← Book details A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 50

Sashe 21

A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yin kyau da kwalliya dukda cewa idan ma bakiyi kwalliyar ba kyau kike yi ke kam Allah ya yi miki baiwa da yawa fatima. Tace "don Allah kiyi sauri mutafi kadda yamma tayi ba kya gajiya da surutu. A cikin mota suna tafiya ummi tana tuki fatima tana gefenta suna hira, tace "duk inda muka wuce fa sai an kalleki fatima ina kallon wani dazun da danja ta tsayar damu sajra kadan yabuga wa wani sbda kallonki, kidinga sa nikab kidaina daukar hankalin mutane. Ta dubeta tace "su sukaga za su iya ni bance wani yakalleni ba duk wanda wani abu yasame shi a dalilin kallona to shi yadauki alhakin kansa, muyi wata hirar. Tace "yawwa ai kuwa yau zan miki gagurumin albishir. Fatima tace "Allah sarki ai kuwa ni bani da wani labari da nake son ji mai faranta rai daya wuce in ga khalifa ya dawo ya amince da batun auranki da shi, wlh a wannan rana bansan farin ckin dazanyi ba, bansan yadda zan fassara wannan rana ba, gskiya anty ummi ina kaunar khalifa ne sbda son da kike mishi., duk da cewa na tsane shi tawani fannin sbda ba ya da tausayi. Ummi tayi dariya tace"ummi misali idan ke ce wani namijin yazo yana miki irin son danake wa khalifa za ki tausaya mai kiyarda da auran ko da ba kya sonsa ? Fatima tace "ummi ni mutum ce da ba na son ganin musulmi dan uwana a cikin damuwa in dai har na san yana zubda hawaye akan ciwon so na irin yadda kike zubda hawaye akan son khalifa zan tausaya mishi. Ummi ta girgiza kai "to albishirinki soyayya ba haka take ba. Tayi saurin katseta da fadin "ko ma yaya take ummi, khalifa ba shi da kirki, ba shi da tausayi, ya kamata mutum yaso mai sonsa, ya kamata mutum yakasance mai tausayi, nikam ba zan taba yiwa khalifa uzuri ba, duk da haka don Allah ina rokon idan khalifa yadawo kasar nan...... " Ummi tayi fakin a kofar gdansu tace "ki kwantar da hankalinki idan Allah ya kaimu gobe khalifa zai dawo kasar nan. Tadafe kirji tare da fiddo ido tace "don Allah dagaske kike ? Tace "kada kiyi shakkar hakan kizuba ido gobe za kiga dr. khalifa. Ita kantaa ummi bataji dadin samun hajiya saude a gdan ba sbda a fili suke nuna ba sa son fatima, yayin da ita kuwa ta tsani mutum ya nuna mata ba ya son fatima, tana matukar kaunar fatima a ranta. Fatima tatsuguna har kasa tagayar dasu su ka amsa kowacce fuska ba fara'a suka ja baki suka tsuke, wayar fatima tafara ringing tamike tayi sauri tafita ganin sunan malam musbahu, nan da nan hajiya saude tazubawa ummi harara tace "wai me kike nufi da yawo da wannan kodaddiyar yarinyar, duk inda za ki sai da ita za ki, sai da ita za kizo gdan nan ma kin dauko ta kina nufin duk abinda xa mu tattauna akai sai dai muyi a gabanta knan ba mu da wani sirri sai ta ji ? Hajiya hauwa tayi tsaki tace "ba ma wannan ne abin haushin ba saude sai yadda ummi take bata rai idan munce muna son magana da ita wai lallai sai duk abinda za a fada a fada a gaban fatima. Bayan ita fatimar idan sun tashi na su sirrin da ta ta uwar tafiya take gdansu suyi maganarsu ba a gaban ummin ba. Hajiya saude tace "ai ummi ba ta da wayo na rasa wacce irin soyayya takewa fatima kamar wadda ta asirceta, ga ta dai a haka kamar wata mai wayo nan kuwa ba komi a ranta sai wauta, mu da mukeso mu mallaki khalifa ta jawo wannan mai kama da aljanu ta jawota gdan kullum a gdan take yini idan yadawo ba kya jin ba zai ce fatima yake so ba ? Ummi tace "hajiya ya ya za ayi khalifa yace yana son fatima bayan an kusa bikinta, kwanaki kadan suka rage akaita gdan mijinta. Hajiya tace "wohoho ummi sai yaushe za ki fahimci halayyar mutane ne kidinga taka tsan tsan dasu, ki guji sharrin wanda kika taimaka wa, lokacin daka tausaya wa mutum kadakko shi daga rana kayi masa gata kadawo dashi inuwa bbu wanda zai tura cikin rana sai kai. Kin ga dai ke ce kika wayar da fatima da iya kwalliya da komi hatta magana ke kika koya mata amma babu wanda fatima za ta fara yiwa illah sai ke, tabbas idan bakiyi taka tsan tsan ba sai kin ce na gaya miki. A DAREN FARKO 18 Ummi takwana tana jujjuya maganganun su mahaifiyarta tana musanta duk abunda suka fada, ita kam ta yarda da fatima dari bisa dari bazata cutar da ita ba ta tattara duk maganganun na su ta watsar, ta fuskanci ranar dazata fuskanto ta wato ranar dawowar mutumin da ba tasan abinda sakamakon dawowar ta sa za tahaifar mata ba, farin ciki ko bakin ciki dole a daya biyu ne don haka a wannan daren bacci ta ragagge ne duk sanda tafarka sai ta ji gabanta ya fadi. Da sassafe takira fatima