tadosa ne sbda tausayin ta yakeji. Ganin bata fito ba yasa yazauna kan kujera kafarsa daya kan daya yana tuna watarana a b. u. k aboki? sa bukhari ke ce masa "khalifa kafito kanunawa yarinyar nan anisa ce ba ka ra'ayin ta don tadaina wahalar dakanta son da take maka ba kadan bane. Ya ja tsaki yace "wai ku mesa ba kwa rabuwa da gutsiri tsoma, ita anisan ce tace ma tana so na? Buhari yace "kai da Allah kar ka raina min wayo ka fi kowa sanin son da take maka idan kuma za ka iya ba ta soyayyarka to kabata fuskar da za ta bayyanar ma da abinda ke ranta. Yayi murmushi yace "Buhari tausayin anisa nakeji sosai a zuciyata, ban shirya batun aure ba ba ni da ra'ayinsa idan nayi soyayya da ita naravu da ita wahala za tasha gara tayi hakuri dani a yanxu akan ta shaku da soyayya ta a gaba ta rasa ni, shiyasa nake nuna mata kamar bansan abin da takeyi ba. Anisa ce takatse mai tunani lokacin data murda kofar dakin tafito rataye da yar madaidaiciyar jakarta tace "inaga ba sai mun fita ba na yi masu waya sun taho nan din yanzu. Yace "ba laifi. Suka zauna shir7 kowa tunanin dayake kara kaina a zuciyarsa, lokaci zuwa lokaci takan kalleshi tashare kwallan dake taruwa a idonta, ta kagu sisters dinta su zo tahuta anya za ta iya kwana a gda daya da khalifa? Namijin data kwallafa rai akansa take masa son da batayi tsammanin anawa wani d'a namiji ba, suka kirata a waya sukace ga su a kofar gdan tamike dasauri taje tashigo dasu. Fadilat da Ramat su ne abokan anisa wanda take ji dasu komi na su tare suke aiwatarwa gida daya suke zaune wanda yake kusa da makarantarsu, amincewar da iyayanta suke nuna mata yake tsoratata yasa take matukar kiyaye rayuwarta, Fadilat da ramat suna rayuwar dasuke so da samari? su yayin da ita ba ta da sakewa da mazan. Ita kanta anisan bata ji dadin irin tarbar da khalifan ya yi wa su Ramat ba, ta dai daure tagabatar dasu a gareshi sannam taya musu cewa za ta taya shi kwana ne, basu jima sosai ba sukace xa sukoma tabiyo su don yi musu rakiya, suna fitowa fadila datake ta fi ramat zafin kai ta hau ta da fada tace "dama haka Abbakar din yake kika gayyato mu gdansa? kina sane da cewa a rayuwata babu ab8nda natsana kamar walakanci, meye dalilin na nuna mana isgilanci haka? Tace "kuyi hakuri nima banji dadin abinda yyi mukun ba haka halinsa yake bai da son magana. Ramat tace "halinsa yake bai da som magana kuma to haka kike tsammanin za ki iya mallakarsa, gskia anisa jikina ya yi sanyi da yanayin khalifa dole ki sassautawa zuciyarki burin da kika ci akansa. Jikin anisa yayi sanyi tace "ina bukatar ku tayani da addu"a xuciyata ba wanda za taso bayan shi, fadila tayi tsaki tace "aikin banza wai dole sai kin rayu da khalifa? Suka tafi suka barta tsaye, ta jima a gun daga bisani takoma ckin gdan, a nan falom data bars&i ta tadda shi yana magana da iyayensa a waya har sai da barci ya dauketa, bayan ya gama da iyayansa yai tunanin ckin yammatansa wa zai kira tadebe masa kewa, yanajin wani iri ne a ransa zaman anisa a gdan ya taimaka masa amma hakanan yake jin tausayinta ba zai iya maidata abokiyar debe masa kewa ba yayin da kudirin datake dashi