← Book details A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 50

Sashe 23

A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

haihu tun karfe bakwai tabar gdan nan ko abinci ba a tanadar min ba kuma yunwa nakeji sosai, yanzu sbda Allah a irin wannan tsarin idan munce, za muyi aure munyi laifi ? ko yanzu da zance zanyi aure sai ka ji bala'i na tashi nakan rasa su mata wane iri ne. Dr. khalifa yabushe da dariya yace "na san duk yunwa ce tasaka wannan surutun ai kai da sauki ma tunda ka iya shiga kitchen ka sarrafa abincinka kaci ni ko tea ba na iya dafawa. Dr.hafiz yace "to ai kuwa ka koya mata ba su da tabbas surutu da soyayya a waje suka iya idan an shigo gdan sai a hankali musamman idan an fara ajiye yara, bara in dafa indomie kaina har ciwo yake sbda yunwa. Bayan ya gama dafa indomie din suka mike a kasa suna ci yace "mutumina wai wace babbar magana ce ? Yace "ina fatan ka gane fatima" Dr. hafiz yace "ba zan kasa fahimtarta da wai ba domin na fahimci zuciyarka ta amsheta da gaggawa. Yace "kwarai ba ka yi fahimtar kuskure ba, kallo daya nayiwa yarinyar naji zuciyata ta aminta tazamo mata ta. Dr. hafiz yace "to ai bbu matsala yarinyar datake rayuwa a cikin gdan ku na yi farin cikin han. Dr. khalifa yace "kai dakata saura sati biyu bikinta. Dr. hafiz yace "to ba sai a lalubo wata ba abinda ga matan nan dayawa dakansu suke cewa ma suna so. Dr. khalifa yace "kai likita mata suna suka tara, duk yawan dasukayi irin su fatima daban suke, a iya budewai idona da yawace yawace na ban taba ganin mace mai kyaun fati ; a ba, tare da kyaun fuska ,dubi yadda tsarin halittar jikinta yake,habawa wannan ai itace mace mutumi na. Dr. hafiz yayi dariya sosai yace "kai wani irin kayatarwa fatima tayi maka, ne karude haka ? Haba likita kada kabari fatima taji za ta rainaka ka ga yarinya ce karama ko ka mance kana cewa ba ka son karanar yarinya ? Dr. khalifa yace "kai tafi chan wannan lokacin ya wuce ba zan iya hakura da yarinyar nan ba. Dr. hafiz yabata rai yace "kai Abbakar muyi magana ta gaskiya yarinyar daya rage saura sati biyu bikinta yya za ayi kace kana sonta ? ko a shari'ance ba kyau nema cikin nema ,kayi hakuri kawai mace in dai mace kake bukata za kasamu wadda tafi fatima kyau sai dai in fa fatima kake nema. Dr khalifa yadan marairaice yace "haba dr. hafizu yaya za ayi ka sanyayar min da jiki ? bayan ka san ban taba nuna maka wata diya mace dana damu da ita ba ballantana har in nuna damuwata akan sonauranta, tunda nagaya maka ai ka san dagaske nake ya kamata kataimake ni da shawarar dazan samu mafita ba kasace min guiwa ba. Dr. hafiz yace "to ai ni banga hanyar mafitar bane Abbakar, sati biyu fa yarage biki sai kuma muce muna so ? wannan ai son kai ne da zuciya, kuma kasani son kai da zuciya ba dabi'a ce ta mutan arxiki ba. Dr. khalifa yace "knan so kake kace min sai dai inyi hakuri da fatima ? Yace "Don Allah kayi wannan hakurin sai Allah yabaka wacce tafita.... Dr. khalifa yace "kai hafiz daina min wannan maganar da wuya in za tayiwu bakasan menake ji bane game da wannan yarinyar, ban taba sanin haka so yake ba. ****** Tun a wannan rana mama tafara shirya amarya fatima da kayan gyaran jiki na mata suka tunkari lamarin dagaske, batasan rikicin da dr. khalifa ke ciki game da matsananciyar soyayyar fatima da ta damki zuciyarsa ba, a wannan daren yakasa sukuni yakwana yana tunanin tawace hanya zai samarwa kansa mafita. Abin da dai yasawa kansa shi ne ko ta wani hanya zai mallaki fatima babu yadda za ayi yayi sakacin dazai rasa ta, bai san haka ciwon so yake ba sai yau. A gdan fatima takwana suna tattauna yadda biki zai kasance, abinda fati take jaddadawa ummi shi ne "ta sani khalifa sbda ba ya da tausayi, tace "ni kam ummi na rasa yadda zanyi da takaicin dana ke ji a raina game da yaya khalifa, ko ganinsa ba na son yi sbda kawai ya nuna ba ya sonki. Ummi tayi murmushi tace 'to yaya zanyi na zubawa sarautar Allah ido na zubawa dr. khalifa ido, na tabbaatarwa raina ko ban samu dr. khalifa ba to zan tabbatar wata diya mace bata same shi ba, idan narasa shi sai dai kowa ma yarasa . Fatima tace "kina nufin za ki hanashi aurene ? yaya mutumin da ka kaasa jawo ra'ayinsa yasoka za kasawa ranka cewa za ka iya hana shi aure ? Ummi ta girgiza kai "ba aure xan hana shi ba ban isa in hanashi aure ba ni dai na ce sai dai kowa yarasa . Riga da zani na atamfar egyptian ce a jikin fatima tana tsaye ita kadai a kitchen tana suyar kosai, kawai ganin mutum tayi a kusa da ita yana fadin "fatima aiki ake yi ne ? A firgice tawaiwayo