Sashe 43
A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tace "Ya fita amma tunda yamma tayi yana hanyar dawowa. Tace "Bari in yi sallah in je gdan su Ummi wai tana shigowa kuwa na san rashin kirkita. Umma tagirgiza kai tace "Wayyo Allah ai ummi gaba daya ba ta ckin natsuwarta hankalin kowa a tashe yake sakamakon wani abin tausayi daya faru. A firgice jiddah tace "Mr ye umma ? ko shiyasa idan namata waya ba ta shiga a kwana biyun nan ? Tace "ai idan kikaga ummi sai kin tausaya mata sbda firgicin data shiga ai na yi zaton ta gaya miki a waya ma ? Jiddah tace "wai me yafaru ne umma ? Umma taja dogon numfashi tace "Uhum ai jidda a ranar aka kashe Dr. khalifa da Fatima ,yanzu haaka zancen danake miki fatima na kulle ana tuhumarta da laifin kashe Dr. khalifa. Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un. Jiddah ke maimaitawa jikinta na rawa tabugi kirji tace "Mama an kashe khalifa ? Ta amsa cikin tausayi. '"An kashe Khalifa jiddah kuma fatima tana cikin mummunan zargi don ita da kanta ta amsawa kotu cewa ita ta kashe shi. Jiddah ta girgiza kai ta mike tsaye tace "Fatima ba za ta kase Dr. khalifa ba, ko da ace ba ta son shi ba ta da dalilin kashe shi akwai wadda na sani wadda ke da dalilin kashe shi kuma shi ta kashe shin ni ce zan fasa kwan, nasan waye yakashe Dr. khalifa. Alhamdulillahi. Masu karatu a yi hakuri ayi jimirin biyoni a littafi na hudu kuma na karshe don jin ya zata kasance, waye yakashe Dr. Khalifa ? A DAREN FARKO 36 NI na san wanda yakashe Dr. khalifa da dalilin dayasa aka kashe dr. khalifa.Jiddah taci gaba da tayar da maganar wanda yasa mahaifiyar ta ta cikin tashin hankali, ta zaro idanuwanta gaba daya cikin kaduwa take kallon jiddah tace "Ke 'yar nan kin san abinda ki ke fada kuwa ? Na sani Ummah, "kin sani jiddah ? "Eh na sani mana umma, idan babu rami babu abunda ke kawo batun rami, wannn maganar da idan mutum yadauketa ya san abinda yataka, haka kawai baxai fada ba sai yana da hujjah hujjar ma mai karfi. Umma ta jinjina kai har yanzu fuskarta a razane tace "Jiddah ki yiwa Allah da Annabinsa kada ki kara furta wannan maganar ballantana wani yajita kija bakinki ki shiru. Jiddah tai murmushi tace "Ummah na yi zaton za kitambayeni inda nasan wannan maganar me cike da gagarumin sirri ba wai ki dinga rokar kada in fada ba, yaya lallai in boye wannan maganar ko kuma kiyi shakkar inda naji ta. Umma ta girgiza kai tace "Jiddah tsoron hadarin dake cikin maganar ne ya firgitani yasa narude ni din ma dakike fadawa tsoro nakeji ballantana idan magana tafasu kowa yaji, kin san irin wannan maganar gagurama ce kuma ni banyi shakka don na ce kina da masaniya akan kisan khalifa ba sbda bazai yiwu kifadi hakan ba face lallai kin sani, mamaki na shi ne a ina kika sani ke da ba ki a kasar, to amma tsoron danaji yasa maganar mamaki ta kau a zuciyata nake roko ki rufawa kanki asiri ki rufa mana. Da zarar kin furta wannan maganar za a shiga tuhumar mu. Jiddah tace "Umma yaya za ayi ina ganin gskiya kiri kiri a rufeta, yanzu sai kisa ido a kashe Fatima ? Alhali ba ita takashe khalifa ba dole in bayyana wanda