← Book details A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 50

Sashe 11

A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

amma ina dole tatashi daga gun tashiga dakin dasuke kwana da kannanta tazauna tana sharar kwalla, har goggo tashigo tazauna kusa da ita cikin saryin murya da tausayawa irin na d'a da mahaifi tace "fatima na san duk abinda zai dameki bai wuce maganar auranki da musbahu ba, fati kada kicutar da kanki idan ba kya son musbahu kina sane malam bazai matsamiki ba, shi ma tunda farko abinda yasa yace ya ba shi ke kai tsaye dan ya san dakake har musbahu babu wanda ba zai yi masa biyayya ba. Sannan ya yi la'akari dacewa ke da musvahu akwai kaunar juna mai karfi a tsakaninku tun kafinn ku mallaki hankalin kanku kusan ku waye ku a rayuwa. Fatima tace 'goggo inason yaya musbahu sbda ba shi da makusa da mace za ta ki shi hasalima banga abinda baba na zai bakata in ki yi masa ba, inji ina kinsa a matsayinku na iyaye na, biyayyarku a gareni wajibi ce, wannan damuwar tawa ba ta da nasaba na kin yaya musbahu sai dai ni kaina bansa abinda yashiga xuciyata ya tsunduma ni a bakuntar rayuwa a yau din nan . Goggo tayi murmushi tace "ai baki shiga bakuwar rayuwa ba fatima sai randa kika shiga gdan aure kika zamo matar aure lokacin ne za kishiga cikin bakuwar rayuwa wadda baki santa ba amma da sannu saiki zama 'yar gari har wata rana kigaya wa wasu yadda aka gaya miki, kowacce mace sai da tashiga irin wannan bakuwar rayuwar. Tashi maza ki kaiwa musbahu abinci daga yau haka za kidinga yi. Bayan goggon ma cigaba tayi da zama ta kasa tashi har sai da goggon taleko takara yimata magana sannan tafita tadauki abincin tanufi dakin musbahu dake zaure, ta yi sa'a ba kowa a dakin ta ajiye dasauri za tafita sai ga shi yafito daga toilet yace "to dawo kidana murna dodon na ki yananan, har wani rawar jiki kike za kigudu ko? Tayi murmushi tatsuguna daf da gado tarufe fuskarta da hijabi, yazauna akan kujera yace "fatima ki rufe fuskarki yadda kikeso sbda kina da abin rufewar, mace kyakyawa irinki ta isa tayi irin kowacci yanga ga kowane d'a namiji ko waye shi ballantana almajiri kamar ni. Fatima tun lokacin da baba yabudi baki yakira sunana har sau uku hankalina a tashe nadinga amsa masa sbda bansan wace magana zai gayamin ba wadda har tasa yayi min irin wannan kiran. Tun kafin yagaya min na san duk abinda zai gaya min din magana ce da muhimmancinsa ta isa. Fatima malam yabude baki yace dani "musbahu na ba ka auran fatima, wlh fati ban taba kwana a zaune ba, yadda naga rana haka naga dare hnkalina ya tashi kwarai dagaske ba dan komi ba sai dan tunanin dame zan rike mace kamar ke fatima. Ina sane dacewa mutane da dama suna tunanin inasonki ne sbda yanayin shakuwar mu tun kina karama nima ina karami to Allah yasani fatima ina matukar kaunar ki sbda haduwar jini da Allah kan hada tsakanin mutum da mutum amma Allah ya sani tun da nake ko da wasa ban taba kallonki da wata siffa ko da wata manufa ba, bayan kanwata ina kallonki ne a matsayin kanwata wadda muke ciki daya. Yana magana ne cikin yanayin tausayin kai muryarsa kasa kasa yana mata wani irin kallo, lamarin yajefata ckin sabon tashin hnkali da rudani idanunta suka kama zubar da hawaye, fatima ban taba tunanin akwai lokacin da xan iya zama in miki maganganu makamantar wannan ba sbda kallon ki nake kamar kanwar damuka fito ciki daya. Shi yasa nayi ta jinjinawa yadda zaman aure zai kasance tsakanina dake. To amma a safiyar yau abokina mansur yasauya min tunani akanki ya ce dani 'tunda aure bai haramta tsakanin ka da fatima ba ba yadda za ai kunya tahana muku nishadantar da zuciyarku ta hanyar soyayya, shi aure dakuke gani ba bu abinda yake rike shi yazauna lfya sai soyayya. Ya jawo abinci yakama ci yana cewa "fatima har na rasa dawata kalma zanyi amfani a bakina kan yiwa Allah godiya daya azurtani da mace kamarki, fatima in sonki wlh don Allah ni ma ki ce kina so na inji dad'i. Bai aune sai kawai yaga ta tashi ta faki idonsa ta fice daga dakin a guje ya kyslkyale da darya har da tafa hannu yace Allahu akbar, fati manya shi abinda yake ba shi mamaki shi ne wai an wayi gari shi da fatima sun zamo masoya soyayya kuma irin ta aure. Tabbas Allah ya amshi ran mahaifinsa ya zamo maraya sai dai shi maraya ne wanda yai rashin mahaifa amma ba wanda yarasa iyaye ba, a rayuwa iyaye suna da daya wa mahaifa ne kwara d'aya kachal, shi kam Allah yai masa baiwa da iyaye nagari yagirgiza kai yana murmushi. ****************wannan page goron jumma'a ne gareku ba ki d'aya,,,, daga jiddan nan dai 'yar mutan A DAREN FARKO 9 karfe goma da minti hamsin hajiya saudat ta faka motarta a kofar gdansu