Sashe 38
A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da yake so ba, sai kawai tabishi suka shiga dakin musbahu wanda yake zauran gdan, dasauri ya rungumota sannan yayi ajiyar zuciya mai karfi yayi mata kiss, ya saketa yace "to zo ki shiga gida. Mamaki yasa ta tsaya galala tana kallonsa, yakama dariya yace "ai dama ba wani abu mai yawa zan miki ba soyayya ce ta yi mini yawa, shi yasa idan idan ina gabanki bana iya jurewa, ki yi hakuri daga gobe idan Allah yakaimu na zamo mijinki za ki ga abubuwa da dama a tare dani, kada kidamu soyayya ce wadda za takasance abar alfahari gareki, sai kinyi tsammanin kin fi kowace mace sa'a a duniya, zan tabbatar miki ina sonki, zan baki kaina kiyi yadda kika ga dama dani fatana dai kiji tsoron Allah, kiyi min adalci kada kiyi amfani da wannan damar ki wahal dani, kiyi hakuri mu zauna lfya shi ne kadai abinda zai sa in samu farin ckin rayuwata. Babu abinda fati ke iya ce masa sai kallo da ido, abubuwan datake ji game dashi a zuciyarta ya fi karfin ta iya fda masa da baki sai dai tabarwa zuciyarta, ita dai ta san tana son dr. khalifa kuma in dai haka soyayya take hakika masoya suna fama da wahala, meye wahala? wahalar ciwon so daban ba kamar kowacce wahala bace, in da wahalar take shi ne in dai mutum bai ga wannan masoyin na sa ba to zuciyarsa na cikin fitina da garari. Yarike hannunta kam kam yayi mata kiss, sannan ya saketa ya fice, ita kuma tashiga gida ta iske ummi da inna suna hira. A cikin daki ummi tadubi fatima tarike kugu tana murmushi tace "amarsu ta ango in ji ko dai dr. khalifa ya fara latsa jikin ki ne.? Tafiddo ido tace "Ban son sharri ummi. Itama ta tsareta da na ta idon tace "ke fatima kada ki mayar dani yarinya karama mana daga lokacin da soyayya ta tsumu a zuciyar mace budurwa mai tashen kuruciya irinki har takai namiji ya fata tabata sai ta sauya. Duk da kyau da ki ke dashi a baya amma yanzu kina da bambamci, idan ke baki san yanayin jikinki ya sauya ba ni na san ya sauya. Fatima taja doguwar ajiyar zuciya ta zauna gefe tana kallon immi, takasa magana. Ummi ta kyalkyale da dariya tana tafa hannuwa tace "Daman akwai lokacin da za ki iya soyayya ? Tadan yi murmushi tace "Anty ummi ai dr. khalifan ne ya isa a so shi ya hadu. Ummi taji wani dam a jikinta da zuciyarta kamar za ta shaki wuyar fatima tace "tashi ki shirya fita zanyi a yi miki gyaran jiki mun dai makara jibi a cigaba. A kofar gdansu dr. khalifa, fatima ta kafe akan ba za tashiga ba ita kunya take ji, ummi tace "ki rufa wa kanki asiri idan mama taji kin ki shiga fushi za tayi dake, idan ma kin sa wa zuciyarki surukuta da kunyar mama to wahala za ki ba kanki tunda kin san ita wayayyar mace ce bbu ruwanta da irin wadannan abubuwan. A harabar gdan suka ci karo da mama ta yowa baki rakiya, bata amsa gaisuwar fatima ba sai harararta datayi tace ke kin dauke kafarki daga gdan nan wai ke suruka ko ? Fatima ta sunkuyar da kai tana murmushi, ta gayar da baki, tawuce ckin gda da sauri jin mama tana fadama bakinta cewa wannan ce amaryar khalifa. Ai kuwa suka fara fadin "kai msha Allahu wannan yarinya da kyau take ya more mace ga kyau ga kuruciya. Daya daga ckin bakin tace "to ai ta fishi morewa a wannan zamanin samun namiji irin da na khalifa sai an tona kinga kuwa mu za muyi yanga va mu za a yiwa yanga ba, tunda duk inda danmu yake rububinsa ake. Bayan sun tafi mama tadawo ckin gida ta samesu a falo tare da anty sadiya ,tace "yawwa "yammata a zo a dafa ma abba abinci saura yan mintuna kadan bakinsa su iso. A ? ty sadia tace "mama munada abubuwa da yawa da za muyi fa lokaci zai kure mana. Tace "ai komi za ayi dole a tsaya a yiwa mai gidana abinci in kuma ba haka ba a fasa fitar. Ummi tace "tabdijam ai kuwa mama a yadda muke ji da amaryar nan tamu yau ko tsakar dare za mukai a gdan mai gyaran jikin nan xa mu kai, mai kunshin ma daukarta za muyi mutafi da ita. Mama tace "Lallai abin naku nayi ne sai ku kira angon a waya yazo yabada kudin kunshin don kuwa bbu wanda zai biya masa kudin kunshin matarsa tunda don shi za a yin. Anty sadiya tace "Eh ko zai bayar kema sai kin bayar da wani abu mama kudin fa da yawa. Tace 'Au tausayin khalifa kukeyi ni baku tausayi na ? duk fa abubuwan nan da ake yi ko sisinsa bai kashe ba hatta walimar nan da za ayi idan allah yakaimu goben su dr. hafiz ne suka dauki nauyi da wani abokinsa da sukayi karatu a jamus, to ko nawa yabayar gun kunshi ai ba wani abu ko ? Ummi takirashi a wya tace "yaya