a kansa ba zai yiwu ba. Yakoma cikin daki yafidda kayan jikinsa yabar gajeran wando kawai yahaye gado sai kuma ummi tafado masa yayi murmushi yakira laila daya daga cikin yammatan na sa, wayarta a kashe, yaja tsaki yakashe wayar ya kama barci. ********* Posting a yan kwanakin nan sai hakuri a dalilin muna ta hidimar biki, duk yadda aka gani a hakura da hakan. A DAREN FARKO 14 GIDAN ainihin iyayan ummi yau hajiya saude tayi ma tsinke ta iske hajiya hauwan tana shirin fita tace "yanzu kuwa nake shirin kiranki a waya inji ko kina gida in biyo ki min rakiya. Saude tace "ai zuwa nyi inji labarin inda aka kwana da batun ummi da khalifa, wai shin har yanzu babu wani labari? Hauwa tace "uhm wani labari ne ban da na takaici saude? wannan yaron zai wahala mu cimma nasara kansa yana da jin kan tsiya. Saude tace "shi din banza, ke fa yadda uwarsa taraba mu da dan uwanmu haka za mu rabata da danta, ba za mu samu wannan damar ba har sai khalifa ya auri ummi. Hauwa tace "to tana can dai tana faman bautar girki a gdan idan yadawo ma san abin yi, yanzu kam sai hakuri tunda ba ya nan. Saude tace '"duk da haka bai dace muyi kasa a guiwa ba da safe ake kama fara idan mukayi sakaci wankin hula yakaimu dare bazamu samu yadda muke so ba. Hauwa tazauna gefen gado tace "to me za muyi yanzu? Tace "gun boka za muyi duk abinda yadace a yi a ja ra'ayin khalifa ga ummi idan ma ta kama muhana shi zaman jamus din gaba daya yadawo ya aureta ba matsala. Zuciyar hajiya hauwa ta karfafa sosai tace, "wannan shawara ce mai kyau tashi mune. A daidai wannan lokacin babbar aminiyar ummi wato jiddah tana wurin ummi ta je yimata sallama don lokacin tafiyarta london karatu ya yi. Suna zaune dakin ummi su biyu fatima tashigo sanye da doguwar rika baka after dress ta yi mata kyau sosai, malam musbahu ne yasayo mata da sukaje kaduna da malam, suka gaisa da jiddah. Ummi tace "kinyi kyau mutuniyar bari in yi miki hoto ,Allah yasa dai angon ya ganki na san zai yaba wannan kwalliyar. Tayi wal da ido tace "shi ne ma ya aiko ni da kwan zabi yace in kawowa hajiya sunje kauye da malam sukayo tsaraba, bari ma inje yana jira na anjima zan dawo insha Allahu. Ummi tace "muje kitchen in ba ki wani lemo dana hada hirar taku za tafi armashi idan kunayi kuna sha.. Fati tace "kai antina kina shagwaba mu dayawa. Tace "haka yadace. Bayan tafiyar fati tadawo daki gun jiddah tace "Allah ya sani ina matukar son yarinyar nan fatima sbda kyaunta da halayenta masu kyau. jiddah tace "ai na ga alama za a iya dawo da ita gidan nan idan tafiya tayi tafiya. Tace "ai da za ta dawo din ai da na ji dadi mama da abba ba su da matsalar komi gdansu gdan jama'a ne suna son suga mutane suna ta zuwa gdan nan. Ta ce "ai hakan yana da kyau shin kuna waya da khalifa? Tarike baki tace "wane ni? Tunda yatafi suke waya da iyayansa bai taba tambayata ba, gaskiyar magana jiddah ina ci gaba da zama a gdan nan ne dan inajin dadin zaman gdan a dalilin kirkin mama da abba amma ba na jin zan samu khalifa ya fi karfina. Jiddah tace "ni abinda yake hada ni dake saurin karaya har yanzu dasauran batu, idan da rai da rabo idan kikayi