← Book details A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 50

Sashe 8

A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ne a falon abban na cikin gida dasafe suna breakfast tare da mamansu hajiya Maijidda. Dr. khalifa ya ajiye cup din shayi yana kallon abbansa yace "abba na ji koda yaushe fa kana gaya min bbu abinda kafi bukata wanda yawuce inzauna kusa dakai in kula maka da harkokin kasuwancinka. Abba yayi murmushi yace "ina sane da wannan khalifa sai dai hakan ba zai hana in yi abinda ydace ba, ina burin kazamo likita don in gina maka babban asibiti anan kano wanda zan sadaukar dashi sbda Allah a dinga taimakawa bayin Allah wadanda ba su dashi. Yace "abba toh kasuwancin na ka fa? ba ka son in taimaka maka akansa? Yace "kada kadamu da wannan saddik ina bukatarka a kusa dani a ko da yaushe sbda abubuwa suna mini yawa sannan yaran danake dasu ba kowane yakeda amana ba, sannan ina samun matsalar rashin masu sa ido a kan abubuwa dukda kokarin danake da ganin na basu hakkokinsu gudun samun matsala irin wannan toh amma matsalata ba za tasa in ki taimakon al'umar musulmi ba, na hakura da amfanuwar da kasuwancina zaiyi dakai kaje kayi wannan karatu don ka taimakawa al'ummar musulmi 'yan 'uwanmu. Mama tace "to amma abba kafin yatafi yanada kyau yayi aure yatafi da matar ko? Dr. khalifa tadafe 'kirji tare da fiddo ido yace "aure mama? sghekaruna duka duka ashirin da biyu ina ni ina maganar aure? don Allah karki 'kara wannan maganar mama ni tun da nake ma ban ta'ba ganin wata mace da zuciyata ta ta'ba so ba, wadda har nakejin zan iya aure. Mama ta ta'be baki tana harararsa tace "kai da Allah rufe mana baki ni za kacewa ba wata mace daka taba so, duk 'yammatan dake biyoka har gidan nan ba 'yan matanka bane? kokuwa kana zaton ba ni da masaniya kan abinda kake? Yalangabar dakai yace 'Alah mama ba budurwata ko daya aciki? su duk wacce kikaga ta zo gdan nan nemana kawata ce ina nufin abokan karatu. Abba yayi murmushi yace "to ko ma dai meye za katafi germany a haka ba tare da aure ba amma idan Allah ya dawo dakai lafiya za ka yi aure insha Allahu ka fahimta ko? Kansa na kasa bai ce komi ba shi kan baya so ko zancan aure a yi masa don ba batun soyayya a gabansa ama batun kawaye wadanda ake debe kewar rayuwa dasu ai babu wadda babu. Bayan fitar khalifa abba yabata rai yana kallon mama yace "ba na son kina matsawa yaron nan kan batun aure tunda ba shi da ra'ayi har 'kwara nawa khalifan yake da za ace dole sai ya yi aure. Mama tace "Alhaji ai kaine dai bakasan abinda ke faruwa ba, dukiyar daka sakarwa yaron nan tasa yanayin abinda duk yaga damar yi masa auren shi ne abinda yafi dacewa. Ya kara tsuke fuska yace "ni fa ba na son zargi irin wannan muci gaba da dagewa da addu'ar damuke masa insha Allahu Allah zai tsare mana shi. Tace "shikenan alhaji kuma bayan haka kana sane da maganar yarinyar nan zainab tana matukar son khalifa amma 'ki'ri'kiri yake nunawa ba ya son ta ka ki yin wani abu a kan wannan maganar dakayi inason kabani goyon baya ne don ayi auransu da zainab har kunyar mahaifiyarta nakeji yadda fa yake d'angata itama 'yar gata ce