ummi, ta sha ado da wata galleliyar shadda maroon colour, ta yi kyau kasancewar su kam Allah ya hore musu kyau da son gayu. ita mijinta ba wani mai wadatar zuciya bane sosai kusan itace mai kudin don yar kasuwa ce, daga kasar dubai ake kawo mata kayan sa wa na mata, koyaushe gdan ta cike yake da mata business takeyi ko ta ina. Ita kam Alhaji muhammad ne asalin ba ta jari amma duk da haka ba sa gani. Taahigo uwar dakin hajiya hauwa tana kwance kan gado ummi na kwance gefenta zancen khalifan dai suke, saude tace "kitashi mana tun yanzu kifara shirya kayanki don da kaina yau zan kaiki gdan alhaji muhammadu chan za ki zauna ni zan xan gaya masa cewa tunda Allah yayiwa mahaifinku rasuwa ya zama dole a tallafa yaya hauwa a gun rikonku, na san dai idonsa da kunya ba zaice ba za ki zauna mai a gda ba sannan ita hajiya maijidda na san za tai farin cikin xaman ki a gdanta, don za ta ga cewa haka zaisa tasamu fada a gunmu ke Kuma idan kinje ba cewa akayi kisaki jiki kina bacci ba, yakin neman zuciyar khalifa za kiyi ko ta halin kaka sannan ki dage dun kyautatawa uwarsa, yin haka ne zai sa in yadawo daga germany ko bai sonki da kansa ita za takalli kyautatawar da kike mata ta tursasa shi ya aureki, kin san son uwa shi ne son d'a, Hajiya hauwa tace "wannan shi ne hanya mafi dacewa. Zuciyar ummi fari kal san da tagama sanya kayanta suka nufi gdansu khalifa, . A bisa hanya hajiya sauda atana ta wassafa mata yadda za tai amfani da damarta duk san da take dashi don jan hnkalinsa. Ummi jin ta kawai tana dura mata a zuciyarta, daga alhajin har hajiya maijidda sun nuna jin dadin zaman ummi a gdan daman fada ne ba na so nayi a samu matsala in ba haka ba in ba haka ba idan hauwa da duk yaranta sukace za su zauna a gdan nn, rikesu xan iya insha Allahu. Daki guda aka warewa ummi a gdansu khalifa kusa da na mama, akwai gado da dressing mirror da toilet acikin dakin, tun a ranar da taje gdan aka gama wannan mama maijidda tace da ita '"gdan nan gdanku ne kin sani ki dauki kanki fiye da yadda kike rayuwa a gdan iyayanki, duk abinda kkeso akwai su idan ma babu kada kigawa kowa kigaya min in har da kudi za a siye shi zan saya miki ummi. Batazo gdan nan dan cutar da khalifa ko iyayansa ba dan haka za ta nemi soyayyar khalifa a bisa hanya ta gaskiya da tsakani ga Allah. Ta tashi tabude kofar sakamakon kwankwasawar dataji ana yi, daya daaga ckin yan matan dake aiki ne tace da ita, "Mama ta ce in zo in ce miki an gama sanya abinci a tebur kifito kici. Ummi tace "ki ce ina zuwa. Har yar aikin ta tafi ta kirata tace "meye aikinki agdan nan? Tace wanke wanke wani lokaci ina yin girki. Ta jinjina kai tace "wa ye yakedafa abincin da yaya khalifa yake ci? Tace"yana da kyankyami bai yarda da abincin mu ba shi da abbansa mama ke dafa musu abinci sai dai mu tayasu shirya tebur kawai Tace "yanzu ya dawo? Tace "eh yana falon dasuke cin abinci shi da iyayansa. Cikin zumudi ummi takoma daki gaban katon madubi ta tsaya tana kallon surar jikinta, daga sama har kasa tana tmbayar kanta shin tana da tagomashin da zata iya jan hnkalin namiji kamar khalifa? Tafito falo cikin yauki khslifa yana zaune kusa da abansa kan kujerar zaman mutum uku sanye yake da bakar kot, da wandonsu. Zahiri da badini khalifa ya yi kyau ba na wasa ba kamar yadda yake kyau a idon kowacce mace ballantana ummi data mutu acikin soyayyarsa. Ta gaidasu gaba daya, kallo daya shi ma khalifan yayi mata yamaida kansa ga jaridar da yake dubawa kafarsa daya tana kan daya, mama ce tace dashi khalifa ga kanwar ka nan ummi ta dawo gdan nan da zama. A nan ne yadan ajiye jaridar akan cinyarsa yakalli ummi suka hada ido yayi mata murmushi takaitacce yamaida ganinsa ga mama yace "ya yi dai dai hakan kinga kin samu mai tayaki zama. Tsigar jikin ummi yadinga tashi sakamakon murmushin khalifa da ta gani kuma ita yayiwa murmushin. Karfe taran dare khalifa yatashi yawuce dakinsa ya kara yin wanka yasauya zuwa blue din jeans da farar t shirt yazuba wani mai tsadar takalmi ga farin gilash dan siriri ya manna ya fesa turare yadawo falon da iyayansa ke zaune yarusuna daf da abbansa yace"abba ba ni aron makullin motarka za ni unguwa in dawo. Ba musu yazaro key din ya damka masa yakalli mama yace "mom sai na dawo. Ta sha kunu sosai tace ina za ka a wannan daren? Yadubi agogo yace "mom wani abokina zan duba a asibiti da asubahi za a tafi dashi egypt. Tarasa abinda za tace sai kallo tabisa dashi har yafice kamar yadda itama ummi ta lalace kan kallon sa. Tabdijam ashe jan aiki ne a gabanta ********** Khalifa bai dawo ba sai biyu da rabi na dare, yana shiga dakinsa yafada bisa gado bacci yai awon
Chapter 11 · 0% Book details