Sashe 20
A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
nacin da dole ya amincewa kwananta. agdansa, ahi kansa bai san dalilin dayake gudun kawo mace gdansa ba sbda anisa, tun daga nau'in kayan jkin shu baby za kasan lalacewar ya yi yawa, a ranta tace "tabbas yau sai na ga abunda khalifa yake tsoro, tabi bayansa zuwa ciki, anisa na kwance a bisa kujera a fali tana kallon wani film a wayarta, duk zamanta a gdan bata taba ganin khalifa ya zo da mace ba duk da ta san yana tare dasu sai fa yau, suka dubi kowa ita da shu baby kowacce tashaki wani masifaffan kishi a zuciyarta, anisa ta maida kanta tana kallonsu suka wuce dakinsa, bby tace "sbda wannan figigiyar yarinyar dama kake kin kawo ni gdanka? Yamata wani irin kallo yace "kiyi abinda ke gabanki shuu wannan kanwata ce ba na son.... Bai cigaba da maganar ba yashige toilet yayi wanka yayi alwala, bayan ya idar da sallar dake kansa yaleka falon yace "anisa wannan da kika gani abokiyar karatuna ce ki kawo mana abinci daki kuma ina so ki gaisheta. Yawan kukanta yana ba shi haushi ganin ta fara share kwalla yasa ya koma cikin daki, tunanin da anisan tayi shi ne wai ita wacece ne a gun dr. khalifa da har zai gujewa bacin ranta, tunda takawo kanta zama a gdansa dole tahakura da duk abinda za taji ko tagani, a sanyaye tamike tashirya abinci a tray tashiga dakin da sallama tatsuguna ta gaisar da baby tafita, kallon daya bita dashi yakara baiwa baby haushi taja tsaki tabude abincin taxuba a plate tafara ci, dandanon abincin ya burgeta ga takaici da kishin wadda tadafa, shima yazuba na sa yana ci yana fadin "kai aniaa ta iya girki mijin ta ya mori mace. Sun kwana suna morar junansu ta hanyoyi daban daban wadanda suka kware a kansu ko wannenau ba baya bane a wannan harkar, sun gamsu iya gamsuwa hakan yasa kowanne zuciyarsa wasai ba damuwa, khalifa na son yayi bacci sosai amma yunwa ta hana shi baccin dole yafito falo sai dai tebur wayam yaleka kicin ba abinci bbu anisa yadawo dakinta ya iske doguwar takarda mike bisa gado tun kafin yakaranta ya san abinda ta kunsa yace"shikenan shukura ta ja min asarar mai dafa min abinci da kula da gdana. Salam. Abbakar ina maka ban kwana tare da fatan allah yasa kagama karatunka lafiya ka koma gda lfya, xamana a gdanka ya kare ba tare da na gaji da ganinka ba sai dai yin haka shi yafi mana ni da kai, na gode kwarai dagaske da masuakin daka ba ni a gdanka duk da cewa hakkana bai cimma ruwa ba na samun masauki a zuciyarka wanda shi ne makasudin zuwa na wannan kasar, amma dai na godewa Allah daya ba ni ikon aikata abinda natabbatar zai wahala ka manta dani har ka koma ga mahallincinka, ina rokaonka a duk sanda katuna dani kai min addu'ar alheri. khalifa na zo wannan kasa ne dan neman soyayyarka da take ta cin zuciyata tun daga ranar da idanuna suka fara ganinka na yi suk kokarin da zan iya na ganin na ja raayinka banyi nasara ba, tun daga gda nigeria har izuwa yanzu dana tabbatar ba zan same ka ba, daga karshe ina maka fatan dukkan alherin duniya dana lahira. Ni na san bbu namijin dazanso bayan kai, Anisa.... Iya abinda takardar takunsa