Sashe 12
A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gaba dashi . Da sassafe ummi tariga kowa tashi agdan tayi wanka tatsala ado za tashiga kitchen sa'ar da tayi ita gwanar iya girki ce da kwalliya ta yi cos din wadannan abubuwa guda biyu a gun hajiyarta. Mama tafito wurin karfe bakwai d rabi tana shirin hadawa abban kayan tea sbda fitar da zaiyi dawuri, sai taji kamshin girki ya game dakin. tashiga kitchen suka hada ido da ummi tarike baki tana murmushi tace 'oh sannu da himma ummi irin wannan kamshi hka? Ummi tatsuguna tana murmushi tagaida tace "ummi ke za kidinga girki a gdan nan, girki ba zai hanaki bacci ba a lkcn da kowa ke hutawa ko yan aikin nan a yanxu haka suna chan suna bacci idan ba abban ne zai fita da wuri ba sai karfe gomaake gama abinci sannan aci. Ummi tace "mama ai daga wannan rana dana dawo gdan nan da zama insha Allahu ruwan shayi ba za ki sake dafawa da kanki ba sai fa in ba na nan, kuma yau ma na tashi da wuri ne jin abban ya ce zai fita dawuri. Mama tagyada kai tace "ya yi kyau lallai na san za ku shirya da yayanki khalifa don yana son abinci mai dadi. Gabanta yadan fadi tayi murmushi kawai. A kwanaki shida da ummi tayi a gdan kafin tafiyarsa germany sai da tayi kokarin da khalifa yake kulata a kalla yana amsa mata gaisuwa cikin fara'a har yakan ja ta da magana a wasu lokutan. Ranar laraba da asuba ta kama tafiyar khalifa germany a daran talata bai shigo ba sai sha biyun dare yan can wurin abokansa da yamatansa da sunan sallama. Mama tana zaune a dakinta ita kadai bayan ta idar da sallar shafa'i da wutiri da casbi a hannunta, ummi tashigo da food flask a hannunta tatsuguna gaban mama tace "mama yaya khalifa ya ce amala yau yakeso da miyar kubewa ya ce a gama da wuri, na yi masa tun magriba ga shi har yanzu bai dawo ba. Mama tace "na yi zaton ma kinyi bacci dama tun dazu kina falo jiran khalifa? lallai baki san gararin khalifa ba, idan yaga dama in yazo yaci idan baiga dama ba cikinsa. Tace "mama ko dai injira in ya ce bazai iya ci va ya yi sanyi in dafa mai wani abun. Mama tace "habadae sai kace kin zamo baiwarsa, tashi ki mayar da abincin falo kitafi ki kwanta. Ummi tadawo da flask falo maimakon taje takwanta sai ta zauna tayi tagumi a daidai wannan lokaci shi khalifa na daki tare da ramcy a yau ta kare mai gida taviyo shi har gdan ubansa, kamar yadda tasha gaya masa ta ce "duk abinda zai faru in dai a kaina ne ta dauka ba gudu ba ja da baya. Khalifa ya rasa yadda zaiyi da ramcy yau ta rikice msa yini guda yayi a gidanta tun safe har dare bata barshi ya motsa ba amma da dare yayi bai san yaya akayi ba har ta biyo shi a motarta ba, sbda shi kansa a yau ckin natsuwa yake sbda alhinin rabuwa da gda ba wasa bane tun safe jikinsa yake a sanyaye dan hka yinin dayayi a gdanta ma ba abinda ya iya aikatawa sai kwanciya tana kallonsa kawai. Sa'ar da yayi shi ne lokacin da zata biyo shi ta yi shigar mutumci ta sa dogon hijjabi mai hannu har kasa yana shiga da motarsa itama tasa tata motar mai gadi zai mata hayaniya kasancewar dare yayi kuma bai taba ganin motar a gdan ba khalifa yace yakyaleta bakuwarsa ce. Suna shiga daki yarufe ta da bala'i yace "ni za ki walakanta haka? baki san uwata da ubana suna gdannan ba? me kike son a daukeni dakika biyoni, toh abinda xan gaya miki shi ne na barki kin shigo nan dakinnan ne don kar inyi hayaniya dake a waje wanda bai san abinda ake ciki ma ba yasani, ki tashi kikoma inda kika fito... Sai tayi wuf takamoshi tarungumeshi kam kam tana masa kiss, wannan ne dalilin dayasa khalifa ba ya hada ramcy da wata dan wata hanya ta kan shawo kan namiji ta sani komi fushin da yayi kuwa, tace "khalifa me na rasa ne? meye mahaifina bazai iya mallaka min ba a rayuwa? sai kai kai ne kadai mahaifina bai da ikon yamallaka min sbda kudi bazai siye ka ba to yaya zanyi da raina khalifa? Jikin khalifa yayi sanyi kwarai da gaske bai taba tausayin wata diya mace irin yau ba, musamman yadda take me kuka da hawaye. Dai dai wannan lokaci ummi ta gaji da zama a falo tana takaicin ace khalifa bai ci wannan abincin ba yadda tzauna ta tsara shi hakan yasa ta kasa juriyar tafiya ta kwanta ta zuba abincin ta jera a plate tanufi dakinsa tunaninta shi ne tabar masa a dakin nasa tunda tana da makullin dakin shi da kansa yabata sbda yanajin dadin yadda take gyara masa komi a dakin a tsaftace. Tana isa kofar dakin tasa makulli ta bude, abinda tagani yasa gabanta mugun fadi, yaya khalifa rungumeda mce tana sanye da hijjabinta, bayan Runguma ba wani mummunan abu da ummi tagani amma duk da haka sai da abincin hannunta