← Book details A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 50

Sashe 15

A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ries : A DAREN FARKO 11 anisa tafiddo ido tace "to momi me ya hana yafara auranki har sai da ya auri su hajiya da mama? Momi tayi murmushi tare da girgiza kai tace "Anisa tun ina 'yar shekara goma sha daya mahaifinki yake so na, so ba na wasa ba tun muna ganin d wasa yake har kowa ya amince so yake min na gas*iya,yadinga hidima dani, duk abinda yasami niyake ba mawa, hr na kammala secondary dina lokacin aurena ya zo knan ba na kula kowa. Lokacin daya tuntubi babana da mganar aurenmu lokacin na yi candy sai yace ydaka ta masa sai ya yi shawara da 'yan uwansa, hnklin abbanku yatshi yanuna min damuwarsa akan haka nace yayi hakuri na san babana bazai ba mu matsala ba. Ahe kuwa matsala na tare damu domin babana biris yayi har takai ga ya kira abbanki yace yadaina zuwa guna dan kuwa ya yi min miji,munga tashin hankali abban ki Ibrahim a wannan rana domin kuka da hawaye yadi? ga yi yana rokin abbana yayi hakuri yarufa mai asiri kada yacuce shi da chan ba a hana shi ba sai yanzun, ba afi sati ba babana yadaura min aure dawani d'an d'an uwansa wanda yace shi yzaba min a matsayin miji. Wannan abu yajefa abban*u cikin matsanancin tashin hnkli domin kuwa ba karamin so yake min ba kowa ya san da wannan. Hakan yasa yan unguwa akayi ta zagin babana ana cewa bai kyauta ba anci amanar ibrahim, wannan ne dalilin dayasa mahaifiyar ibrahim tayi fushi tazo har gida tana gayawa babana bakaken maganganu yace da ita ai ba maryam ce kadai diya mace a duniya ba, bai ba wa ibrahim diyarsa ba ai ba wani yahaifa masa ita ba, idan anyi hushi ta aurawa ibrahim mata biyu koma hudu a rana daya shi ne zai tabbatar ita mai zuciya ce. Ai kuwa abinda yafaru knan, hajiyar ibrahim ta nemo mai 'ya'yan aminanta biyu itace hajiya hauwa uwar gidan abbanku ta yanzu da hajiya hafsa dakike ce ma mama. Ibrahim yayi namijin kokarin ba wa mahaifiyarsa hadin kai dan kada yakunya ta ta a idon duniya ganin walakancin da akayi mai a kaina,ya amince da auran hauwa da hafsa wadanda aka daura auransu rana daya aka fara kai hauwagdan da hajiyar ta sa tagina mai daga bisani bayan sati daya aka kai hafsa ,yayin da ni kuma bayan wata daya da daurin aurena da Aminu aka kaini gdan iyaynsa dake bayan layinmu. Na yi kuka na yi bakin ciki mara misaltuwa sbda ko ido ba na sn in buda in ga Aminu. Sai daga baya zance yabayyana cewa mahaifin Aminu ne yake bin babana wasu kudade masu yawan gaske yabukaci yabashi abinsa ba shi dashi, mahaifin aminu yace "tunda lokacin damuka yi za kabiya ya yi kuma babu to sai dai kabaiwa Aliyu auran maryam in ba haka ba kuwa zaiyi kararshi ne kuma nan take dole yabiya sa kudinsa, yace wadannan kudi in dai yabada maryama to sune a matsayin kudin aure da kayan lefe, sadaki kawai zai biya a daura aure, hnklin babana yatashi sosai sbda ya san dai da kunya yahana ibrahim auran maryam lokaci daya yabawa Aminu bayan lokaci mai tsawo ibrahim yadeba yana hidima da maryam tabbas ya san sai duniya ta zageshi, yayi duk tunanin dazaiyi dan yasamu mafita bai samu ba, kudi kuma bai