← Book details A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 50

Sashe 2

A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yadda kaso yankewa mutum wahala idan Allai bai kaddara lokacin yankewar wannan wahala ta sa ta yi ba ba za ka iya yanke masa ba. na godewa Allah daya kaddara min shiga wannan hali ina fatan wannan jarabawar da Allah yayimin tazamo kaffara agareni, ummi inaso kisani ban tsananta bakin ciki akan halin danake ciki ba ni a karan kaina wannan kukan dako dayaushe za aga idanuwana na yi inayinsu ne sbda tausayin iyayena daku yan uwana a Bisa halin dxaku shiga ba bakin cikin halin dana tsinci kaina a cikinsa, dkuma uwa uba rashin mijina wanda xuciyata ba ta da juriya akan wadannan abubuwa biyu, wannan damuwar ba zanyi kuka ba inhar akan halin danake cikibne. Zaman danake ummi ina jiran ranar da za ayanke min hukuncin kisa ne inbi mijina. idan har akwai taimakon danake da bukata daga gareku ayanxu shi ne ku taimaka ayanke min hukunci inhuta wannan damuwar kuma kuhuta domin idan an kasheni kun daina ganina dole watarana kuhaura idan ko ina raye haka xa kuyi taxama cikin damuwa. Wannan shi ne dalilin dayasa naki magana a kotu kuma ina nan akan bakana na ba xance komai a kotu ba don ba ni da abin cewa duk abinda xan furta bai wuce ince ba ni nakashe doctor ba, idan nace ba ni nakashe shi ba in neman kariya knan wadda e nufin inci gaba da rayuwa alhali ni kaina banga amfanin rayuwata a duniya ba. Umi kiyi hakuri kiba iyayena daduk yan uwana hakan kirokar min su gafara kowa yayi hkuri yamanta dani ba na bukatar taimakon kowa agareku sai addu'a, na gode kwarai dagaske kada kisake wahalär dakanki gun dauko min lauya....... Ummi takatseta cikin huci tace "Fatima kin amince kidauki laifin daba na ki ba, kin amince kikashe kanki,? wayake kin taimako kin amince kijawa dukkan zuri'arki abin fadi? kina zaton wannan ba zai zama mugun aibi ga zuriarki ba? wanda xaija adinga aibata muku zuri'a mata surasa mazajen aure? Kina zaton idan ankashe ki wani zai sake zama lafiya acikin iyayenki da yan uwanki? To kisauya tunani lauya tunda kince ba kya so na janye shi, amma ko shakka babu kuskure ne babba wanda xa kitafka idan har kikayi ikirarin kece kika kashe docto khalifa alhalin ba ke kika kashe shi ba. Fatima tace toh idn ni nakashe shi fa ummi? Ummi tayi murmushin takaici tace ba ke ce kika kashe docta ba, dankuwa ba ki da dalilin kasheshi, kina fadin hakanne kawai dan kin gaji da duniya ba kyason rayuwa a halin da kinason ki gaggauta barinta, shiyasa kike furta abinda xai raba ranki da gangar jikinki". Dan sanda yace "Lokaci ya yi" Ummi tace kayi hkuri ina fada mata abinda xai amfaneta ne. Yace ba shi da amfani gareta da saita karba kidaina wahalar da kanki. Ya tisa keyar fatee, kallon data waiwayo tayiwa ummin tawuce shiya sa tsigar jikin ummi tashiga tashi tazube a kasa tarika kanta da hannu bibbiyu. Shi kansa barrister nura jikinsa ya yi sanyi, ya jima xaune agun yana kallon ummi daga can yadan ja numfashi yace "Tashi mutafi ummi tun anan na tabbatar yarinyar nan fati ba ita takashe docta ba dukda Cewa ta ki amincewa daduk wani taimako daxa abata ta rufe duk wata kofa takariya daxa a ba ta, bawani abune