kana ina ne ? Yace "mun fita dasu dr. bashir. Tace "To muna bukatar kudin kunshin amarya da gyaran gashinta. Yayi wani mur. ushi yace "Da kyau ummi idan har aka yiwa amaryar nan tawa adon daya birgeni ni nasan kyautar da zan miki ko nawa ne zan biya a yi mata in dai zai yi kyau. A DAREN FARKO 32 Ummi tayi dariya tace "yaya knan in dai batn kyau ne yau za mukai amaryarka in da za ka kasa gane ta sbda kyaun da za tayi. Khalifa ya kyalkyale da dariyan da bata taba jin ya yi ba yace "kia ina ja fa ummi amaryata fa me kyau ce shi yasa na zabeta a cikin dubban mata nace ita kadai zan aura sbda dogon nazari nayi a kanta tun daga lokacin da idanuwa na suka fara gani? ta. Ummi ta cije lebe tare da runtse ido har wani gumi taji yana tsiyayo mata sbda daci da ciwon maganganun da khalifa yake yaba mata, ji take kamar ruwan zafi ake watsa mata a jiki, shi yasa nan take tajike da gumi, a hankali tace "yaya khalifa wai don Allah me yasa kazabi fatima ka fifita ta akan duk wata diya mace, har kabata matsayi me girma a zuciyarka? Yace "Ummi na ji dadin wannan tambayar da kika yimin domin ina son in ji ina fadawa wanda yashafi fatima matsayin fatiman a zuciyata don yarinka karfafa mata xuciya tana sanin cewa dagaske nake. Ummi tace "to in banda abinka daman yaya khalifa ai fatima ta san kana sonta ,yanayin soyayyar dakake nuna mata ne ma yake karfafa mata zuciya take kara sonka tare da sakin zuciyarta ta yarda da son da kake mata, in ban da haka fati za ta iya sanya shakku a zuciyarta game da kai sbda yanayinka. Khalifa ya dan tsuke fuska yace "sbda me kika ce hka ummi? wannan magana ta ki ta ban mamaki don Allah yi min karin bayani. Tace "yaya khalifa a yanayin rayuwa irin na fatima dole taji tsoron sakin jiki dakai idan tana kallon yadda rayuwarka ke tafiya, kayi mata nisa nesa ba kusa ba, amma dayake kana nuna mata soyayya mai karfi ta yarda dakai ta amince akan kana mata so na gskiya, ina ganin idan haka ne ba ka da bukatar wanda zai ci gaba da nusar da fati soyyarka gareta. Khalifa yace "kuma hakane amma duk da haka ina bukatar taimakon ku fatima yarinya ce. Bayan sun yi sallama ummi ta ajiye wayar a gefe tayi tagumi, wannan soyayyar da dr. khalifa kewa fatima tana da yawa, fidda fati daga zuciyarsa abu ne mai wahalar gaske, wace hanya za tabi knan, ta ina za tasamu khalifa? Duk kudin da suke kashewa a gun malamai abin ya ci tura tamkar suna asirin karawa dr. khalifa soyayyar fatima ne, aiki ne ja a gabanta tun da ta tabbatar wa ranta ba za ta hakura tasa ido wata diya macen ta mallaki khalifa ba in dai tana raye. Tayi kwafa tamike tabi fatima da anty sadiya inda suke girkin abincin Abba. Suna ckin shirya tebur khalifa yashigo gdan cikin sauri tare da dr. Bashir, kai tsaye suka wuce tebur din wai dama yunwa sukeji, mama ta harare su tace "ai duk yunwar ku ba za kuci wannan abincin ba. Khalifa yaduvi fatima zai yi magana mama tace "oh za kace mini matarka ce tayi ko? Yarufe baki yana dariya, fatima dai tabar dakin dasauri tanufi dakin ummi suka yi sallar azahar ummi tashigo musu da abinci suka ci a tsatsaye. Kudin da dr. khalifa yaba ummi na gyaran jikin amarya sai da suka firgita su sbda yawansu, ta yi murna sosai domin abin nema ya samu a ranta tace "ka ba da kudin da za a yaki soyayyar fati a zuciyarka da sannu za kagane kuskurenka. Mama ma tadada musu kudin tace su sayo duk abu! uwan dasuke bukata har na su ma kansu ita da anty sadiya. Da yake lamari idan nakudi ne bbu matsala suna zuwa gdan gyaran jikin aka watsar da kowa a ka dukufa akan fatima babban guri ne kamar wata ma'aikata, ayyuka sukeyi kala kala, cikin awa biyu xuwa na uku fatima ta sauya gaba daya ta dauki walwali abin ba acewa komi, anayi ana turara mata jiki da turaren wuta masu kamshi mai sanyi da shiga rai ga humra ana mulkawa. Bayan an gama da nan aka zuba mata kamshi kafa da hannu masu gyaran gashi na tsaye sunayi fatima tazamo tamkar tauraruwa a cikin taurari hatta su ummi da sadiya lalacewa sukayi gun kallon fatima sbda kyau datayi ya wuce misali, ga wani kamshi mai dadin gaske na tashi a jikinta, basu dawo gda ba sai karfe sha dayan dare, tuni angonta yadamu da son ganinta yanata kiransu a waya suna mishi dariya. Yana tsaye yana waya dawasu abokansu yan kaduna yaga shigowar motarsu, yayi saurin katse wayar yace zai kira yafito. Kafin ya iso garesu anty sadiya taja hannun fatima suka shige gida, suka turata toilet wai tayi wanka ba ta son dr. khalifa ya ganta lokaci guda