mahaifiyarta na sonta kaga...... Abban yace "Don Allah kihutar da bakinki da fad'in abinda ke kanki kinsan ba zai yiwu ba. Daman na ce miki mahaifiyar zainab ba ta son ta ne, kokuwa kin ta'ba ganin wanda yahaifi d'ansa yace ba ya so? kawai dai kud'i ake nunawa da so? kinfi kowa sanin cewa ba zan ta'ba tursasawa d'ana auran matar da ba ya ra'ayi ba don muna da dangantaka da iyayanta, kamar yadda nima ba zanso a tursasawa wata d'iya ta auri khalifa ba alhali ita ba ta so. Inaso idan khalifa yatashi aure ya auri matar dayake matukar so itama tana matukar sonsa, insha Allahu zanyiwa khalifa bikinda za a jima a garin nan ba a ga biki na d'an gata irin sa ba. Farin cikina da kwanciyar hnkalina bai wuce auran soyayya bane don hka idan khalifa yanason zainab zai aureta a lokacin daya nuna yana son aure, idan kuma ba ya sonta zai auri wadda yake so ne bbu dlilin dazaisa don tana son shi ace dole sai ya aureta, hkan na nufin ita an mata adalci shi kuma an tauye masa hakki nsa knan? Tace "shknan ya wuce. A DAREN FARKO 8 Ummi d'iya ce ga Hajiya Hauwa yayar Abba wadda take bin babbar yayarsu Hajiya jummai duk da cewa kafin tasowar ummi hajiya Hauwa ba sa shiri da mama don tana cikin masu zakewa 'yan gaba gaba a kan sai abba ya yi aure tunda ita maman ba haihuwa take ba, in banda hajiya jummai datafi karfinsu ita kuma tana matukar son mama sbda kirkinta yayin dasu hajiya hauwa gani suke duk kirkin dasu jummai ke cewa tana dashi na kissa ne da munafunci don ta mallakesu su da d'an uwan tare dacewa babu abinda alhaji muhammadu ba ya musu hatta saudiya shi yakai hauwan ita da mijinta kasancewar duk cikin 'yan uwan nata ma itace ta auri mai karamin 'karfi sai dai tsananin soyayya, kayan abinci da kudi akai akai yake musu aike dukda haka hajiya hauwa ba ta gani kawai sbda ba ta son matarsa hajiya maijidda, yan biyu hajiya hauwa tafara haifa sannan tahaifi wani namijin mai suna Abdulrasheed tahaifi wasu 'yan biyun su kuma mata ummi ce d'iyarta ta biyun 'karshe inda taci sunan mahaifiyar abbansu ake cemata ummi daga ita sai dan autansu umar. Hajiya hauwa na matukar son ummi kasancewarta mai halayya irin ta ta, tun tana yar karama take abokiyar shawara gareta ,ba laifi itama tanada kyau da d'an gwargwadon abinda yasa ake dad'a ganin kyaun ummi bai wuce yanayinta ba da kuma bkin tsiwarta tsiwar kanta tan yi mata kyau, tana burge mutane da dama. Bata fiye zuwa gdan abba ba sai ana wani sha'anin sbda ba shiri take da mama ba, tanada d'abi'ar duk wanda hajiyarsu bata shiri dashi itama baza tayi shiri dashi ba, tana biyewa ra'ayi da son zuciyar hajiyarta shi yasa ra'ayinsu ya zo d'aya. Ummi na aji hud'u na secondary Allah yayiwa mahaifinsu rasuwa kuma a gun zaman makokin ne wata irin soyayya tashiga zuciyar ummi da Dr. khalifa farat d'aya a lokacin ummin shekarunta goma sha shida kacal a cikin 'yan maan ma bata ri'ka ba shi ne lokacin dasuke tasawa. Ranar da aka kwana bakwai da rasuwar suna zaune a d'akin hajiya hauwa ita da babbar aminiyarta kuma makotansu wato jidda khalifa yashigo tare da sallama fuskarsa a tsuke yake amsa musu gaisuwa yace "ina hajiya? " Jiddah tace "tana gaisawa da ba'ki a sit room d‹in baba. Yace "to idan ta fito kice mama ta ce maganar sa'kon nan zatayi mata waya yanzu dai bai samu ba ni sauri nake ba zan iya jira tafito ba. Bai saurari abinda za suce ba ya fice su ma basuyimagana ba ya ga toh dasuka hada baki suka fada lokaci guda. Bayan Fitarsa jiddah tadubi umi tana murmushi tace "Oh ni tunda nake ban taba ganin mutum mai jin kai da isa irin yaya khalifa ba ko dan yana ganin ya had'u ne. Ummi tayi ajiyar zuciya tace "lallai kam ba abinda yake sashi ta'kama wanda yawuce haduwarsa sai kuma dukiyar mahaifinsa wadda yake takama da ita kina ganin duk tsadar mota khalifa zai hauta da zarar an shigo da mota sabuwar yayi 'kasar nan komi tsadarta abbabnsa zai siya masa ya hau, kuma dan wani karin jin kai da alfahari ma ba zai yawo a mota d'aya ba sai ya jera motoci goma yana tsakiya tare da abokansa yana homa daga bisani ne surutu yayi yawa a dangi da abokan abbansa ya tsawatar masa a kan yadaina fita da motoci da yawa haka shi ne yanzu yake fita da motoci biyu ko uku. Jiddah tace "duk abinda yayi ya yi daidai don ya isa yayin, ni kam yaya khalifa yana matukar burgeni ina mai ba ki shawara ummi in har za ki iya shiga zuciyarsa kada kibari ya subuce miki. Ummi tayi ajiyar zuciya tace "jiddah kin san dai yaya khalifa kuma kinsan yadda rayuwarsa take, nima kinsan gwargwadon wayewata da fahimtarki da rayuwa kina ganin zan iya shiga xuciyarsa ina nufin kina ganin ina da nagartr da zai so ni? Jiddah tace ummi kina da kyau kuma kina da wayewa, meye zai gagareki idan kika bar wannan damar tawuce miki za kiyi nadama. Ummi ta jima tana nazari kanta na 'kasa tace kada kijefa min damuwa a zuciyata kan abinda samuwarsa gareni zaiyi wahala. Jiddah tace "idan kika sa wa zuciyarki damuwa akan samuwar khalifa gareki to lallai wahala zai zame miki, yayin da idan kika sa wa zuciyarki abu ne mai sauki mai sauki ne kada kidamu da jin kan yaya khalifa ko haduwarsa da takamarsa kina da hanyar da za ki iya mallakar zuciyarsa cikin sauki mata irinmu da ba mu da alaka ta jini tsakaninmu shi ne zai mana wahalar samuwa ke kuwa uwa daya uba daya iyayanku suke gdanku gdansu ne haka gdansu gdanku ne, kitashi tsaye ki mallaki miji na fita kunya mijin da za a iya shiga dashi ko ina a kalleku bayan kyau ga dukiya ga uwa uba ilimi ba jiya kikace min zai tafi germany karatun likita ba? Cikin sanyin murya ummi tace "jiddah na yi mamakin wannan magana ta ki sai jace kin shiga zuciyata, wlh jiddah tun kafin in mallaki hankalin kaina insan waye namiji insan menene so nake matukar so da sha'awar yaya khalifa duk sanda na ganshi nadinga kwatantashi a matsayin mijina abinda yas nakasa kusantar kaina gareshi sbda miskilancinsa kina gani ko gaisawa akayi sama sama yake amsawa, ban taba gaida khalifa ya yi min murmushi ba al'amarin har tsoro yake ba ni, amma khalifa shi ne nakema son dana tabbTar babu wani d'a namiji da zanwa ko da rabin son danake masa, tabbas a wannan rana kin fama min inda ke min 'kai'kayi a da na kwantarwa da zuciyata soyayyarsa dake raina amma yau kin tayar min da ita insha Allahu sai
Chapter 8 · 0% Book details