← Book details A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 50

Sashe 37

A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ce an bashi to sai ya ki karba don kada mutane su ce ya yi son kai? A bisa dole mama tahakura don bata samu goyon baya ba ta kowanne fannin, dayake harka ce ta masu kudi duk da kasancewar baa gayawa yan uwa ba tun auran da wuri ba amma daga lokacin da aka fara bada sanarwar daurin auran gdan yafara cika da mutane maza da mata yan taya murna. Ummi tana gdansu tun lokacin da dr. khalifa yafito daga asibiti ta tabbatar za a yi auransa da fatima ta karasa rikicewa hankalinta a tashe tajewa hjiyarta da labarin, ta bayyana mata duk yadda abubuwan suka faru tace "Hajiya mama da abba babu abunda suke sosai farin cikin dansu, Abba da kansa yaje ya sanar da mahaifin fatima halin da dansa ke ciki a kan yarsu, suka taho asibitin da niyyar dubashi lamarin dayasa musbhu yace ya barwa khalifa fatima sun manta ina son khalifa tun kafin yaso fatima, bbu wnda yadamu da hlin danake ciki ana nan an fara shirye shiryen auran gadan gadan. Hajiya tashare mata hawaye tace "Daina kuka ummi in dai ina raye a gdan duniya nan zanyi miki maganin damuwarki, ba zan taba cewa kidaina son khalifa ba don ita zuciya ba a rabata da abinda take so a zauna lfya, idan har muka hakura da khalifa to mata muka rako duniya, wannan dogon lokacin damuka dauka muna nemansa ba zai tashi a banza ba, tashi mu koma gun malam. Ummi tadanyi jim sannan tace "hajiya bai dace mucigaba da wahalar da kammu a gun zuwa gdan mlami ba da wahala idan hakan zai amfanar damu tun da a baya bai mana amfanin kmi ba. Hajiya tafiddo ido tace "ke saurara nsara a hankli samunta idan lokacin samuwarta ya zo za kiyi mamakin aikin malam, ke de muje muji ta bakinsa, motsi ai yafi labewa, bari in karasa miyar can yunwa nake ji. Ummi tace "ni don haushi ma ko yunwa ba ta damuna. ina mamakin son kan da ake nunawa kowa akan khalifa amma ta watsar da komi ta kanta kawai take ko kunyar idona ba ta ji. Hajiya tace "duk ki kyalesu son zuciya bacinta da sannu dukka za sugane kurensu. Ummi ta tashi tashige dakin hajiya ta tsaya a gaban madubi tana karewa kanta kallo tare da tuno siffofin fatima a idanuwanta tajinjina kai tare da ajiyar zuciya tace "ba komi. Sai bayan sallar isha'i suka isa gdan malam shima yana mamakin ganinsu a wannan lokacin ya san ba lfya. suka baje masa bayanin komi. Unmi ta marairaice tace "Don Allah malam kataimakeni xan rayu ckin bakin ciki mai tsanani idan narasa dr. khalifa dole in yi kishin fatima domin ta san sirrina ta san abinda ke ckin zuciyata, ko zan hakura dr. khalifa yarayu da wata diya mace ba dai fatima ba, na amince in rasa shi amma kada wata ta mallake shi. Malam yabushe da dariya yaja ra'ayinsu ya fara zane zane yana bajewa lokaci mai tsawo suna kallonsa sannan yadago kai ya dubesu yace "haba ko da naji ai uwar Khalifa ce tashiga malamai aka tsare mata jikin khalifa don kada wata macen tasamu damar asirce shi ta rabata da shi, tunda tasan yammata za su so shi da yawa ita kanta fatiman don soyayyar da yake mata ta ra'ayin kansa ce shi yasa duk ayyukan da muke jifansa dasu ba su tasiri akansa, to amma ba komi akwai aljanin da zamu hada shi da shi sai yayi tasiri a kansu shi da fatiman kuna zaune za kuga ya tsaneta hankalinsa ya dawo kan ummin, amma sai an sayi sa babba wanda za a yanka shi a yi aikin a kan sa aiki irin wannan karfi gareshi sai an yi yanka. Ganin sun yi jim yasa yaci gaba dayi musu dadin baki tare da kwadaitar dasu amfanin aikin idan an yi, yace "wa kukaga ya ji dadi ba tare da ya sha wahala ba, duk wadannan abubuwan tarihi za su zama idan Khalifa yazo hannu sai ya baku tausayi ku dai ku daure. Suka dawo gida suna tattauna yadda za su nemo kudin sa, sun yi ammana aikin malam zaici, ummi tace "Hajiya dole ne in saki jiki wurin gudanar da al'amarin bikin nan xan nuna kamar bbu wani avu a zuciyata xa ayi komi dani, amfanin hakan shi ne dan in samu kudin da za muyi amfani dasu. Hajiya tace "Lallai kin zo da dabara, idan har kika nunawa khalifa cewa kina son auran sa da fatima komi za musamu a jikinsa da abbansa, kin ga knan mun jefi tsuntsu biyu da dutse daya. A DAREN FARKO 31 Ana ya gove daurin auren fatima da khalifa wasikar musbahu ta iske mallam inda yake shaida masa cewa kada su daga hankalinsu a dalilin rashin ganinsa ya kauracewa gdan ne don ya samar da zaman lfya da walwala yayin bikin fatima, a cikin wasikar yace. "Malam idan naci gaba da zama kana ganin damuwata za ku dinga jin zafin fatima yayin da ni kuma zuciyata ba za ta taba yi min