da hanyarsu, hakan yasa yarufe idonsa yana takaici yaba Aminu aurena, lokacin daya ga damuwar goggona ya yawaita ne yasa yagaya mata yadda akayi shi ne nikuma tagaya min. Hakan danaji yasa zuciyata tadan sosu tadamu na tausayawa babana domin ko yaushe tunanina shi ne yadda babana ke son ibrahim meyasa yahana shi aurena rana tsaka ,bayan babana mutumun kirki ne ba mutum ne mai kwadayin abun duniya ba. : Shekarata biyu a gdan Aminu kowatan bata ban taba yi ba, shi da mahaifiyarsa suka shiga min walakanci suna cewa ba na son Aminu shiyasa naki yarda in haihu, ni kam ina iya kokari na duk da ba son Aminu nake ba ina mai biyayyaya shikuma yana wahalar dani kasancewar ba wani mutumin kirki ne sosai ba halayyarsa ba masu kyau bane. Watarana ina kwance a dakina yace dani "in fita inje gdanmu ya sakeni ba zai iya cigaba da zama dani ba, ba ni da wani amfani sai inci inyi kashi, natafi gda na fadawa babana daya tuntubi mahaifin Aminu kan maganar sai yakama fada yana cewa kar a gaya mai zancen banza mana maryama ce tahura wa Aminu wuta sai ya saketa gar da yi masa gori cewa ita ba shi takeso ba kuma tunda an yi masa haka kudinsa dinnan dai sai an biyashi tunda baiga amfanin auran maryama ga aminu ba, babana yace bai isa ba tunda dai yakafa sharadi kuma anyi auran a bisa sharadin daya kafa zancen kudi kuwa babu shi sai dai in kara zaiyi. Momi tadan yi shiru tana kallon fuskar anisa wadda tazuba mata ido tana mamakin labarin da take ba ta tace,"to momi yaya akayi har kika auri babana? Momi tace "Anisa hakika abbanku ya san darajar soyayya kuma ya mutunta kaunar dake tsakanina dashi; ahaifin Aminu yayi karar babana yace sai ya biyashi kudinsa tunda dai diyarsa maryam ta ki zama da Aminu, kiri kiri alkalin nan yagoyi bayan mahaifin Aminu bayan ni da baba na mun bayyana a kotu yadda abubuwa suka kasance wai sai alkalin nan yace sai na kawo shaidar mutum daya kwakkwara wanda zai min shaidar cewa Aminu ne yasake ni da kansa ba ni nace yasakeni ba, nace banda shaida sai Allah dan shi ne masanin dukkan abubuwan dasuka faru,, alkali yace dole sai babana ya nemo kudin Aminu ya biyashi lamarin daya tayar da hnklin kowa a gdanmu har kuka sai da babana yayi, kwasam Allah mai iko bayan kwana biyu dayin hakan sai ga abbanku ibrahim ya zo gun babana yakawo mai kudin da sukafi wanda baban Aminu yake binsa, mamaki yakamashi da kunya yarasa abinda zai ce, Ibrahim yace karka damu baba ni fa kaunar dana kewa maryam Allah kadai yasan iyakarta, duk abinda yashafe ni ya shafeku, Allah ne bai kaddara itace matata tafarko ba shiyasa abubuwan dasuka faru suka faru. Babana yabiya baban Aminu kudinsa kuma yace bai yafe masa ba, ina kammala idda aka daura aurena da Ibrahim, ban cika shekara daya ba na haifeki a cikin shekarata ta uku a gidan nan na haifi kaninki mahmud, kuma a wannan shekarar ne Allah yadaukaka arzikin mahaifinku wanda izuwa yanzu shi da kansa bai san abinda ya mallaka ba. Har yanzu iyayena ba su da abin Kauna kamar ibrahim kamar yadda nima ban iya hada shi da kowa, abinda nakeso inkaiki gareshi guda daya ne Anisa mahaifinki dani kaina mun san martabar soyayya muna mutunta ta. Mahaifinki ya nuna