a waya tace don Allah tazo, tace lafiya, tace "banjin dadin jikina ne da zuciyata inason ki zo miyi hira. Fatima tace "don Allah ki kwantar da hankalinki khalifa fa ba wani bane illa mutum kamar kowa, meye na(aga hankalin ki akansa ? Tare da fatin suka shiga kitchen lokacin dataxo gdan wuraren karfe tara na safiya, ko da yaushe mama na yabawa yadda suke tsara girki da tebur a halin yanzu fatima dai da iyayanta sun zamo yan gda sosai a gdansu mama, suna yawan yi musu alheri na kayan abinci da sutura, wani lokacin mama dakanta take zuwa gun innar su fatima suyi hira sosai tanajin dadin shawarwarin datake ba ta akan rayuwa, sun shaku dayawa haka malam da abban khalifa sun zamo aminan juna ,idan kashiga gdan za kace fatima 'yar gdan ce sbda sakewar da takeyi, ci mai kyau da sha mai kyau ga kayan ado hakan yasa fatima tayi kyau ba na wasa ba kamar a taba jikinta jini yafito ta zamo kamar irin taurarin matan nan da suke zamowa ababan kallo a duk inda suka shiga, mafi yawan mazan dasuke shige da fice a gdansu mama idan sunga fatima sukan nace suna sonta, ba ta sauraron kowa duk kudin mutum da kasaitarsa, fatima ba ta bari yashiga ranta sbda alkawarin datayiwa babanta na auran malam musbahu yana tsaye a zuciyarta, bata taba wasa da maganar iyayanta ba koyaushe farin ciki ? su shi ne ranta. Gargadin karshe dasu hajia hauwa suka yiwa ummi shi ne "ta sallami fatima daga gdansu mama kafin khalifa yadawo kasar nan in ba haka ba tai kuka dakanta, ta jiye ma kanta abinda zaisa ta tayi kuka ba iyaka, bbu maganar data kama ummi aciki face ma dariya dasuka bata, magana daya tayi musu inda tace "su kwantar da hankalinsu da ace fatima za tayi soyayya da wani da tuni ta yi kafin ma khalifa yadawo sbda mazaje dayawa masu matsayi da takama da dukkan abinda da namiji yake takama dashi sunce suna sonta bata taba sauraron wani ba, ta rike maganar iyayanta dagaske ,tunda dai fatima bata yi soyayya da wani da namiji ba ba za tayi da khalifa ba. Hajiya saude tace "haka kike gani, ke mesa kikace ba kya son kowa sai khalifa ? Tace "wannan kuma daban soyayya gamon jini ce bai zamo dole don ina son wani yakasance wance itama shi tame so, masu iya magana ma kance abincin wani gubar wani. Gaba daya ummi ta san basu gamsu da hujjojinta ba, hankalinsu a tashe yake a bayan azahar in yau sai da hajiya takirata tana tmbayarta "in ce ko fatima ba ta gdan nan, na ji ance khalifa ya iso gda nigeria yana Lagos yana shirin isowa kano. Ummi tace "hajiya itace take tayani hada mai abinci, kin san yana son abinci mai dadi. Taja tsaki takashe wayar har tarasa yada za tayi da ummi. Karfe hudu na yamma dun abubuwan ci da na sha da sukaiwa khalifa sun hada a tebur, gida ya dau kamshi an gayare mai dakinsa fes yanata kamshi, bayan fati Ta idar da sallar la'asar tazura dogon hijjabin ta da nufin tafiya gda. Ummi ta fito daga wanka tace "zan tafi idan bakon ya isa ki ce muna masa sannu da zuwa. Ummi tace "ai kuwa baki isa ba dole ki tsaya kiga khalifa ya dace kigan shi. Tace "To ai na sanshi a hoto duk wanda ke shigowa gdan nan ko bai taba ganinsa a fili ba ya san shi a hoto ko ina a gdan nan fa hotonsa ne. Tace "ai na san da hakan nace kitsaya kigan shi duk yadda yake a hoto ya fi nan. Fatima tayi dariya tace "na san zaifi haka ummi idan za ki lura ai ban taba cewa kinyi laifi don kin wa dr. khalifa son da kike masa ba, ya cancanci a so shi dan ya hadu kowa yana son abu mai kyau, ba laifi bane don mace ta so mijinta yakasance mai kyau irin dr. khalifa sai dai bbu ,gskiya yi hakuri ba zan boye miki ba ba na farin ciki da gani ? khalifa, ina tayaki murnar dawowarsa ne kawai don shi ne farin ckin rayuwar ki ina son abinda zai faranta ranki ummi fiye da farin cikina, da ace dr. khalifa ya amince ya karbi soyayyarki da zan kasance cikin dumbin farin ciki mai yawan gaske amma duk da haka.... Ta katseta "fatima in dai dagaske kina son farin cikina tsaya dr. khalifa yazo don Allah. Fati bata sake magana ba tafidda hijjabinta tahaye gado takwanta, doguwar rigar shadda ce a jikinta ruwan powder, daga sama ta matseta yayin da tayi fadi daga kasa, babu kwalliya fuskarta gashin kanta ne dai ya sha gyara yakwanta a kafadarta ,a cikinsu babu wanda tasan khalifa ya shigo gdan. Ummi tace "don Allah fatima dako min ragowar furar dana rage a fridge. Fatima tafito a yadda take ko dankwali babu tashiga kitchen din falo tadakko furar kwatsam suka hada ido da dr. khalifa daya fito daga dakin mamansa, abbansa na biye dashi da manyan abokansa biyu dr. hafizu da dr. bashir, gaba
Chapter 21 · 0% Book details