Sashe 3
A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba, wannan ba sai na ro'keku ba na san kuna yi min. Dan Allah kuyi ha'kuri kuyafe min babu abinda zan iya cewa a kotu. Aliyu yayan fati yayi mgana a karon farko tun zamansu a d"akin yace "fatima bamu amince kici gaba dayin shiru a kotu ba dole kiyi magana. " Tace "shi knan yaya zanyi magana. Alhaji muhammadu dakowa yafi sani da, abba yace "kar kice ke kika kashe shi fati". Tace "Abba idan nace ba ni nakashe shi ba waye? idan kuma akayi bincike aka gane ni d'in ce abinda ake gudu shi zai faru, kuna fad'in hakane don fa kusamar min mafita wadda za ta ba ni damar ci gaba da rayuwa a duniya, yayin da ni kuma ba na son rayuwar ta fita daga raina so nake na mutu na bar duniya yadda mijina yabarta. " Aliyu yace "Anya fati baki samu ta'bin hankali ba? " Tace "lafiya 'kalau nake yaya ".kowa yarasa abin fad'i a kayi shiru. ********************************************* ********* Da sassafiyar ranar daxa a koma kotu hajiya maijiddah da akafi sani da mama tana kwance kan faffad'an gadonta na alfarma tunani da ba'kin cikin duniya ya isheta tarasa abin dake mata dad'i, tana mutuwar son D'anta an kashe mata shi wata 'kanwarta dake tayata zama wato anty sadiya tashigo d'auke da abincin karin kumallo tazauna kusa da ita suka gaisa tace "kidaure ki sha ko da ruwan sanyi ne zama da yunwa ya fi komi illa duk abinda yafaru rubuttaccen alamari ne babu wanda ya isa yago ge shi. " Tami'ke zaune tazubawa anty sadiya ido tace "anty sadiya kina ganin haka yadace mu zubawa lamarn nan ido kullum Alhaji yana cewa fatima ba za ta kashe khalifa ba toh ni so nake agaya min wa yakashe min d'ana? Anty sadkya tace "tabbas kam fatima ba za ta iya aikata wannan mugun aiki ba abinda yake da sar'ka'kiya shi ne daga shi sai ita a d'akin to waye yashiga yakashe shi? Mama tace "ke sadiya idan ma ba ita takashe shi da hannunta ba to da had'in bakinta aka kashe shi sbda ana ganin ubansa yana da dukiya d'ansa d'aya ne ko don a mallake dukiyar ubansa za ta iya yimasa haka. Anti sadiya tace "kigafarce ni amma ban tari numfashinki ba to amma idan haka ne da had'in bakin fatima ya ya za ayi ita data kasheshi ko ta had'a baki aka kasheshi bata gudu ba har akazo aka kamata? Allah (SWT) dasu kuma mahukuntan tunda Allah yabasu basiran gano gaskiyar wannan alamari cikin hikima da izinin Allah za su gano mana wanda yakashe mana d'a jininsa ba zai tafi a banza ba. A bisa hanyarsu tazuwa kotunne cikin mota mitar da mama ke tayi wa abba kenan yayi tsit yana jinta ko tari vaiyi ba ya yi tagumi yana jan charbi. Suna shiga su malam da goggo suka shigo suka gaisa, Abba yace"malam bana jin dad'i Yadda kake kaucewa had'uwa dani tunda wannan abu yafaru. " malam yarufe fuskarsa da babbar riga dan kar abba yaga fuskarsa yace "haba alhaji me, zan ce dakai? menake dashi wanda zan gaya maka dahar zaisa intsaya in kalleka, kaico. Ina ba'kin ckin faruwar wannan alamari har ina cewa ina ma ace banzo duniya ba da dai ace 'yar cikina ta kashe d'an mutumin kirki kamar kai d'in nan Alhaji muhammadu. Abba yaja hannunsa suka wuce cikin kotu ba tare dayace komi ba, wuri d'aya suka zauna mutane