min kaunar da ban taba jin wani da namiji dayai wa mace halacci irin wadda ya min ba ko da kuwa a labari, shi yasa ban wasa da duk abinda yasha fe shi. Duk da kasancewarsa adali a tsakanin matansa amma kowa ya san soyayyar dayake nunamin ba karama bace shiyasa hajiya da mama suka tsaneni to amma ba su da ikon komi akaina sbda sanin halayyarsa. Wlh Anisa ni kadai ce matar da zan tunkareshi da kowace irin bukata yayi min ko baida ra'ayi don hka zan umarce shi da ya shirya miki tfya xuwa kasar germany don ki karasa karatun ki a chan. Anisa ina rokon ki kiji tsoron Allah a wannan tafiya da zakiyi kada kija min bacin rai,duk rintsi duk wuya kada ki lalata rayuwarki idan ban gani ba Allah ya gani ki min alkawarin tsare mutuncin kanki. Anisa tace "mom na maki wannan alkawari insha Allahu. Kowa yayi mamakin batun tafiyar anisa har kasar germany da sunan karatu tun da babanta dai ba shi da wannan ra'ayin ko babban dansa da hajiya hauwa tafara haifa anan kasar yake karatunsa na jami'a hakan yasa aka dauki hassada aka daura akan anisa amma dan ita abin bai dameta ba cikar burinta ne kawai damuwarta har a ranar da za tabar gida nigeria zuwa jamus batun mominta guda daya ne. "Anisa kiji tsoron Allah kada ki zubar da mutuncin ki baki da takamar data wuce budurcinki a gun mijin da za ki aura duk abinda zai rudeki kiji tsoron Allah kada ki biye masa bbu inda zai kaiki face ga nadama wadda zai sa kiyi ta kunkan da ba ki da ranar dazaki daina, duk abinda d'a namiji zai aikata a rayuwarsa ado ne mace ce a cikin hadari da bakin ciki idan batayi taka tsan tsan da rayuwarta ba. A cikin jirgin anisa ta hada kanta da guiwa ne tana tunanin wadannan maganganun na mahaifiyarta wadanda suka tsaya mata a rai, hawaye suka dinga zuba a idonta wani na bin wani, taji tausayin kanta da iyayan ta jikinta yayi sanyi sosai batasan yadda rayuwarta za takasance a wannan kasa ba. *********** Jiddah zaria Babban magana wai namiji dasuna Hajara, anya kuwa Anisa za ta iya cika wannan alkawari na mahaifiyarta???? ni ma dai jiki na ya yi sanyi amma dai ga mai fili ga mai doki........ karku gaji dai kukasance kuna biye dani a baya ganin yadda za takaya.... Ni ce dai 'yar mutan zazzau. Hawwa umar. a.k.a jiddah zaria. A DAREN FARKO 12 Kamshin da khalifa yaji ya halarci hancinsa yasa yamike xaune yana kallon Anisa, tace "ga abincin nan tashi kaci kayi wanka kayi sallah. Ya fubi abincin cike da gamsuwa yace "amma fa nagode Anisa kin fara ragemin damuwata zauna kigaya min dalilin zuwanki garin nan. Tayi murmushi tace "karatu nazo yi nima, rakiya nayo wa wata kawata za tayi tafiya kamar daga sama na ganka. Yajinjina kai yace "na godewa Allah daya kawoki daidai lokacin da zama ya kamani a nan. Farin ciki ya mamaye zuciyarta ta fara jiyo kamshin nasara a cikin muradinta duk da cewa ta san akwai aiki ja a gabanta. ******** Ruwan sama akayi kamar da bakin kwarya tun safe har gab da za ayi sallar azahar sannan yadauke, garin kano yadauki sanyi mai dadi kasancewarba sanyin takurawa jikin bil'adama ba. fatima tagama shiryawa cikin atamfarta maroon mai adon ja da fari, ta yi mata kyau sosai tadauki
Chapter 15 · 0% Book details