yakashe khalifa yau din nan, tamike tsaye. "Umma ki kwantar da hankalinki babu abinda zai same mu sai alheri insha Allahu, itama umman mikewa tsaye tayi tace "ta ina zan kwantar da hankalina jiddah ? ai hankali ya bar kwanciya in dai kika fasa wannan maganar ni dama na sani ban fadi miki ba. Tace "Ummah ko baki gaya min ba zanji ke dai ki tamin addu'ar neman kariyar Allah ahine me kowa da komi, tarike hannunta lokacin data yi hanyar fita tace "jiddah kar dai kijefa kanki ckin hadari, takatse ta umma bazaki tambaye ni wanda yakashe dr. khalifa da dalilin kashe shi ba sai rayuwa ta kike neman karewa to bari kiji, "Kariya tana gun Allah ban taba tunanin zan dawo nigeria a wannan lokaci ba haka kawai ina zaune hankali na naji ya tashi, Allah ya dawo dani ne don yatoni asirin wadanda sukayi wannan kisan . Allah ya dawo dani ne don ya kubutar da Fatima kinga kuwa ba ni da dalilin dazai sa in rufe bakina don in kare rayuwata, jin an yi kiran sallar magriba yasa jiddah tafita tana fadin "ina zuwa ummah. Hankalin ummah yatashi sosai zuciyarta tashiga harbawa, kar fa yarinyar nan tajawo mana fitina ya kamata in sanar da babanta halin da ake ciki, wannan maganar me hadari wa zai sa kansa a ciki don wauta ? Tana cikin wannan tunanin babansu jiddah yashigo tare da babban yayansu Alhaji Nazifi, tace "Yawwa Alhaji gara da Allah yaka wo ka jiddah dai ta dawo mana da fitina tana neman jefamu ckin zargi. Yace "me ya faru daga dawowarta ? Ta bayyana masa duk abubuwan dasuka tattauna da jiddah, hankalinsa shima yatashi, Nazifi har ya fi abban na su fusata yace "kin ga yarinya mara hankali ? wa yagaya mata ana irin wannan ? Alhaji yce "Dakata, tanada dalilin fadin hakan, ta gaya miki ? Umma tace "Yo Alhaji ni da hankali na yatashi ina na tsaya tmbayarta wanda take nufi ya yi kisan. Yace "yanzu tana ina ? Tace "ta fita nasan dai ba za tawuce gdansu dr. khalifan ba ko gdansu fatima. Yadubi Nazifi yace "maza nemo mini ita a waya, zo muje masallaci mudawo, Alhaji Nazifi yayi kwafa xuciyarsa cike da haushi nomban jiddah tana dagawa yace "Ke fitinanniya munji maganar dakika zo da ita sai ki zo kiyi mana bayani. Bai jira jin abinda za tace ba yakashe wayar. Suka yi alwala suka nufi masallaci. itama umma alwalar tayi tai sallah zuciyarta cike da fargaba sai a yanzu take son jin hujjar da jiddah ta taka take furta cewa ta san wanda yakashe dr. khalifa. **** A harabar gdansu ummi, jiddah ke tsaya tana neman wata waya kiran yayanta yashigo, don haka tafasa shiga gdan tadawo da baya zuwa gdansu kafin baban na ta sudawo daga masallaci itama tayi ta ta sallar. Kannanta duka suna falon da abokiyar zaman umanta hajiya zainab da suke cewa Anti, Abba da Nazifi suka shigo har gara fuskar Abban tana nunawa zai karbi maganar da fahi ; ta. Nazifi kuwa gallawa jiddah harara yake kamar ya shaketa yahuta, ya tsani ana zaune lafiya a tado da ftina. Jiddah na zaune gaban abbansu ta lankwashe kafafu kanta na kasa tana mai bayanin daya daurewa kowa kai, babu wanda yakatse ta sai da tayi shiru. Nazifi yaja tsaki yace "kai jiddah ni duk da haka inain wannan abubuwan