Sashe 50
A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
duniya, xa kizo kina nadamar da za tasaki kuka da idonki. Farida tasaki ranta sosai kamar ba ita ba ta gayar da dangin mijinta tare da tmbayar ina amaryar take za taje su gaisa,jidda da tafi kowa tsanar farida tayi tsagal tace "kin ga malama ba ruwanki da amarya kiyi harkarki tayi ta ta. Farida tayi murmushi tace "haba jidda meye don na ce zanje mugaisa. Daya daga cikin yayyan usman hajiya hadiza tace "kin ga dakin nan shiga ni ban son hayaniya. Tamike tashiga dakin da aka nuna mata tayi sallama, suka amsa tace "na san baku sanni ba ni ce farida matar usman na rakoshi taryar amarya ne. Daya a cikinsu tace "ai kin kyauta mun gode sosai. *** Farida ta kwana ne a dakin usman sbda ta marairaice masa yan uwanta dana fatima tsangwamarta sukeyi, har ckin ransa ya amince da ita har yaji a ransa ba dadi, yace to tadawo dakinsa tazauna kawai. Tayi ta amfani da damar data samu gun jan ra'ayinsa yana bata kulawa, da safe ma bata barshi ya fito daga dakin da wuri ba duk da ya san da yan baka a gdan amma sai yadinga ji da farida bai son damuwarta, har su jidda suka gama hidiman cin abincin su da wanka. Farida dashi usman din suka shigo, farida tai saurin zama kusa da ita takamo hannunta tace "haba amarya wani irin kuka ne haka kamar zamanin da, sbda fa in deve miki kewa nazo in dan tayaki zama kafi? ki saba don Allah ki hakuri ki saki ranki. Farida ta kalallame usman tahana shi sakewa da fatima da zarar zai shiga dakin sai tabi shi tana fadin, "man muje muga halin da amaryarmu ke ciki. Shi duk bai san kishi bane ya dauka dai kyautatawa ne shiyasa yake biye mata. Farida tabar usman a falo tashiga daki ta fada toilet takira wayar isha take tambayarta yaya za tayi tahana uaman kwana da fatima. Isha tace "shiga za kiyi dakin ke kadai ki nuna mata wuka ki cemata wallahi idan tayarda usman yashigo lallai sai kin kasheta, idan usman yashigo lallai tai ta ihu har sai ya fita, to da zarar ya fito ke kuma sai ki janye ra'ayinsa kuyi daki, gobe kuma sai mu shirya mata wani tuggun a haka har yagaji da ita yakoreta kiyi zamanki a abuja. Farida ta kyalkyale da dariya tace 'kai Allah yabar mana ke isha kin iya tsara tuggu shiyasa nake sonki. Tace "sai kinji ni aminiyar... Ba karamin frgita farida tayi ba, jikinta yadauki rawa sakamakon ganin usman tsaye a kanta yana mata wani irin kallo. Ya zabga mata wata muguwar harara yace "kaiconki Farida,zuciyarki tana miki saka da mugun zare, dama biyoni kikayi don ki rabani da matata ko? Allah bai baki sa'a kin kori fatima ba kanki kika kora, don ina son ki tattara ki bar min gdana na sake ki. Faida takwala kara zata fara yi mai hauka yafice yashige dakin fatima ya sama kofar key,. Fati tatashi a tsorace tana kallonsa, nan da nan idonta yaciko, yayi murmuahi yace "haba fatima sai kace kinga dodo. Tashiga mai magiya, ko kula ta baiyi ba yakashe fitila, tun tana kokarin kwatar kanta har tagaji tahakura. **** Da kyar fatima tatashi tayi sallan asuba taci gaba da barci, bata farka ba sai sha dayan safe. Ta tsuguna tagaishe shi cke da fara'a ya amsa, tace "ina anty farida mu gaisa? Yayi tsaki yace "ba ta gdan. Ina tatafi? Bansan inda tatafi ba. Tayi mai wani iein kallo wace irin magana ce wannan? Yajawota jkinsa dakarfi yahadeta da kirjinsa takama kuka tana kici kicin kwacewa. Yace "dama kin hakura kin hadu da cingam. Hankalin fatima yakara tashi ganin yadda yake neman cire mata riga, Allah yabata sa'a tafisge kanta ta gudu ckin dakinta. Kafin tarufe kofar ya danna kai yatsaya yana mata dariya, yace "kin fiye tsoro fatima. Ta durkus tana fadin "Don Allah kayi hakuri na tuba. Yarungumeta tsam yana shafa mata jiki, yace "wai don Allah fatima so dadi gareshi ko wahala? Me yasa ciwon so yakeda daci a zuciya? Me yasa soyayya ba ta barin zuciya tazauna lafiya. Ba ni wannan amsar". Alhamdulillah. Daga taku RABI'ATU NASIDI ABUBAKAR.