kuma yasatayi hakan ba ta yi ne kawai sbda bakin ckin dake damun xuciyarta wanda yake tafarfasa xuciyarta yasa rayuwa tafita a zuciyarta. Hakan yasa taki mgana a kotu sannan taki yarda da taimakon da za a ba ta, ba komi Llah yana tare damasu gaskiya, sannan ba ya goyon bayan zalinchi, indai ba ta da hakki dasannu xa kiga hukuncin da Allah xaiyi. " Ummi bata kuma cewa komi ba har suka fice daga gun. [5:07PM, 7/13/2017] ‪+234 706 196 7803‬: A DAREN FARKO 2 dasauri yagoge hawayen dake zuba a idonsa jin sallamar matarsa, goggo Abuwa tazauna sharaf a gabansa jikinta na rawa ta ajiye flask d'in abincin datazo kawo masa, yadda jikinta ke rawa haka muryarta take rawa, tace "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un malam kuka kake? Yayi d'an murmushi yace "haba dai kuka ba kuka nake ba Zainabu. " Tace "Dom Allah karkace haka malam bayan na gani da idona kana kukan kuma na ji shasshe'kar kuka, malam idan kayi kuka akan wannan al'amari mu kuma yaya za muyi da ranmu? Kai kake nuna mana muyi ha'kuri bisa fushi dayin Allah me zai sa kai kayi. " Malam musa yace "Zainabu al'amarin nan yana matu'kar bani mamaki da d'aure min kai, ya ya za ayi fati ta iya kashe mutum? idan munce ba ita takashe shi ba wa ne yakashe shi? alhalin da Ita sai shi a gidan d'akin a rufe da sakata taciki. Meyasa fati takashe Dr. khalifa me yayi mata? Meye iyayen khalifa basu yimana ba? shi kansa khalifan meye bai yi mana ba? Ace fati tarasa tukuicin dazata saawa wad'an nan bayin Allah saida wannan mummunan aikin? " Goggo Abu tace "malam ka yarda fati ita takashe Dr. khalifa? Yace "to zainabu idn a ita bace waye? daga ita sai shi a d'aki yashiga yarufe 'kofa shi zai kashe kansa ne zainabu? " Tayi shiru na lokaci mai tsawo, daga bisani tajinjina kai tace "ko shakka bbu acikin wannan al'amari akwai rikitar da 'kwa'kwalwa sannan duk wanda yayi wannan aikin wanda yasan sirrin gidan ne, tabbas fati ba ita takashe dr. khalifa ba don ba ta da dalilin kashe shi ko tanada dalilin kashe shi ba ta da 'karfin halin dazata aikata wannan mummunan aikin, saboda zuciyarta tanada sau'ki akan al'amura, Allah kad'ai yasan yadda al'amarin nan yakasance. " Cikin sanyin murya malam yace "Zainabu nima abinda yake damuna knan kowa ma haka yake fad'a su kansu iyayan khalifa haka suke cewa basu yarda fati takashe shi ba, to amma meyasa ba za tayi magana akotu ba idan akaci gaba da tafiya a wannan hali za asamu mafita ? Tunda ba ita bace tayi magana mana " Goggo tace "wannan shi ne abinda yadamu kowa ma ba kai kad'ai ba malam. " ************************************ Kasancewar mahaifin marigayi Dr. khalifa babban mutum,d'aya daga cikin masu fad'a aji a cikin gwamnatin garin yabasu damar ganin fatima cikin isashen lokaci batare da tsayawar 'yan sanda ba, ko kuma ankwa. Alhaji Muhammadu Nazif mahaifin marigayi Dr. khalifa da hajiya maijidda mahaifiyarsa suna zaune a wani babban d'aki da aka 'kawata da kujeru, Malam musa da goggi suna zaune gefensu sai babban wansu fatima dakuma ummi da Barrister Nuraddeen, fatima na tsakiyarsu kanta a 'kasa ba kuka takeba su d'in ne baki d'ayansu ke sharar 'kwalla sakamakon matsanancin tausayi da bayanin datake furtawa yabasu Alhaji muhammad