dakika fada bai isa ya zamo hujja akan wannan gagarumin magana ba,. Shari'a fa sabanin hankali ce kuma ita an yi mata lakani da mace mai ciki ba a san abinda za ta haifa ba, sannan hausawa sunce idan baka iya kama barawo ba barawo sai ya kamaka, eh abubuwan da kika fada mana ya isa a dubesu a yi nazari amma ba zai isa gamsashiyar hujjar da za a tunkari kotu da ita ba kai tsaye sai an yi dogon bincike da taka tsan tsan sbda kotu ba gun wasa bane. wannan maganar saita jefamu a wahala. Umma tayi farat tace "yawwa alhaji abinda nake son ka kalla knan mutum yana ckin zaman sa lfya bai dace yadauko ma kansa abinda zai zama fitina gunsa ba, wannan magana ce me sarkakiya. Jiddah tace "ki kwantar da hankalinki insha Allahu Allah zai fitar damu ni dai addu'arku nake nema, ina ji a jikina wani nauyi ne ya hau kaina wanda ya zamo dole in yi magana a cikin wannan lamarin idan nazauna inajin tsoro za ayi kwaba. Gaba daya suka yi shiru kowanne zuciyarsa bata gamsu da abunda jiddah ke niyyar yi ba a son ransu abba ya hana amma ga mamakin su sai ga abban na cewa "Allah ya taimake ki jiddah, Allah ya tsareki. Dama kowa ya san fatima ba ita tayi kisan nan ba fatima ba za takashe khalifa ba. ***** Daga wanna rana rayuwar Jiddah ta kasance a boye babu wanda yasan tana kano sai 'yan gdansu har zuwa ranar da kotu za tazauna don yanke huku ? cin karshe tunda dai wadda ake zargi ta amsawa kotu karara cewa ita tayi kisan. A ranar fatima fuskarta ba tashin hankali sosai idanuwan ta ba hawaye sai dai jawur dasuka yi. Yau kotun ta cika makil, 'uyan'uwan fatiman har wadanda basu taba halartar kotun ba yau sai da suka zo. Ummi na zaune kusa dasu inna kamar yadda tasaba kanta na kasa. Fatima na tsaye kan minbarin amsa kara bayan mai karanto kara ya karanto. Kafin kowa yace komi sai akaji barrister abbas ya tashi ya nemi izinin magana. Alkalin yace "yana da damar yin hakan, yayi godiya sannan yashaidawa kotu cewa yau ya zo da babbar hujjar da zata gamsar da kowa cewa ba fatima ce tayi wannan kisan ba, aka bashi izinin yagabatar da hujjarsa. Wata kofa ce tabude jidda ce tafito, lamarin dayasa kallo yakoma kanta ana shirin ganin abinda zai faru, itama fatiman kallon jidda kawai takeyi cike da mamakin lamarin kamar yadda fuskar kowa a kotun yanuna ckin wadanda suka san jidda, kowa ma knan ballantana babbar aminiyarta ummi. Barrister abbas ya gabatar wa da kotu jidda da kuma rokon kotu tabawa jidda daman gabatar da bayanin datake dauke dashi, ake ce duk za a iya yin hakan. Bayan jiddah ta yi sallama tafara da fadin "Ina gdan da nake zaune birnin london wani yamaci naji wayata na ringi ? g ina dakkowa naga nomban babbar aminiya ta ummi, hakan yasa nadaga dasauri muka gaisa na tambayeta labarin gida da rayuwa. Tace "komi lfya jiddah, sai dai ni ina cikin matsanancin tashin hankli wanda yasa rayuwat ma gaba daya ta fita daga raina. Nace "Subhanallahi me ke damunki kike fadin haka ummi. Tace "eh to jidda a iya saninki dai kin san tun tasowa ta ma'ana lkacin da na mallaki hankalin kaina babu abinda yake barazana da duk wani farin ciki na rayuwata wanda