Sashe 31
A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shi. Khalifa yaji sanyi a ransa guiwarsa takara karfi yace "baba auran fatima nake son kabani. Gumi yashiga karyowa malam kansa na kasa yayi shiru yakasa magana, itama innar shirun tayi yayin da fatima ke cikin daki a zaune tana jiyosu sai gabanta ke faduwa. Zuwa can malam yadago kansa yace "ikon Allah, khalifa ban taba zaton bukatar da za kazo min da ita ba knan, ko dayake ba abin mamaki bane don ka so fatima Allah ne mai hada zukatan bayi su so juna kuma na ji dadi sosai na gode da son da kakewa fatima, amma ina ba ka hakuri na riga na ba da fatima, a inda ba zan iya karbota in ba ka ba, in banda haka wallahi zan ba ka fatima khalifa kayi hakuri insha Allahu za miyi ta maka addu'ar Allah yabaka matar datafi fatima. khalifa yayi shiru kansa na kasa lokaci lokaci yana sharar gumin da yake tsatsafo masa, gdan ma ya yi tsit kamar ba kowa a gdan, daga bisani yamike dakyar ko ina a jikinsa ya yi mai nauyi yace "to na gode baba Allah yasanya alheri. Malam yamike yabiyo khalifa kofar gda suka tsaya, malam yace "Abbakar ina matukar bakin cikin hanaka auran fatima amma kayi hakuri Allah ne bai sa matar ka bace, akwai abubuwa da dama da Allah kan jarrabi bawansa don yagwada imaninsa, idan yajure yayi hakuri sai Allah yamusanya mai da abinda yafi wannan alheri sakamakon hakurin da yayi da abinda Allah yajarrabe shi dashi. Duk kokarin da dr. khalifa yayi na mayar da hawayen da suka taru a idonsa don kada malam ya gani abin yaci tura, domin sai da yadinga sharar kwalla yana jan numfashi da kyar, daga karshe kasa ci gaba da tsayuwa yayi sai durkusawa yayi, hankalin malam yatashi sosai tun yana iya magana har yayi shiru ya zurawa khalifa ido, yaji tausayinsa a wannan lokaci ,tausayi mai tsanani, zuwa can khalifa yatashi yatafi gida ba tareda yakara cewa da malam komi ba. Malam ya jima yna kallonsa sannan yashige ckin gida ya iske inna itama na ta jikin a sanyaye, yazauna yace "kai yaron nan dagaske yana son fatima. "Itama tana sonsa malam ". Inna tafadi tana kallonsa. Yace "wane irin tana sonsa kuma da maganar musbahun a kanta take son wani. Tace "wallahi kuwa fatima ta yi abinda ban taba zato ba a yanayin rayuwarta, tadubi idona tace a yanzu ita khalifa take so tana son mu fasa ba musbahu auranta mu bata shi in bar da tana son sa za tayi haka? tunda tagaya min wannan maganar jikina ke rawa hankali na yatashi sosai, ni dai yin wannan rana na yi shi ne kawai amma zuciyata tana cike da sarkakiya da damuwa, sbda fatima ta ban mamaki ta ba ni tsoro, duk abinda fatima za ta budi baki tayi magana akansa ba karami bane, tana da kunya sosai da zurfin ciki, tunda harta iya magana to da gaske tana son khalifa, yawan kukan datakeyi shi yake dada dagan hankali har na rasa yadda zan bullowa lamarin. Malam yace "amma wannan zancen banza ne, ni za ta mayar karamin mutum, sa rai da ci shi ke kawo jin yunwa in barda ta sa soyayyar ta sa ai ba za ta daga hankalinta akan shi ba, tun yaushe aka sa wa musbahu rai da batun auran ta, ya saki jiki itace matarsa kawai sai ta dawo tace ga wanda take so, a gun nan nafada mata idan ba ta son musbahu ba zan mata dole ba tace ta ami? ce, yanzu ya kike zaton mutane za su daukeni idan nafasa ba musbahu naba khalifa, kwadayi? Babu ta inda zan fidda kaina a gun musbahu da yan'uwansa dasauran jama'an gari na sayowa kaina zagi. Inna tace "wallahi malam ni ma ban goya mata baya ba don na san son zuciya ne karara tazo dashi. Haushi yakara kama malam ya kwalawa fatima kira, tafito tana rabe rabe ta tsuguna ybuga mata harara yace "na fahimci cewa ke ce kika ba khalifa fuskar yazo gdan nan yazo min da batun auranki alhalin kina sane da musbahu, kin ba ni mamaki fatima ban taba shakku akan lamarinki ba sbda biyayyar ki garemu kada ki bamu kunya kada kija abinda zai ja mana damuwa alhali muna zamanmu lafiya. Fatima tayi doguwar ajiyar zuciya tace "kuyi hakuri baba ni ma banyi tsammanin zan wayi gari ckin wannanyanayi ba, ni kam ina son khalifa don Allah ku ba musbahu hakuri.... "Salamu Alaikum Muryar musbahu knan, suka daga kai a razane suka zuba mai ido fuskarsa a cunku she yazauna jagwab kusa da malam muryarsa na rawa yace "Baba hakika na ji duk tattaunawar ku da fatima kuma na ji matsayina a gunku, ba ni da abi? da zan ce muku sai godiya, kyautatawar dakuka mini Allah ne zai biyaku domin don shi kukayi. Baba na san ina son fatima soyayyar da tasa nake jin cewa idan na rasata zai wahala in yi aure domin bansan ta yadda za ai in so wata mace ba