suna mamaki sosai yadda suke ganin iyayan wanda aka kashe da iyayan wacce ake zargin ta yi kisan. wannan abu yana matu'kar baiwa mutane mamaki haka zakaga jama'a na kallonsu, yai d'in ne ma dai hajiya maijidda tasauya fuska sama sama suka gaisa ba wani magana dasukayi fuska tamau ko da aka shigo da fatima ma ko kallon inda take batayi ba. ummi kamar ta fi su kansu fati shiga tashin hankali ta rame ta lalace . Fati na shigowa kotu da ummi suka fara ido sannan tadubi iyayanta dasauri tad'auke idonta xuwa 'kasa tashin hnkali datake ganin iyayanta a ciki ko wannan ma ya ishi mutum tashin hnkli da ba'kin ciki ina amfanin rayuwarta. Yau kam duk abinda zai faru sai dai yafaru lallai sai ta kawo 'karshen wannan zaman kotu. Bayan da akayi abubuwan daya dace ayi aka zauna mai karanta 'kara yakaranto, tuhumar da akewa fati na ta kashe mijinta a ranar da aka d'aura musu aure a daren farko. Mai shari'a Usman Muhammad Bamaina yace "fatima musa kinji tuhumar da ake miki a karo na biyu? " Ta gyad'a kai tace na ji ya mai shari'a, yau kowa na jin muryarta sosai, kuma kowa ya ji dad'in yadda tayi mgana har alamun natsuwa a fuskar iyayanta da 'yan uwanta musamman ummi wadda har tsima jikinta yake a ranta tana fad'in yawea fati gara ki yiwa kanki adalci da iyayanki damu masoyanki.Mai shari'a yace "fatima musa me za ki iya Fad'awa kotu akan haka? ma'ana kin amince ke kika kashe mijinki Dr. khalifa.? Kai tsaye fati taware muryarta tace "Eh ni na kashe shi ya mai shari'a. [5:07PM, 7/13/2017] +234 706 196 7803: A DAREN FARKO 3 Gabad'aya kotu tarud'e da sallalami kowa na fad'in albarkacin bakinsa ,iyayan fati dasu kansu surukan suka rud'e, ummi kuwa hannu tad'ora aka tana fad'in "wayyo Allah na wayyo fati meyasa kikace ke kika kashe Dr. khalifa bayan ba ke kika kashe shi ba. Mai shari'a yayi tsawa akayi tsit sai dai kukan 'yan uwan fati da ba ya 'karewa, ita kuwa fatin yau tana tsaye 'kyam ko gezau gadukkan alamu zuciyarta ta fara soyewa, idanuwan amma ba kuka take ba zafin zuciya ne, ba ta son takalli iyayanta taga mummunan tashin hnkalin dasu ke ciki, dama chan ita mutum ce mai tsananin tausayin mutane balletana iyayenta. Mai shari'a yace "fatima kotu tanason kiyi mata bayanin dalilin dayasa kika kashe mijinki a daren tarewarku. Fati tace "ban san dalilindayasa kika kashe mijinki a daran tarewarku". Fati tace "bansa n dalilin dayasa nakashe shi ba, ba abinda nao na zai iya furtawa a kan haka ya mai shari'a ina ro'kon wannan kotu mai alfarma Data taimaka min tayanke min hukuncin kisa a yau in bar duniyar nan inhuta, ba na son bugawar da zuciyata keyi yazamo sanadin mutuwata na fi son a yanke min hukunci dai dai da laifi na. Tanumfasa tana kallon al'kalin daga bisani tad'auke idanunta daga kansa zuwa kan jama'ar dake kotun, gaba d'ayansu su ma ita suke kallo kowanne da abinda zuciyarsa ke sa'kamasa game da ita. Tayi shashe'kar ajiyar zuciya tace "iyayena da 'yan uwana da dukkan masoya na ina ro'konku don girman Allah kuyafe min wannan yanayi dana sa ku nadamuwa sannan kuyi min addu'a rayuwa ta fita daga raina minti d'aya ba na son in 'ka ra yi a duniya na fi son inbi mijina. " Tayi shiru kamar