← Book details A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 50

Sashe 47

A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta isa na gamsu Allah shi ne abin godiya daya nufeni da in yi hakan da bai ba ni iko ba ban isa in yi ba, yanzu wata alfarma nake son ki yi min. Fati tace "ki fada jidda ko mene zan miki in dai xan iya, kin fi karfin komi a gareni. Jidda tace "sanin hakan danayi shiyasa nazo, a safiyar yau din nan ne mahaifiyar ummi taxo tana rokona in taimaka in zo in roke ki ki je asibitin da ummi ke kwance ki dubata domin ta farfado amma tana ta kuka tana rokon a kawo mata ke da iyayan dr. khalifa za ta fada maku wata maganar, dafarko nace da hajiya babu ruwana sai nagata kama kuka tana rokon in taimaketa tace wllhi jidda nima ba laifina bane ba ni da masaniya ko ta kusa ko nesa game da abinda ummi ta aikata,. Fatima ta jinjina lamarin sosai a ranta, yanzu kam a duniya ba ta da makiyin daya wuce unmi, ji tayi kamar za ta hadiyi zuciya ta mutu sbda bakin ciki me za tayi da wadda tarabata da masoyinta, kai hakika ummi ta gama cutar ta har me za ta gaya mata. Babu yadda ta iya da jidda tana ganin kimarta da yawa don haka ya amsa mata cewa za ta, ta sanar dainna da malam suka mata izinin zuwa, dogon hijjabinta me hannu da nikab tasa ravon ta da fitowa waje tun ranar da aka sallamo ta daga kurkuku, hawaye suka dinga zuba daga idonta har suka iso asibitin., a lokacin taga mama suma suka iso su biyu jidda takira hajiyar ummi a waya tace dasu sun zo tafito tashiga dasu dakin da ummin take. Duk yadda zuciyarsu ke cike da tsanar ummi da bakin ciki sai da jikinsu yai sanyi, sakamakon yadda suka ga ummi ta yi wata muguwar rama kamar an sauya ta, ta yi baki ta fita daga hayyacinta, babu wanda yazauna sun kame ne suna kallonta. Ummi ckin rawar murya hawaye wasu na bin wasu tace "Abba, mama, fatima na gode kwarai da kuka danni zuciyarku kuka zo nan, na bukaci zuwanku ne don kuga halin danake ciki kafin Allah yakarbi rayuwata, domin ni tawa ta kare ba zan kai labari ba ba kuma so nake ku tausaya min ba don ni ba abin tausayi bace, kuyi hakuri masu karatu a littafin babu page 47-51 Kwanan ummi goma sha shida a gadon asibiti karkashin kulawar lokitoci da jami'an tsaro tarasu, bayan aman jini ta hanci da baki data yini tanayi saita dinga sai tadinga zabura tana gwara kanta da bango tana ihu, "Na cuci kaina, shi ne kadai abi? da bakinta yake furtawa har tadaina numfashi, lokacin da labarin mutuwarta yazo kunnan fatima ta yi kuka har sai da zazzabi da ciwon kai suka rufeta.. ***** Wai shin masu karatu kutambayeni ina musbahu yashiga mana? ku biyoni kuji. Lokacin da musbahu ya tabbatar ya rasa fatima sai ya kaddara a ransa cewa dama ba matarsa bace, . Musbahu gdan kawun sa malam habibu yafara zuwa ya sanar dashi abinda yafaru, kawun ya ji b dadi a ransa amma ba yadda za ayi in dai mutum mai hankali ne da adalci babu yadda za ayi yayi wani zargi akan malam da inna don sun rike musbahu tsakani da Allah, Allah ne bai kaddara fati rabonsa bace. Musbahu ya shaidawa malam cewa zai tafi garin bauchi gun yayar mahaifiyarsa ne sbda yana so yayi nisa da kano a dalilin ba ya so yaga daurin auren fatima. Karfe biyar da rabi na yamma yashiga gdan goggo mairo dake ckin garin bauchi tayi mamakin ganinsa tace "ango na amarya kaine tafe? Yace "Gwoggo ina wuni mun sameku lfya. Tace "lfya kalau yashi kaje dakin au sagiru yana nan yana barci kayi wanka kayi sallan xan aiko ma da abinci idan kaci sai kazo mu gaisa sosai. Sagiru kusan sa'an musbahu ne shi ne dan goggo na biyar ya biyo mata biyu maza biyu,. Tun a ranar yafara devewa musbahu kewar damuwar dayake fama da ita, sbda mutum ne me ban dariya, da alheri ga son mutane. Musbahu ya bayyana masa abin da yarabo shi da kano, sun tausaya mai sosai ganin damuwar dayake cki yasa nan take goggo tace ga diyarta nan hafsa in dai yana son ta ta ba shi, musbahu yayi dan jim bai ce komi ba, goggo tace "ko bata yi maka bane in dai ba ka son ta babu dole. Yace "ba haka bane goggo ina tunanin yadda malam yace ya bani fatima tace ta amince sai da na saki jiki da ita nabata amanar soyayya ta sannan tace ba ta so na, dr khalifa take so shi ne ra'ayinta nikuma ra'ayin iyayanta, nayi mata uzuri cewa ba ita ta zabeni ba niyyar biyayya ga iyaye tayi . Gwoggo mairo tayi murmushi irin nasu na manya tace "musbahu duk wannan abinda yafaru kaddara ne Allah ya hukunta cewa ba matarka bace, idan xa ka lura duka kwana nawa yarafe a daura maku aure khalifan ya bayyana, da ace matarka ce ba zai bayyana ba ko ya bayyana kuma ba zaiyi