tadubi dr. khalifa yana sanye da doguwar riga fara kal kamshi mai dadin gaske yana tashi a jikinsa, ta matsa gefe ganin yadda yatsaya daf da ita kamar zai taba ta, yayi murmushi yace "ya kike matsawa haka kamar kinga wani dodo ? zo ki kwashe kada yakone. Ta katsa motsawa sai gabanta ke faduwa a lkacin ummi tashigo tana fadin "fatima kin gama ? Ganin wanda ke tsaye a kitchen din yasata tsayuwa turus tana kallonsa shi da fatima, ganin ummi yasa yatsuke fuska yafice daga kitchen din ummi takwashe kosai tana fadin "yau kuma meya kawo doctor kitchen din nan ko wani abu yake nema ? Kokarin da fatima tayi shine na daidita muryarta don kada ummi tazargi wani abu a ranta tace "ni ma gani nayi ya shigo. Kallon da ummin tayi mata shi ne yasa tafahimci kuskuren ta a bisa abinda tafada, to sai dai kuma batasan abinda za tafada din ba in ba hakan tafada ba, jikinta yakara sanyi sosai ganin ummi bata sake magana ba, takwashe kosan tace tadakko kunun gyadan dasuka dama zuwa falo. Bayan sun gama shirya tebur din ne tadubeta tace "ki je kigayawa doctor an gama shirya tebur kada yai sanyi yakasa ci. Cikin dacin rai fati tace "ni ce ma zan fadi mai ? kin taba ganin na nufi hanyar dakinsa. Ummi ta tabe baki tace "ai ba abin zafi bane gani nayi ya fi son yi miki magana fiye dani amma kar ki damu bari ni inje in gaya mai. Fatima taja tsaki tawuce daki, yayin da ummi tanufi dakin dr. khalifa ta kwankwasa yace "waye ? Tace "ni ce ummi. Ga mamakinta sai yace "shigo" Ta bude jikinta ba karfi yana kwance bisa gado yanuna wata kujera yace "zauna in miki tambaya. Ummi na son kallon fuskar dr. khalifa yana yawan burgeta nan da nan taji hawaye ya taru i donta tayi kasa da kanta, yana sane da halin datake shiga idan tana kusa dashi yashare domin shi ma din a halin yanzu abin tausayi ne duk yadda take son sbi ya fita son fatima kuma ya fita shiga hadari domin kuwa gab yake da yayi babbar asarar rasa fatima. Ke ummmi gaya min dangantakar ki da fatima". Abin da yace da ita knan lamarin dayasa tadago cikin sauri zuciyarta na bugawa sosai tace "ban gane ba yaya khalifa. yamike zaune bai ce komi ba, tunanin da yake kai komo a zuciyarsa shi ne shawarar da dr. bashir yaba shi duk a daren jiya lokacin daya same shi a waya yabashi labarin halin daya ke ciki yace "Bash don Allah kada ka kashe min guiwa ba zan iya hakuri da fatima ba ni kadai nasan halin da zuciyata ke ciki. Dr. bashir yayi shiru kamar ba zaiyi magana ba. Khalifa yce "ya ya naji ka yi shiru. Bashir yayi ajiyar zuciya yace "Abbakar ta yaya xa a maido wannan aure a kanka bayan sati biyu yarage kace ayi mata aure. Yayi tsaki yace "amma dai ni ne nafada maka saura sati biyu ayi bikin ko ? ka ga ba na bukatar kasanar dani shawara dai nanemeka bashir. Yace "to shi me rai ba ya rasa motsi, hanya daya ce wata kila idan munbi za mu iya dacewa. "Fadi inji" Bashir yace "ta hanyar ummi da mama ne kawai za mu iya yin nasarar jan hankalin fatima idan da rabo sai ayi nasara. Ummi tace Bashir ? Ya amsa "ita nace dalilin dayasa nace ita kuwa inada labarin cewa fatima ba ta da kawa aminiya abokiyar shakuwar data wuce ummi, ummi na iya sauya ra'ayi da tunanin fatima sbda yarda da amincin dake tsakaninsu, yayin da mma ke da girma a idon ummi ba ta iya musa maganar mama. Dr. khalifa yajinjina labarin a ransa yace "hakane Bashir to amma fa kada ka manta ba wanda ummi ke so sai ni, ban amince da auranta ba ta yaya za ayi ta amince da wannan batu ? Ba ka ganin za tayi amfani da wannan damar gun lalata min al'amarina da fatin ? Bashir yace "to ai daman ba kai tsaye za kagaya matan ba sai ka bi tawasu hanyoyin na hikima wanda zaisa ta fahimci kana sassauta zuciyarka akanta,ma'ana kadinga sakar mata fuska kuna hira kuma karara kanuna mata cewa kana bukatar ta taimaka maka akan fatima za kayi mata duk abinda take so, idan kayi mata za ta amince tunda tana sonka ba ta son damuwarka, sannan ita kuma mama ka marairaice mata sosai kanuna mata ba za ka iya rayuwa ba fati ba, so so ne amma son kai ya fi da sannu za ta tausaya maka tagoya ma baya. Dr. khalifa yakashe wayar kansa a daure tamau yana jinjina yadda zai iya jan hankalin ummi har ta taimaka masa, bayan magana ma ba yi mata yake ba, ya kwana yana tunanin abin ga dumbin ciwon so na karuwa a zuciyarsa har yana jin ina ma zai iya fidda son fati daga ransa ya huta, amma ina duk yanayin dazai shiga in dai zai mallaki fatin dole yajure tunda mallakar ta shi ne kadai kwanciyar hankalinsa da farin cikin rayuwarsa, amma fa yana takaicin hakan
Chapter 23 · 0% Book details