yadda kotun ma tayi tsit kai ka ce ba kowa a kotun, al'kali yana 'yan rubuce rubucensa, haka a 'bangaran lauyoyi wasu suna rubutu wasu shiru kawai sukayi suna kallon fatima. Taci gaba da fad'in "ya mai shari'a a karo na biyu ina ro'on a taimaka a yanke min hukunci daidai da laifina na amsa laifina ni ce nakashe mijina". Wani daga cikin lauyoyi yami'ke yanemi izinin magana daga gun mai shari'a yace kanada daman magana. Yayi godiya yadubi fatima yace "sunana barrister Abbas Mukhtar inason kare wadda ake 'kara sbda na fahimci ba ita tai kisan ba ina nufin fatima musa ba ita takashe mijinta Dr. khalifa ba ina ro'on wannan kotu mai adalci data ba ni damar yin cikakken bincike a kan wannan al'amari, kuma inason a ba ni damar dazan yiwa fatima tambayoyi akan abinda ake tuhumarta dashi. " Mai shari'a yace "kanada damar yin haka. Yayi dariya yana d'an murmushi ya'kara maida fuskarsa ga fatima wadda itama shi take kallo fuskarta a tsuke, yace "malama fatima musa 'karfe nawa aka kaiki gidan mijin kuma a wace rana ce. " Fatima tayi shiru kamar ba da ita ake magana ba, Barrister Abbas ya'kara maimaita tambayar tare da ro'kon kotu data tursasa fati tayi magana". Mai shari'a yayi hakan amma Fatima cewa tayi "nagode da kake burin taimakona a bisa halin danake ciki, sai dai inason kayi ha'kuri gaskiyar magana ba zan iya ba ka amsa ko d'aya ba a bisa tambayar dakake min sbda ba so nake in ku'buta daga halin danake ciki ba, wanda yake bu'katar lauya shi yakeson yatsira nagaya muku ba na bu'katar rayuwa dan Allah kuyafe ni. Mai shari'a Usman muhammad Bamaina yadubi wani dogon d'an sanda dake tsaye gefe yace "Za a gwada 'kwa'kwalwar fatima don mu tabbatar da mai hankali muke shari'a, idan munyi zama na gaba za mu ji sakamakon sannan mud'ora a inda muka tsaya. Daganan aka d'aga 'karar zuwa mako biyu idan Allah yanuna mana,amma kotun ta ba wa 'bangaran lauyoyi guda biyu damar suyi duk binciken su akan yadda al'amarin yakasance don ba da kariya dawadda ake zargi. Yau ma kamar wancan karon kotun ta tashi da hayaniya kowa na fad'in albarkacin bakinsa akan kafiyar da fati tayi a shari'ar mamakin da take bawa yawancin mutane shi ne tayaya za ayi mutum yace shi ya fidda rai kwata kwata da rayuwa mutuwa yake muradi, wasu suna ganin wannan ya isa kowa ma ya amince ba ita tayi kisan ba, yayin dawasu ke ganin dan ace ba ita bace shi yasa tasallama tami'ka wuya, idan ba ita bace waye? Gida su biyu kachal ba kowa d'aki a kulle su biyu in har ance ba fati takashe Dr. khalifa ba to sai dai ace shi yakashe kansa, hatta hajiya Maijidda mahaifiyar marigayin dayawa daga 'yan uwansu abinda suke gani knan wannan kukan da take abinda suka d'auke shi kukan munafinci ne kawai. A harabar kotun kafin sutafi gaida malam musa ya tsaida barrister Abbas yana masa godiya a bisa 'ko'karinsa nakare 'yarsa, barrister yayi murmushi yace, "Ba komai kada kadamu baba na yi wannan ne domin Allah da tsananin tausayin da fatima ke ba ni tun randa aka fara tsaida ita a gaban shari'a na tabbatar ba Ita tayi wannan kisan ba, duk wanda yakashe Dr. khalifa na gida ne wanda yasan sirrin gidan insha Allahu da izinin Allah zamu gano ko waye,sai