tasiri a zuciyarta takalle shi da sunan so ba. Ba wai ina gaya ma hakan ne don kaso hafsa ba, in kana raayin hafsa ga ta nan in ba ka ra'ayi kayi zamanka har Allah ya baka wadda kake so. Musbahu yakara dukar da kai yace "wallahi goggo hafsa tafi karfin namiji yaki ta, in ta amince dani ma ta yi min alfarma domin ta girmi ajina. Goggo tace "karka sake fadar haka kaje gareta ku daidaita kanku, Allah yatabbatar mana da alheri. A cikin sati biyu musbahu da hafsa suka fahimci juna, yasameta yarinya mai sauki da son mutane kamar mahaifiyarta, ga ladabi da biyayya, kowa ya yi farin ckin wannan al'amari a dangin su, nan da nan aka tsaida magana babansu hafsa yace zai ba musbahu aron gda su zauna kafin su koma kano, ba wani kudi musbahu yakashe ba illa iya abinda yayo sai da goggo tai masa fada cewa daya suke dashi da hafsa a gdan nan. Bayan wata guda aka daura aure sukayi biki sosai suka kashe kudi, musbahu har mamakin gatan da suka nuna masa yake, aka gama biki lfya aka kai amarya dakinta, a ranar da zai shiga dakin ne yadinga tunanin abubuwan daya tanada zaiwa fatima a ranar da aka kai masa ita, ashe ba matarsa bace yanzu haka tana chan da angonta ta ma manta dashi shikuwa yana fama da ita a zuciyarsa. Sai da yadinga addu"a Allah yataimake shi yarabashi da tunanin fatima kada ya cutar da hafsa sbda ya lura hafsat ta yi dammarar zaman aure dagaske tare da biyayya, ckin ikon Allah yataimake shi yasamu natsuwa a zuciyarsa yamaida hankali sosai gun kyautatawa matarsa sukayi zamansu lfya kowa yana sha'awar auran na su. A DAREN FARKO 40 Kusan watanni shida knan da rasuwan dr. khalifa an dan samu cgaba a rayuwar fatima sbda ta fara rage damuwa har ta shiga wataislamiyya nakusa dasu da akeyi alhamis da juma'a, ta kuma fara tunanin komawa makaranta a halin yanzu ba ta da aminiyar da ta wuce jidda koda yaushe suna tare itama jiddan bata koma london din ba ta dawo da karatu? ta BUK tana karanta mass comm. kasancewarsu tare da jidda ya taumaka kwarai gun debewa fatima kewa sai dai har yanzu idan tatuno dr. khalifa takan yi kuka mai tsanani sbda soyayyar da take masa tayi mata yawa a zuci, shi yasa yau da jidda tazo mata da wata magana sai da taji kanta yana mata tsawa. Ta zubawa jidda iso kawai tana nazarin fuskarta bata katseta ba sai da taji tayi shiru sannan tamike zaune tace "jidda maimaita abinda kika gaya min yanzu. Jidda tabata rai tace "kina nufin baki ji abinda na gaya miki ba? "Na ji ina so in kara ji ne. Jidda tace "cewa nayi yayana usman ya aikoni in mika mai kokon bararsa gareki da fatan za ki amsa mai bukatarsa. Fatima tayi ajiyar zuciya tace "ni kam jidda na yi mamaki danaji wannan maganar a bakin ki, na yi zaton ko yaushe ke nake gaya wa cewa babu wani namijin da zan iya sawa a zuciyata in haka ne kuwa bai dace ki zo min da batun wani namiji ba. Jiddah tace "Fatima kin san dai ba zai yiwu ki zauna babu aure ba don dr. khalifa ya rasu dole sai dai kiyi hakuri ki amshi kaddarar da Allah ya hukunta miki yarda da kaddara shi ne cikar imanin musulmi mumini. Ko kusa fatima ba ta jin dadin hirar don haka tace "To na ji ba ni lokaci zanyi tunani. Ganin yadda fuskar jidda ta nuna rashin jin dadin maganar tasa tace "kiyi hakuri jidda ba cewa nayi ba na son dan'uwanki ba wlh zuciyata ce ke cikin matsanancin hali har yanzu karfin hali nake ni nasan abinda nake ji game da ciwon kisan da akayi wa khllifa, ,na kasa sabawa da wannan damuwar, duk namijin danace xan aura a yanxu na cutar dashi domin ba zan ba shi kulawar data dace in bashi ba, wannan shi ne dalilin dayasa na fidda batun aure a zuciya ta, zan yi zamana haka har lokacin da Allah zai karvi rayuwata nima. **** To a bisa wannan ra'ayin fatima take tafiya da gaske ba ta son wani namijin yasake shiga rayuwarta, ba ta son sake soyayya dakowa sbda wahalar datake sha, amma ina yadda kasan kofa aka bude ma maza nasu sota, wasu su kan biyo tagun malam ganin bbu fuska ta fuskar fatima, wasu ma ta gun tsohon surukinta Alhaji muhammadu mahaifin dr. khalifa kasancewar zumuncin su ya dada karfi, Abban yana da tacewa a cikin rayuwar fatima, ya maida ita kamar diyar sa dan ma dai ba t son zuwa gdan ne a dalilin yawan kukan da take,. Bayan dawowar ta daga islamiyya yau ta idar da sallar azahar inna ta shaida mata cewa mama ta aiko nemanta, nan da nan rant yabci, to kawai tace tamike tayi wanka tasa wata doguwar riga ta shadda tasa dogon hijjabi fuskarta ba fara'a tashiga gdan su mama ta tsaya a harabar gdan tana kallon dakin dr. khalifa, har yanzu bbu abunda aka taba a ciki?
Chapter 47 · 0% Book details