← Book details A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 50

Sashe 46

A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya fara ba ni tsoro. Malam yace "kira min ita. Ta kwalawa fatima kira tafito a sanyaye ta tsuguna a gefe yace "Haba fatima wannan kukan da kike yana nuna cewa tamkar ba ki ki yarda da kaddara bane shi duk abinda Allah ya hukuntawa bawansa va makawa sai ya faru, godiya ya kamata muyi wa Allah daya takaita mana al'amarin ya tsaya a haka, addu'ar da muke yi ce tayi tasiri da karshen al'amarin yazo, ko meye na tsananta damuwa, tunda kika fito daga kurkuku kike kuka kin ki cin abinci isashe, kin ki magana kin daina barci isashe to yaya kike son mi miki ? Fatima tayi ta yi tahadiyi kukan dake makale a idanunta ta kasa ta dora kanta a guiwarta hawaye suka dinga ambaliya a fuskarta, tace "kuyi hakuri baba wallahi ina jin ciwon damuwarku sakamakon damuwar da nake ciki wadda tayi sanadin damuwarku ban san yadda zanyi indaina kuka ba tabbas da na daina amma ba yadda zanyi nima ban san lokacin da nake kukan ba, zuciyata ce ba za ta iya jurewa abubuwan dasuka faru ba, ina cikin bakin ciki da damuwar abinda ummi tayi min nakasa sabawa da damuwar rashin khalifa, ummi bata yi min adalci ba da tasa aka kashe khalifa na san tana sonsa amma ita tanuna min ta hakura dashi ta gaya min cewa idan bai aureta ba kashe zhi za tayi da..... Malam ya katseta yace "Fatima khalifa ya rsu kuma ba zai taba dawowa ba har abada, tunda aka halicci duniya bbu wanda yataba dawowa bayan ya mutu haka khalifa ma ba zai dawoba, kin g kuwa idan hakane babu amfanin aci gaba da tattaunawa da maganar, zai fi kyau miyi hakuri, wannan al'amarin daya faru mu barshi a matsayin kaddara, Dr. khalifa babu abunda za muyi masa illa addu'a, Allah yaji kansa yakai rahama kabarin sa, kuka da zaman damuwa ba zai sa yadawo ba kuma ba zai goge abin da ummi tayi ba, da ace zai goge ko yadawo mana da khalifa da sai ai tayi, kiyi hakuri Allah yabaki wani mijin. ***** Tun a lokacin da kotu tagama yanke hukunci ummi tafadi bata kara sanin inda kanta yake ba, a bisa dole aka kaita asibiti tun tana numfashi har ya kaance ba ta iya numfashi da kanta sai da taimakon oxygen. Kowa sai Allah wadai abinda ta aikata akeyi tare da mamai mai tsanani, abinda yafi zama abin mamaki shi ne yadda ummi ta tayar da hankalin ta bayan mutuwar khalifa, ta fi kowa nuna damuwarta akan mutuwar ta sa, tunda aka binne dr. khalifa ummi take kuka ta rasa sukuni, kullum ckin zirga zirgar masu taimakon ta don fidda fatima daga zargi tare da binciko wanda yayi wa khalifa kisan gilla, abin mamaki wai itace ummul haba isin kisan, wannan shi ne a na zatom wuta a makera sai ga ta a msaka. Hakika fatima ta ba ma kowa mamaki ta bar ma mutane abin tattaunawa kowa na fadin albarkacin bakinsa ciki dai har da iyayan ita kanta ummin ballantana wadanda suka haifi khalifa, mama ita ke tare da ummi kullum tun kashe dr. khalifa har yau ita tafi kowa sanin damuwar da ummi ke ciki da irin kukan da takeyi a lokuta da dama ita maman ce ke lallashin ummi amma ckin wani irin yanayi ya bayyana cewa ummi ce ta kashe wanda take kokawa mutuwarsa kukan da batayi ba a lokacin da mahaifin ta yarasu, abin tambayar anan shi ne shin me yasa ummi take kukan mutuwar khalifa ? bayan ita takashe shi, sbda bata son rayuwarsa a doron kasa a bisa gurguwar hujja wai don ta rasa shi kowa ma sai dai yarasa idan akace don ta yaudari mutane take wannan kuka tana zargin daman asirin ta zai tonu ne, kokuma ta yi abin ne don ya dameta, shiyasa take kokawa kanta don ta san ta yi babban kuskure da ganganci a rayuwarta. To koma dai meye Allah kadai yasan dalilin kukan ummi bayan kisan datasa aka yiwa dr. khalifa da kanta. Ga ta nan dai a bisa gadon asibiti batasan inda kanta yake ba, karkashin kulawan jami'an tsaro, likitoci sun bada sakamakon binciken dasukayi akan ummi cewa damuwa tasa tashiga wannan halin, akwai yiwuwar tadawo normal akwai yiwuwar tarasa ranta, sbda tsananin damuwar datake ciki yayi yawa. Mahaifiyarta hajiya hauwa ce me jinyarta, hankalinta a tashe sosai yake sbda yadda ake yayata labarin a kafafen yada labarai na jihar har da makota, tayi kuka ta yi kuka har ta ba uku lada, ba a barin kowa ganin ummi sai dai tasa ummin a gaba tana kuka, tunda aka kawo ummi bata taba farkawa ba, numfashinta yahau ya sauka sai dai wani lokacin tana motsawa kamar za ta farka sai kuma tacigaba da barcin da in barda ana ganin numfashinta sai kace ta mutu ,kunyar mutane yasa hajiya hauwa ba ta iya fita ko ina batasan yadda za ayi ta iya hada ido da iyayan khalifa ba, dansu kwaya daya ummi ta yi sanadiyar