yasubuce ya tarwatse a gun takoma ckin gida da gudu tana haki, wani abin takaicin tahadu da mama a falo za ta sashen abba. Gaban mama yafadi tatsare ummi da tambaya, hnklin ummi yatashi tarasa abinda za tace wani karya za tawa mama, mama tawuce tabarta jiki na tsuma. Khalifa ture ramcy yayi yace shkan hnklinki ya kwanta kin tona min asiria gdan mu ko? Za tayi magana yadaka mata tsawa yace, "kawai kifita idan kikaci gaba da tsayuwa anan komi zai iya faruwa dake tunda asirina ya tonu ba na fargabar komi dn haka kama gabanki. ******** Karfwme dayan dare tayi khalifa ya kasa runtsawa, ganin da umi tai masa rungume da mace ya tayar mai da hnkli matuka bai san wani irin kallo yarinyar za ta ci Gaba da yi masa ba a yadda take ba shi girma shknan ta daina ganinsa da kima bayan wannan za ta iya gayawa mama daga nan maman za ta iyasa wa ai masa aure da diyar da maman ke son ya aura itace 'yar aminiyarta mai suna ummi. Yamike cikin tsananin mutuwar jiki cikin sanda ya kwankwasa dakin ummi a hnkli ya san dai da wahala su abba su ji. ummi tamike ckin tsoro tace waye? A hankali yace ni ne khalifa, dasauri tamike ko kayan bacci yau bata sa ba, kayan jikinta ne hijjabin datayi sallah, ta tsaya jikin bango tana kallonsa, cikin kakkausar murya ta jaruman maza yatsare ta da idanunsa. A wannn lokaci hnkalin ummi yai matukar tashi yace "ummi Murya na rawa ta amsa yace me ya kaiki dakina dazun? Tace abinci kawai naje kai maka na ga ka jima baka dawo ba ni kuma ba na so yakasance baka ci abinci ba sbda tun azahar na shiga kitchen nahda maka shi. Ya danna mata harra kamar zai shaketa yace 'damaa a dakina nasaba cin abincin? Sai dai na zo ne dan in gargadeki dan kisani kada wani yaji kinga wata mace a dakina. Idan kuma naji ko da wasa wani ya furta ta ko shakka babu na san ke kika fada, saiki saurari matakin dazan dauka wanda ba zai taba yimiki dadi ba. Sannan maganar soyayya tsakani na dake bbu, ni ba sa'anki bane, idan naji kince da mama ko abba ko wani cewa kina sona xa kisha mamakin matakin dazan dauka akanki, idan wannan ce gulmar da kika dakko kikazo gdan nan da ita sbda ni to kikoma don ba xa kiyi nasara ba, yaja tsaki cikin hushi yafice daga dakin. ******* Tabdijam su duka biyun bbu wanda yayi bacci a wannan dare, abinda yadaga hnkalin kowa daban kowa tunaninsa daban. Bayan fitar khalifa ummi tatashi ckin tashin hnkali tayi kuka kamar ranta zai fita tadubi agogo karfe biyu da minti ashirin bata ga nisan dare ba takitra mahaifiyr ta a wannan dare tana kuka wayar a kashe, hajiya sauda itama a kashe, takira babbar aminiyarta jiddh bata kashe waya ba, jiddah tadauka a figice tana fadin "inalillahi wa inna ilaihir raji'un. tadaga wayar abinda tace shi ne "ummi waye yamutu? Musanman kukan dataji ummin na rusawa kamar ranta zai fita, tace ni ce na mutu jiddah mesa kuka ban kwarin guiwar in so wanda ba zai so ni ba? Jiddah tayi ajiyar zuciya tace "ummi yau kwananki nawa a gdansu khalifa? Tace "shidda. Ta j tsaki tace "gaya min abinda yasa kika kira kanki matacciya gashi kina raye. Cikin sanyin murya ummi tabayyanawa jidda abubuwan dasuka fru a wannan daren, jiddah tace "kin ban kunya da hushi ummi kuma kin kashe kanki a wurin khalifa. jiddah tace "ummi ita nasara tare suj tafiya da hakuri, tunda khalifa tafiya zaiyi abu daya yarage miki shi ne kiyi kokarin yin abinda zai matukar ba shi tausayi tyadda idan yaje jamus abin zai tsaya masa a rai, . Khalifa na sanye da bakar kot ya tsuke sosai fuskar nan ba fara'a ya sha kunu, mama tana dakinta ko fita batayi ba, ummi ta bishi dasauri ta tsaya daga baya a langabar da kanta a jikin bango tana kallon khalifa yana taku dai dai. Lokacin dazai shiga motar ne ya waiwayo sai karaf kuwa suka hada ido da ummi, sai yayi cak yana kallonta bai shiga motar bazuciyarsa tashiga harba wa, ganin haka sai ummi tadaga hannu sama da nufin tana masa addu'a kuma tashiga yi masa bai bai da hannu tashiga ckin gda da gudu. Khalifa yafada mota abbansa na kusa dashi direbansu yahaya yaja motar zuciyar khalifa ba dadi abubuwa da dama suka cunkushe masa a zuciya. Tausayin ummi suka kamashi har suka isa filin jirgin saman malam Aminu kano hannunsa biyu tallafe a kumatunsa, abubuwa da dama suka tsaya mai a rai, abokansa da yammatansa ba wanda bai nunawa tsananin damuwa ba ama ba wanda yatsaya mai a rai irin ummi. Ya kwana yanajin zafinta a ransa a tunaninsa ma yarinya karama dako secondary bata gama ba tatsaya gaban namiji tace tana sonsa. Lokacin dazai shiga jirgi yarike hannun mahaifinsa yace "abba kayi min addu'a zan bar kasar nan cike da