dadi ba in dai yakasance kuna jin ahushin fatima a sbda ni da ace da ace zan iya shanye damuwata da zan dawo amma hakan hakan ba zai yiwu gareni ba, zuciyata ba ta da wannan karfin. Baba da inna ina rokon ku yi hakuri don Allah ku dauki wannan al'amarin a matsayin kaddara kada kuyi fushi da fatima, fushinku matsala ce babba ga rayuwarta ina nan ina ta mata fatan alheri, insha Allahu da zarar an gama bikin an kaita gdanta zan dawo. Sun ji tausayin al'amarin kwarai da gaske sai dai ba yadda za suyi al'amarin kaddarar nan dai da kowa ke fada itace dole ayi hakuri a karbeta, surutun da ake gudu shi ake tayi a cikin unguwa da dangi, kwadayi kwadayin abin duniya shi ake tafada musamman lokacin da sanarwar daurin auran ta cika gari ta hanyar kafafan yada labarai dake arewacin kasar nan ba ma nan kano kadai ba tare da sanarwar za ayi gagarumar wlima bayan daurin auren da yamma amma na maza zalla,tuni aka cikawa malam gdansa da nau'ikan kayan abinci na alfarma wanda za ayi amfani dasu a gun bikin, hatta nama kala kala aka kawo, kayan da amarya za tasa lokacin biki mama da anty sadiya suka tsara mata su gun kwararrun telolinsu dake tsara musu dinki, kaya ne msu tsadar gaske haka dinkunan sun sha kudi amma fa sunyi kyau sun dace da amaryar, kayan lefene suka ce sai an gama hidimar daurin aure ango da amaryar za su tafi da kanta za ta xabi irin kayan da take so da kanta. Anty sadiya ta hurawa mama wuta akan lallai su za su gyara amarya tun daga kan fatarta da abubuwan da ake sha masu kawo ni'ima ga amarya, mama tarike baki tace "sadiya wannan ai na su ne na iyayanta da yan uwanta ina dangin miji ina gyaran amarya. Sadiya tace "Tabdijam ai kuwa mama anan ne ma yadace ki yi gyaran da hujja, me yasa kikayi mata a baya lokacin da za ta auri musbahu, kika gyara don dan wani ma ballantana na mu, ai ajiye kunya za muyi mi tattalin farin cikin danmu zamanin duhun kai ya wuce ina innarta za ta iya irin wannan abub tana fama da kunya. Mama tayi dogon tunani taga gaskiyar fa sadiya barin kashi a ciki bai maganin yunwa, musamman yadda taga khalifa yana cike da tsananin farin cikin auran daya samu ko kawaici bai iya yi. Lokacin da ummi ta iso gdan da safe tashaida mata cewr tana son tadan yi dabarar da dan ja hankalin fatima tadawo gdan nan tazauna a yau, duk abinda aka fada akan fati sai ummi ta ji tsigar jikinta ya tashi, sai dai bata bari a fahimci damuwarta ta saki ranta sosai, a wannan lokacin ma fadada fara'arta tayi tace "Ba damuwa mama ai ke ce uwar amarya uwar ango mu kuma mune kirjin biki. Bayan sun gama cin abinci tanifi gdansu fatiman ta iske su ita da ango dr. khalifa a soron gdan suna hira, tarike baki tana murmushi tace "to ai dai aski ya zo gaban goshi yaya khalifa meye na mannewa anan? Ni na dauka ma ka fita. Ya bata rai yana harararta yace "ke wai ni abokin wasanki ne xan dauki mataki akanki idan baki shiga taitayinki ba. Tace "a'a yi hakuri kamaida wukar ni dai katayamu murna Allah yasa rakiya tayi nisa. Suka bushe da dariya gaba daya ita da fatiman tawuce cikin gida tana fadin "Bari mugaisa da inna kafin kugama. Khalifa ya matso kusa da fatima yana dan rausayar da kai fuskarsa dauke da murmushi yace "Wallahi fatima har na rasa wacce hanya zan nuna miki soyayya duk abin da nayi miki don in tabbatar maki da soyayya sai in ga ya yi kadan matsayinki ya wuce nan. Ta kwantar da kanta a jikin bango tana kallonsa, shadda ce a jikinsa ruwan kwai, iya guiwa rigar ta tsaya masa ta dan matse me jiki, fuskar nan fes fes tamkar kullum kyau ake kara masa, bbu wani da namiji da fatima take tsayawa tamasa kallon kurilla sai jan gwarzanta Abbubakar saddik, sbda ahi take kallo taji sanyi a ranta, duk damuwar datake ciki in dai za taga khalifa sai taji sanyi a ranta kuma sai taji lallai ta gamsu ta ga da namiji cikakke wanda in dai ka kalleshi ka san ka ga da namiji. Khalifa yaci gaba da fadin "Fatima Allah ne yayi ke rabona ce shi yasa nadawo gida a dai dai wanna lkacin, godiya nakewa Allah daya ba ni ke, domin da na rasaki ban san halin dazan samu kaina ba fatima. Wani irin kallo take masa tana dan lumshe ido tana budewa tare da marairaice fuskarta domin za tayi kuka, lamarin daya dagawa dr. khalifa hankali sosai yakasa rike kansa yakara matsowa daf da jikinta yakai bakinsa kunanta yace "Don Allah fatima zo mu shiga dakin nan in dan ji dumin jikinki zuciyata za ta fashe yanzu. Tayi wal da ido ta waiwaya gaba da baya ba kowa. Ko me yasa bata iya musu da dr. Khalifa tana sane dacewa bukatarsa gareta bata dace ba amma ba za ta iya kaucewa abin
Chapter 37 · 0% Book details