bayan ita, ko da yike komi na Allah ne amma wannan soyayyar danake mata ba za tasa in aureta alhali na san ba ta so na ba, kayi hakuri baba kaba fatima khalifa... Cikin zafin rai malam musa yace "yi min shiru musbahu, wannan yarinyar bata isa tasauya min ra'ayi ba, tunda tun farko da amincewarta aka sa bikin auran nan kadarra cewa ma ka auri fatima ka gama. Ranar da aka sanya za a daura wannan auran ba fashi, insha Allahu za a daura in dai ka ga ba a daura ba sai dai in ranar ce tariskeni ba na numfashi, za a daura auranku kuma za a kaita gdanka, a ranar tahadiya zuciya tamutu a kawo min gawarta. Musbahu yabude baki zaiyi magana malam yayi mai tsawa yace "in dai kaima ba so kake kabata min rai ba kayi min shiru, idan Allah yakaimu gobe kaje ka amso katunan daurin auran a kaiwa kowa. Yatashi yafice ,musbahu ma yabi bayansa, itama innar tashige daki tabar fatima tana kuka. Tunda take bata taba batawa iyayanta rai ba ballantana suyi fushi da ita sai yau, shin me ya shiga zuciyarta ne tasauya haka, a duk lokacin da ake magana, soyayyar khalifa ce take karuwa a zuciyarta, kamar ana hura mata wuta, idanuwanta suka kada jawur tarasa yadda za tayi da ranta. Soyayyar dr. khalifa ta gama rufe mata zuciya ji take kamar ba xa ta iya rayuwa ba in ba shi, gabaki daya ta watsar da batun ummi ta kanta kawai take, tana ji a ranta in dai ta auri khalifa duk abinda zai biyo baya me suki ne, iyaka dai ummi tadaina kulata ita in dai tana tare da khalifa bukatar zuciyarta ta biya, matsalarta yanzu iyayanta wadanda sun dau zafi dayawa. Ta daga kai ta amsa sallamar musbahu, haushi yakara kamata tabishi da ido har yatsuguna gabanta yace "fatima. Bata amsa ba sai kallo yace "kiyi hakuri. Ta mike tashige ckin daki a zuciyarta tana fadin ai kai hakuri yakama ba ni ba. Musbahu yayi zaman dirshan a gun yazuba tagumi da hannu bibbiyu shin wani irin iftila'i ne yasa me shi haka?da can bai rasa fatima ba sai da yagama sakin jiki bai da mata sai ita, yakasa juriya yabita dakin na su, ya isketa a kwance tana kuka. Yace "fatima baki min adalci ba don Allah ki kwatanta idan ni nayi miki haka za ki so? a ce a irin wannan lokaci in ce na fasa auranki wata zan aura? Ya tsuguna a gabanta kamar mai neman gafara yace "don Allah fatima ki taimake ni wlh ba karamin so nake miki ba, ni ban isa in ce kwadayin duniya ne yasa kike son khalifa ba idan akwai kwadayi ba za ki tsaya akaina ba, masu kudi dayawa sunce suna sonki baki ba su hadin kai ba. Fatima batayi niyyar yi ma musbahu magana ba dan ita kanta ta san ba ta da abinda za tace musa, amma a bisa wannan maganar tasa da taji ya dace tace wani abu a kokarinta na samin mafita. Tace "Nagodewa Allah dayasa da kanka kayi min shaidar ba kwadayi yasa nace ina son khalifa ba, ka san cewa soyayya ce don Allah, ina son kayi hakuri kayi min adalici, soyayya Allah ne me sanyata a zuciya ba mutum ba. Ya katseta zuciyarsa cike da daci yace "fatima ki fito a gaban ido na kawai ki ce ba kya so na, khalifa kikeso, na gode fatima nagode. Yamike dasauri yafice yana goge hawaye. Fati tace "innalillahi wa inna ilaihir raji'un. A DAREN FARKO 27 izuwa wannan lokaci ummi ta tabbatar fatima ta daina yi mata aikin komai ita takewa kanta, ta fahimci soyayya suke shimfidawa da dr. khalifa ta gaske duk da cewa rigima ake tafkawa a gdansu, ga katunan daurin auren yau an fito dasu har an kawo na Abba gdan, a kalla kwana uku kachal a daura auran musbahu da fatima, har takaici da kishi ya yiwa ummi yawa, yaudara ita take fassara fatima ta yi mata tunda gashi ta fita hanyarta tunda gashi ta fita hanyarta gaba daya ko neman ta ba ta yi lallai mutum abin tsoro ne. Ta iso gdansu da katin daurin auran ta nunawa hajiyarta tace "to ai zance ma ya kare in dai aka mata aure aka kaita dakin mijinta ai dole khalifa ya hakura da ita duk maitarsa . Unmi tace "kayya dai hajiya khalifa yana son fatima in kinga abin da yake nunawa za kiyi mamaki. Tace "duk ihu yakeyi bayan hari shi zai bawa kansa auran na ta? ki kwantar da hankalinki malam yana nan yana buga mana aiki da kafarsa khalifa zai zo gdan nan. Ita dai ummi hnkalin ta ya ki kwanciya son da khalifa ke nunawa dmfatima kadai ya isheta takaici, ita ko kallon ta ba ya yi tamkar ba aiki ake yi a kansa ba. ***** Ummi ce take sha'aninta khalifa bai san an fara rabon katin auran fatima ba sai da yamma daya dawo daga asibitin su dr. hafiz ya iske katin a hannun abbansa, yana gama karantawa yazube a gun. Abba yatashi a firgice yana jijjiga shi tare da kiran sunan sa da karfi ina khalifa ko motsi