← Book details A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 50

Sashe 18

A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hakuri watarana za ki cimma nasara akan khalifa, kidaure kici gaba da zama a gdan nan a matsayin mai yakin neman zuciyar masoyinki idan kika ci gaba da kyautata masa zai iya auranki musamman dayake kin shiga zuciyar iyayansa duka biyun. Tace "toh Allah yasa inafa cigaba da addu'a na san bbu abinda yafi karfin Allah. Jiddah ta mike da niyyar tafiya ta ce "ina takaici da zanyi wannan tafiyar ni kadai ba tare da ke ba soyayyar khalifa ta nisanta ki da kowa. Suka fito suna ci gaba da tattauna maganar shawarar da bata wuce abinda yashafi khalifa ba daga karshe ummi tace "jiddah soyayyar khalifa tayi min yawa a zuciyata abin har tsoro yake ba ni ,ina ta kokarin ganin na fidda shi a zuciyata don in huta amma abin ya ki yiwuwa, ina jiyewa kaina abinda zan iya aikatawa akan kowa idan narasa shi, idan na rasa khalifa bai auri wata macen ba nasan zan iya hakura abu daya ne ba zan taba iya hakura akaiba shi ne khalifa ya auri wata macen, ina nufin idan zai zauna haka ba na ganin mace a tare dashi shike nan. Jiddah taja tsaki tace "ni wannan shirmen na ki ne ba na so, wadannan maganganu? ba za subaki khalif ko su hanaki shi ba. Tace "ni fa ki sani haka jidda ina gaya miki ne dan ki san abunda ke ckin zuciyata wannan shi ne abin tsoron. Bayan tafiyar jiddah gdansu fatima tanufa ta iskesu ita da musbahu a zaure suna hira, wani yaro yashigo da sallamarsa yace "wai wani a waje ya ce don Allah wadda tashigo yanzu tazo. Ta tsuke fuska tace "kai tafi kace ba za tazo ba. Malam musbahu yace "haba ummi bai dace kiyi haka ba mu maza ba ma son muga anawa yan uwanmu haka. Fatima tace "malam ko kaje mana kaji me ke tafe dashi. Kafin malam yadawo suka shige cikin gida innarsu fati ta je unguwa a tsakar ida suka zauna kan tabarma, fati ta bata rai tace "ummi duk abinda nayi kina bata rai akan banyi daidai ba meyasa ke nake ganin ba kya iya sauraron duk masu kaunarki? shin ke abunda kikeyi daidai ne? ko kuma dan komi ke ce kika iya;? Malam musbahu yashigo cike da fara'arsa yana fadin "don Allah ummi kizo kugaisa da mutumin nan na san shi mutumin kirki ne sosai. Tace "don Allah malam kasallame shi yatafi kace an yi min miji kun taba ganin na saurari wani? Yayi dan jim sannan yace "to ba zan matsa miki ba amma zan shawarce shi akan yanemi shawra a gun abbanku. Bayan fitarsa fatima ta ci gaba dayi mata kallon tuhuma ranta a bace take fadin "baki ba ni amsar tambaya ta ba. Ummi tayi murmushi tace "fati knan kin more mijinki ma ya mori mace duk abinda kikayi kyau yake maki batan ran ma da kikayi yanzu bakiga yadda kika kara kyau da haduwa ba. Fatima takara fusata tace "ni ba wannan na tambayeki ba dole sai kin ba ni amsa ta gaskiya bisa tambayar dana yi miki idan kuma ba haka ba nima na daina yin abinda ki ke umarta ta. Ummi tana dariya tace "idan kin kwantar da hankalinki ko baki bata rai ba zan fada miki komai. Ta mike zaune suna fuskantar juna tace "fatima a cikin rayuwa bbu abinda ba ya samun mutum wani yasamu yadda yakeso wani akasin haka, wanifarkonsa yana ckin jin dadi karshensa wahala, yayin da wani zai taso ne cikin wahala karshensa yasamu jin dadi, fatima ni kam bbu wanda zanso a rayuwata bayan mutum daya da zuciyata ke muradi. Waye wannan? Na san ko baki san khalifa a ido ba hotunan da kike gani a gdansu zai sa ki shaida shi idan kin gan shi a fili, khalifa shi ne mutumin da zuciyata ta rataya da soyayyarsa, wannan shi ne dalilin dayasa ba na kula kowa dalilina shi ne duk wanda na kula bata mai lkaci zanyi domin zuciyata ba za ta so shi ba, me ye amfanin in yaudari mutum in nuna amincewa na gare shi alhali zuciyata tana tare da son wani, in dai ba yaudarar mutum zanyi ba to gwara in kyaleshi bbu wanda zan mallakawa zuciyata bayan shi, bbu wani da namiji da zai samu farin ciki a tare dani sai shi domin shi ne nake da kwarin guiwa dazan farantawa zuciya ko ina so ko ba na so sbda karfin kaunar danake masa ba mai misaltuwa bace, son danake masa ba zai bari in yi abinda zan bata masa rai ba, wannan shi ne dalilin dayasa nake ta burin ace shi na aura don in samarwa kaina farin ciki da kwanciyar hnkali a auran, kuma insamu tsira a gaban Allah idan nayi mai biyayya, fatima ina zaton wannan shi ne dalilin dayasa ake ba ma'aurata daman zabar wadanda suke so yayin neman aure, wanda zuciyar mutum ta aminta tana so shi take iya bi. Fatima tace "toh ummi an yi maganar auranku ne da khalifan kan tafiyarsa ? Tayi murmushi "fatima in banda khalifan iyayansa ma basu san ina masa wannan