barinsa duniya sbda wani hujjarta mara tushe ballantana makama. Tuni dai yan sanda sun sami nasarar chafke matashin nan me suna yaya wanda ya tabbatar shi yakashe dr. khalifa da hannunsa a bisa umarnin ummi, bai wahalar da shari'a ba ya amsa laifin sa har yayi magana da yan jaridu cewa ai dama kawo kansa hukuma ne kawai bai yi ba amma zaman jiran kamu yake tunda shi da kansa ya bayyanawa duniya ta yadda al'amarin yakasance kuma yabari aka ga fuskarsa to ai ya yi talla da laifinsa knan. A gdansu khalifa abin ya zamo tamkar na jajantawa yadda jama'a suka dinga ta zuwa bayan 'yan jaridu dake zuwa neman labari, Abba na iya magana da 'yan jarida ita kam mama wannan al'amari ya dawo mata da mutuwar khalifa sabo fil a zuciyarta, tayi kuka ta yi kuka kukan da bata taba irinsa ba a rayuwarta, jama'a na bata hakuri tana fadin, "ku kyaleni in yi kuka abin kukan ne ya sa mun, ummi ta cuci kanta me yasa ta hau dokin zuciya. Wasa wasa lamarin mama tadaina barci tsabar takaici ne fal a zuciyarta, dan na su kwara daya shi ne don masifa sai da aka salwantar. Wannan daran ma zama tayi daram a dakin abba tazuba tagumi tana kallonsa yana barci ita kuwa ta kasa tayi juyi ta yi juyin shiru, ta gaji ta tashi tazauna hawaye wani na bin wani, tadunga tuno yadda al'amrin yakasance bayanmutuwar khalifa. A DAREN FARKO 39 UMMI takan zauna tana kuka kamar ranta zai fita, watarana mama ta isketa a zau? e a harabar gdan tana sana'ar ta ta, mama tace "ummi ya ya kika fito nan kina kuka? kowa yana kallonki duk kukan na ki ya wuce ckin gida sai kinzo waje. Ummi tace "mama wai ba ni da dalilin kuka ne? duk wanda yashigo gdan nan abin mamaki ne don ya ganni ina kuka? Wallahi mama tun daga ranar da aka sa khalifa a kabari har yau har nima in mutu ba zan daina kuka ba. Mama tace "haba ummi a matsayimmu na musulmi dole mu dogara ga Allah a bisa kaddarar da Allah yadora mana, ni ce fa na haifi khalifa wa ya fini sanin ciwon sa? a cikina ya rayu nayi nakudarsa na raine shi, bbu wanda zai nuna min son khalifa tunda na hakura na karbi kaddara ya dace kema kiyi hakuri. Ummi tadago jajayen idanunta tadubi mama tace "na san da haka mama amma kin san wani abu daya, kuna kukan rashin khalifa ne don ku kuka haife shi nikuwa kukan danake daban ne da zan iya bayyana miki wani gagarumin sirrin dake zuciyata da daga yau na san ba za ki kara cewa indaina kuka ba mama. A wan? lokacin da ummi ta fadwa mama wannan magana babu abunda tasa a ranta face sirrin da ummi ke nufi bai wuce na soyayyar da take wa khalifa ba. Abba dake ta barci yamike zaune kamar an tashe shi ya zubawa mama ido yace "maijidda wanan tunanin zai ci gaba da hanaki barci a kowane dare idan har ba za kiyi hakuri ba. Mama tafashe da kuka tace "Alhaji ta yaya tunani da damuwa za su fita daga xuciyata, wane irin bakin ciki ne wannan? Yace "kiyi hakuri Allah ne yakaddara kwanan khalifa ya kare shiyasa suka samu nasarar kashe shi, kuma da sukayi hakan meye meye ribar da suka samu banda faduwa, tunda aka kai khalifa kabari ummi bata sake samun natsuwa ba babu abunda yaja mata hakan face hakki, haka shima wanda tasa yayi kisan hakki ne yasa ya tonawa kansa asiri da kansa. To kinga lah za muyi wa godiya muyiwa khalifa addu'a . ***** Jiddah ce tadaga labulen dakin inna tare da sallama, inna ta fadada fara'arta tace "maijidda ke ce tafe da yamman nan, daga ina? zauna ga kujera nan. Bayan sun gaisa tace ina fati;a? Inna tace "Tana daki shiga. Ganin fati a kwance yasa tabata rai tace "wai don Allah fatima sai yaushe za ki kwantar da hankalin ki ki dinga walwala? dubi yadda kika rame kika yi duhu kullum idanuwan ki ckin zubar hawaye har sun zama jajaye fati me yai zafi haka? Fatima tamike zaune tace "jiddah duk wadannan abubuwan dakuke ganin laifina da rashin dauriya na kune baku san ina dauriya akan su ba, jiddah tun da nake rayuwa a duniya ban taba kwatanta so ba sai akan khalifa, ko da cewa a baya na yi niyyar auran musbahu na ami? ce ne sbda da darajar iyayena amma ko sau daya ban taba jin digon soyayyarsa a zuciyata ba, ni kadai nasan asarar dana tafka wadda ba za ta taba mayar da ko da kwatankwacin mijina ba ballantana fa daidai dashi . Jidda tadafa mata kafada tace "kiyi hakuri yadda Allah yabaki khalifa ya amsa abinsa haka zai musanya miki da wanda zuciyarki za taso, lamarin na ubangiji ne babu abunda zai fi karfinsa in dai bawa zai dogara dashi to ya isar masa. Fati tace "jidda har ban san kalaman da zan yi amfani dasu gun gode miki ba, kin yi namijin kokari a gareni Allah yayi miki sakayya da mafificin alherin sa na duniya da lahira. Jidda tace "fatima godiyar nan
Chapter 46 · 0% Book details