knan, har gumi yaji yana keto masa sbda tsabar tausayin anisa, yadinga jin wani iri a ransa yana tunanin rayuwar dasukeyi wadda ba ta da wani amfani a garesu, idan suna gaban iyayansu sai su dinga nunawa su na kirki ne amma a bayan idon iyayan na su suna aikata abinda suka ga dama. Shin tsakanin iyaye da Allah wa ya fi dacewa aji tsoro, in har suna boyewa iyayansu halin dasuke cki ne don suna tsoronsu, Allah daya halicci mutum shi yafi dacewa a ji tsoro, kuma Allah yana kallon mutum a ko wani hali yake. Wannan nasiha da khalifa yaiwa kansa yasa yaji nan take komi ya fice mai daga rai ya tsani yan matan dayake tare dasu na holewa, yana bukatar yazamo natsatsen mutum wanda yake biyayya ga Allah da manzonsa, takaicin abubuwa da dama suka kamashi har yaji kyamar kansa da kansa yakeji, yamike jikinsa ba kwari yafito daga dakin yadawo dakinsa, ya isje shu bby har yanzu baccinta take cike da nishadi da kwanciyar hankali, yasa hannu yagirgizata dakarfi tabude ido tana fadin "bacci ke damuna,yace " ba na iya juriyar yunwa. Tace "ina yar aikin gdan nan? Yace "ba ta nan. Ba abinda shukra tatsana irin girki amma da yake khalifa ne haka tadaure tadafa ruwan tea da dankali da plantain, ba wani kwarewa tayi da girkin ba yunwa ce tasa kawai yaci. ***** A DAREN FARKO 17 Tun daga wannan lokaci rayuwar khalifa ta sauya gaba daya yadaina sauraror kowacce mace har da ita kanta shuu babyn, hatta fAisal ya watsar dashi sbda ya yi ya yi yaja hankalinsa don shima yadawo hanya tagari faisal ya yi masa wani irin kallo shekeke yace "kai kiwa meya sameka da za kace mudaina rayuwarmu, tajin dadi mu takura kanmu, ko mafarki kayi ka mutu an sa ka a wuta? Khalifa yace "ko kusa banyi wani mafarki ba na dai yi wa kaina fada ne dan na fuskanci gaskiya, na ga yakamata inja hankalinka kaima damu daina wannan rayuwar kafin ranar nadama tazo mana. ko wata amsar kirkifaisal bai ka ra bashi ba yamike yavarshi a gurin,hakan yasa khalifa ya janye jikinsa yakoma rayuwarsa shi kadai, yanemi masu dafa masa abinci da gyaran gida bai zuwa ko ina sai makaranta inya dawo yakan kulle kansa a dakinsa yayi ta nazarin abinda yake karantawa ko karatun alkur'ani mai girma wanda a baya ko bude shi ba ya yi sbda shagalta da rayuwa da ya ya mata dayayi, sai yake jin dadin rayuwarsa a haka hatta hotunan sa da nambobinsa ya goge, yayi ta karfafar zuciyarsa tare da neman gafarar Allah yana rokon Allah yataimake shi yaraba shi da wannan rayuwa. A haka a haka har Allah yataimake shi yakammala karatunsa yakawo shi inda ya fito da kyakyawan sakamako zuwa babban likitan mata a lkacin ya dada kasaita irin mazan nan ne da dole idan aka kallesu a kara sbda cikar zatinsu, kwarjini da ilimi, 'yammata sun yi sunyi suja ra'ayinsa kowacce tana fatan yasota amma ya ki bada kai, matar aurance har yanzu baiga wadda yagamsu yaji ta yi masa zai zauna da ita a matsayin matar aure ba, amma dai mace ta holewa ya yi alkawarin insha Allahu ya daina. Kafin ranar dawowarsa gida nigeria ya yi ta neman yadda za ayi yaga anisa ya rasata haka a kano bai san a ina zai ganta ba, yana yawan jin tausayin