son ba, ya gargade ni akan kar in sanar da iyayansa ballantana a matsa masa kan ya aureni, khalifa ba ya so na ni ce dai zuciyata ba ta iya hakuri dashi. Fatima ta girgiza kai"anya kuwa za ki ce kai tsaye bai son ki ummi ? shin meye abin ki a tare dake, ko halayyarki ta arziki ta sa mutum yaso ki. Tace "Allah sarki fatima ke ce kime ganin haka, ai ita soyayya ba ruwanta da kirki ko rashinta, idan kana son mutum to kana sonsa idan ba ka so kuma ba za ka so shin ba koda ya fi kowa kirki. Fatima tace "to yanzu meye abinyi ummi ni bar na ji na tsani khalifan sbda rashin tausayin daya nuna miki, bai dace ka watsawa wanda yake sonka kasa a ido ba ya dace yatausaya miki, ni kam ina bakin cikin wannan damuwa ta ki inama inada halin taimakonki wlh da sai inda karfina yakare. Ummi tace "fatima idan kika biyewa damuwata za kiyi tazama cikin damuwa ne domin kuwa damuwa ba ta kare mini don lokacin dana fara son khalifa nake kuka nake zama a cikin damuwar da har sai da nasaba da ita, inata kokarin raba kaina da soyayyarsa don in huta amma ko yaushe soyayyarsa karuwa take a zuciyata abin ko sauki ba ya yi, tunda har aka kai wannan lokacin khalifa bai waiwayeni ba ba zai tausaya min ta fuskar soyayya ba kuma dagaske yake bai sona, ban isa in tursasawa khalifa ya aureni ba dole knan in hakura da auransa, amma ba zan iya hakuri dashi ba, ba zan auri ko wanne namijj ba ba zan hakura da khalifa ba. ******** Khalifa ya fara karatu mai zafi a kasar germany cike da zuciya mai karfi da cikawa mahaifinsa burinsa na ganin ya zamo cikakken likita dan yataimaki al"umman musulmai, Anisa tana tre dashi a gdansa ta zamo tamkar kukunsa itace abincinsa na safe da yamma a bisa ka'idarsa na cin abinci guda biyu kamar yadda ya tsarawa kansa, ko kusa Anisa batayi niyyan zaman gdan khalifa ba illa soyayya data rinjayi zuciyarta wadda ba ta barinta tayi tasiri a tare dashi, duk abinda yace mata dashi take amfani, yana matukar gamsuwa da nau'ikan abincin da take shirya masa kuma yana yaba mata tare da nuna mata jin dadinsa, lamarin dayayi mata dabaibayi knan take jin cewa data sabawa dr. khalifa gara ita ta matsawa kanta, babbar abin mamakin shi ne duk irin yadda ake neman soyayar mace ga da namiji zuciyar anisa ta gama nisan kiwo a ckin son khalifa amma a takure take da zaman gdan na sa sbda bbu abunda yake hadata dashi sai hirar duniya ba batun soyayya, idan gari yawaye tagama masa abin karyawa zai fita zuwa makaranta itama za taje ta ta, idan tadawo sai tayi abincin yamma, in dare yayi zai shirya ya dau ado yafice yawon zaga gari yayin dazai barta a gida kamar wata yar jiran gdansa, sai ya gama gararin ta zai dawo yabarta a falo yashige dakinsa, anan take kwana, wani lokacin tanaji zaiyi ta hira da yammatansa taci kukanta tagaji tahakura, idan tayi yunkurin barin gdan sai taga wata dai sabuwar damuwa ce za ta hada kanta da ita idan ba ta ganinsa. Yau ta tashi da kasala zuciyarta bbu dadi tahada abincin safen kamar yadda tasaba tashiga falon fuskarta bbu walwala, dr. khalifa na zaune teburin cin abinci bai fara cin abincin ba magana yake a waya tazauna tana mai kallo, a kullum shi me kyau ne amma kyaun dayayi yau na daban ne, wani irin abu taji ya kara turnike mata zuciya, idanuwanta suka kada jajur tazauna kan kujera taci gaba da kallonsa yanata hirarsa a waya cike da nishadi abubuwan dayake fada suka cigaba dasa zuciyarta a wani yanayi tadinga jin cewa meye amfani zamanta a gdan khalifa kullum ranta na baci, bata san inda tadosa ba, ya kamata tayiwa kanta fada. Bayan ya kashe wayar ya kawo ganinsa gareta yace "ya akai sister an tashi lfya ko,? Wani irin kallo tayi masa wanda bai taba gani ba tare da ita yataso zuwa gabanta yatsaya hannayensa zube ckin aljihun wandonsa yana kayataccen murmushin nan na sa mai kayatar da zuciyarta amma yau takaici ne yakara rufeta, hawaye suka taru a idonta tai sauri tashige daki. Khalifa yatsaya shiru yana kallon kofar dakin nata cike da mamakinta, ko dayake bai kamata hakan yazamo abun mamaki ba gareshi don yanada tabbacin son da Anisa ke masa ne yasa tayi shahadar zama a gdansa tare da sadaukar da kanta gun hidimar dafa abinci da gyara mai gida, hatta gadonsa ita ke gyarawa za tawanke mai toilet tagyara mai kayan sawar sa da komi na sa, in banda ya dage akan bai so tai masa wanki da gugar kayansa da tuni ita ke wankewa don har ta fara ya yi mata jan ido yace ba zai yiwu ba ayyuka za suyi mata yawa, ita ba lada zai biyata ba ballantana yadinga biyanta kudi ,damuwarsa itace bai san dawani ido zai dubeta ba ranar data gaji ta bayyana mai batun soyayya da bakinta
Chapter 18 · 0% Book details