yace "Fatima abinda nakeso kigane shi ne dukkanmu nan mun san ba ke kika kashe Dr. khalifa ba sbda kamar wanda zaiyi kisan kai ya fita daban, ko da auren dole akai maki dashi ba za ki iya kashe shi ba balletana anyi auran nan ne da amincewarki, ke yarinya ce mai biyayya ga iyayenki, wadda kike zaune dakowa lfya kowa na yabon kyawawan halayenki tayaya za ayi Muyarda kin kashe Dr. khalifa. Ki bud'e bakinki fatima nan ba kotu bane mu ba lauyoyi bane mu iyayenki né duk duniya ba wanda kike dashi wadanda suka fimu idan rufin asiri ne ba rufin asirin dayafi na Allah, ba wanda zai rufa miki asiri bayan mu, kigaya mana saurin lamari waya kashe Dr khalifa ?? Falon yayi tsit kamar ba kowa sai 'karar A. C ko motsi fati batayi ba ballantana tabasu amsa, malam yace "fati dame muke magana kigaya mana yadda akayi idanma ke kika kashe khalifa ya ya za muyi dake ? khalifa dai ya mutu kuma ba zai dawo ba, fad'a mana gaskiya shi yafi dacewa, kullum hankalinmu a tashe yake fati ba mu da sukuni idan mun kwanta don muyi bacci bacci ba ya yiwuwa, abinci ba ya ciyuwa, muna cikin matsananciyar damuwa ,bansan dawani ido zan kalli iyayan khalifa ba, bansan da wanne ido zan cigaba da kallon 'yan uwansa ba damutanan unguwa, ba wani abu ne ma ba fatima shirun dakikayi har yau baka fad'i Wata magana wadda za a kama ba akan maganar nan kin mana adalci, dukkan 'yan uwansa da masoyanki kowa yana cikin damuwa. " "Ni na kashe shi baba. " Akayi tsit kowa yazuba mata ido, maijidda kallonta kawai take ta yi tagumi d'ansu da suke mutuwar so khalifa ta sake rushewa da kuka, Goggo Abu tace "shikenan tunda kince ke kika kashe shi to lallai ne kidaina wahalar da mutane idan anje kotu kifad'i dalilin dayasa kika kashe shi, kin san ba wai kice ke kika kashe shi kiyi shiru ba dole ne kifad'i abinda yasa kika kashe shi. Ummi tari'ke hannun goggo tazaunar da ita tace "goggo me mye amfaninki yi hushi da fati alhalin kowa anan ya san takura matan da akayi da maganar nan yasa tace Ita takashe shin to haka idan ma akaje kotun aka takura Mata abin da za tace knan 'karshe idan tace ita takashe shin dole tayi shiru tunda ba ta da dalilin dazata fad'a wanda yasa takashe shi. " Goggo tace "shikenan ummi haka za muyi tazama cikin damuwa tunda ba ita takashe shi ba idan anje kotu ta fad'i Iya abinda tasani mana. " Fatima tana kuka tace "kiyi ha'kuri goggi ba'kin cikin damuwar danasa ku ya fi damuna fiye dakowa sai dai ba yadda zanyi, goggo ba zan iya cewa ba ni nakashe Dr. khalifa ba sbda gaba d'aya bayanan sun tabbatar dacewa ni nakashe shi." Kuyi ha'kuri shirun danayi a kotu wannan shi ne abin da yafi damuwa na, idan nace zanyi magana bansan abinda zan fad'a ba 'karshe dai na san duk abinda shirun na wa zai haifar bai wuce a yanke min hukuncin wanda yayi kisan kai bane a kashe ni. To dama abinda nake jira knan, ni kam rayuwa ta 'kare a guna sai dai sai dai jiran lokaci ko ba'a kasheni ba ba'kin cikin halinda iyayena kuka shiga a sanadiya ta da ba'kin cikin rashin mijina shi zaisa zuciyata tabuga in mutu ba zan iya cigaba da rayuwa ba shi yasa ba na bu'katar taimako tako wani fuskar lauya don ku'butarwa idan akwai abinda nafi bu'kata bai wuce addu'a
Chapter 2 · 0% Book details