ta tare da yimata addu'a duk sanda yatuna ta. Tunda ya daura damarar tahowa gida damuwarsa itace yarinyar nan ummi ya san ta yi girma yanzu sosai ta kara wayo a baya ma ta iya budar baki tace tana son shi ballantana yanzu, bayan shi ba wani sakar mata fuska yakeyi ba ballantana ace shi kwata kwata ba ya da ra'ayin auran zumunci kuma ko yana dashi ma ummi bata cikin lissafinsa, cikin hikima yatambayi mamansa a waya ko an yiwa ummi aure, tace ai bata fidda da mijin ba ma ba ta sauraron kowa tun da tayi candy abban k7ma ya ce ya dace ta fidda mijin aure tunda mutane dayawa suna nunawa suna sonta in ya so taci gabada karatun a gdanta sai tace wai wanda takeso din ya yi doguwar tafiya idan yadawo za ta gabatar dashi. Wannan yafadarwa dr. khalifa gaba ya tabbatar yarinyar nan in baiyi da gaske ba zata zame masa matsala, har ranar dawowar tasa tunanin da yake fama dashi a xuciyarsa knan, yarinyar tashiga ran mamansa za a iya cewa sai ya aureta ko da yake bai da matsala da abbansa, maganar mamansa kuma da karfi a kansa baya son bata mata rai. ***** Karfe sha biyun rana fatima tagama shiryawa cikin wata blue din batik mai haske riga da zani ne amma kai kace siket ne sbda yadda kayan suka zauna a jikinta suka yi mata kyau abin har ba a magana, ita da kanta ta yi sha'awar kanta sbda kayan sun mata kyau, telan dayayi dinkin ya gwanance a fagen tsarawa mata dinki, ta jima tana gyara gashinta ya dau kyalli ta tsara daurin dankwalin sosai yadda yadace da adonta tazuba fashion da mayafin da suka dace da kayan, ummi ce ta bukaci taraka ta gdansu yau wato gdan iyayanta, fati bata fiye son xuwa gdansu ummi ba sbda jininsu bai haduwa da hajiyarsu ummin ba tare da ta san abinda tayiwa hajiyar ba, tana cin darajar diyarta ummi ne kawai sbda a halin yanzu ummi tanad\ matsayi lamba daya a zuciyar fatima ba ta da na biyu kowacce irin alfarma fatima za ta iya yi akan ummi. Innar tana zaune a kofar dakinta tace "inna sai mun dawo. Tace "adawo lafiya a gaida su. Tayi sallama a kofar dakin malam musbahu yadago yadubeta sai yayi saurin bude idonsa gaba daya yace "kai fatima wacce irin kwalliya ce wannan? kin ga yadda kikayi kyau kuwa? Ta lumshe kyawawan idanuwanta tana murmushi tace "ka manta na gaya maka za muje gdansu ummi. Yace "fatima gskiya in banda ummi na da matsayi mai girma a gareni ba zan iya barinki fita cikin wannan kwalliyar ba ban taba ganin ranar dakikayi kyau a ido irin wannan rana ba, fatima ina fatan Allah ya mallaka min ke. Tace "malam ai ya mallaka ma saura kadan yarage komi lokaci ne. Ganin zai tsaida ita da maganganu na santin kyaun datayi yasa tawayance tafice tabarshi yana hadiyar yawu kamar yabi ta yayi ta kallonta yau kyaun datayi masa daban ne. Bayan sun gaisa da mama tawuce dakin ummi ta iske ta tana shiryawa tace "mutuniyar kin hadu kayan nan sun yi miki kyau bana wasa ba. Fatima tace "kai wai ke ba kya gajiya da yaba kyau na ne? kullum sai kin cena yi kyau. Tayi dariya tace "to ai yabon gwani ya zama dole kinyi kyaun ne ba na gajiya da kallonki fatima, don Allah idan kinyi aure kada kidaina kwalliya kina matukar