Sashe 22
A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
daya taji kunya ya kamata cikin karfin halin gaske tarusuna tace "barka da isowa. Kallon da yayi mata yasa jikinta ya hau rawa ta wuce dasauri cikin dakin ummi tace "ke ai mutumin na ki sun shigo. Ummi tadafe kirji tace "don Allah ? furar da bata sha ba knan tazuba wata doguwar riga amma ita ta atamfa ce tayafa dankwalin a kanta ta fesa turare ta fito falon, tuni har sun haye tebur sun fara cin abinci. Fatima tabude dakin taleko don taga kallon da dr. khalifa zai yiwa ummi, ai kuwa fuskarsa baa fara'a yake amsa mata gaisuwa, su dr. hafiz ne masu zolayarta, shi kam gogar na ka ya yi dif abinci kawai yake durawa cikinsa. Wani irin takaici yakama fatima kamar taje tashake dr. khalifa tahuta an masa abinci ko yabawa ba zai yi ba yana walakanta wadda tayin. Wai wane irin mutum ne haka, nan da nan tayi takara tsanar sa, taja tsaki takoma kan kujera taharde . Ummi tashigo dakin harara tafara samu a idon fati tace "mi yiwa Allah ki daina son dr. khalifa ba shi da kirki. Ummi jikinta a sanyaye tazauna tayi tagumi tace "kiyi hakuri haka halayyarsa yake har in mutu ba zan daina sonsa ba, shi kadai nafara so a rayuwa rata, ba na iya hadashi da kowa ko bai aureni ba ba zan hakura dashi ba kitayani addu'a kawai. Fatima tafigi hijjabinta tace "to gaskiya ni ba zan iya ci gaba da zama a gdan nan ina ganin wanna abin haushin ba. Bata ji kiran da ummi ke mata ba tafice, sai dai abi ? takaicin dole tawuce ta falo gashi ba ta son kara ganin dr. khalifa yayin da shikuma dr. din kamar an ce yadago idonsa sai yadago karaf akan fatima za tafita, shi kansa bai fahimci muryarsa ba lokacin daya ke ce wa, "ke zo nan" Tayi dan jim, ba wata a falon lallai ta san da ita yakeyi, ya dace ta walakanta abin da ummi ke so, ranta a bace ta nufo inda suke ta tsuguna a gefe kanta na kasa tace "Ga ni . To bai san dalilin dayasa yakirata ba, ballantana yasan abinda zai gaya mata, ya samu kan shi da zuba mata ido shi dai bai san ta a gdan ba, Dr. hafiz ne yace "yammat don Allah ya sunanki ? Fatima kawai tace. Kafin wani cikin su yakara magana tamike dasauri tabar gdan. Dr. khalifa ya ajiye spoon din hannunsa yayi ajiyar zuciya yace "fatima. Kai wannan yarinya Allah ya hore mata kyau. Dr. bashir ya kyalkyale da dariya yace "likita knan bokan turai nan kuma kagano ance inda baki yakarkata nan yawu ke zuba. Fitowar mama takatse maganar tazauna suna hira, dr. khalifa yace "mama ina kuka samo fatima ? Tace "yarinyar nan makwabtan mu ne wanda kuka gaisa da babanta a waje dazun wanen malam musa. Ya basar da maganar kamar bai damu ba sukaci gaba da wata hirar. ***** Tun a daren masu zuwa yiwa dr. khalifa sannu dazuwa suka fara cika gdan yawanci tsoffin abokansa ne musamman na B. U. K da 'yan'uwa da abokan ckin dangi, wayoyin sa ma kashe wa yayi don yahuta, bai samu kansa ba sai sha biyun dare yahada ruwa mai zafi yai wanka yafesa turare yahaye gado, tunanin bai samu masauki a zuciyarsa ba yahau bacci sallar asuba ma sai da abbansa yatayar dashi suka nufi masallacin tare, ita kanta sallar idanunsa a rurrufe yayi ta suna dawowa yakoma wani sabon barcin. Yayin da ummi takwana ckin fargaba da kai komo a zuciyarta da tunanin tayaya za ayi dr. khalifa ya aureta ? zancen haduwa yanzu ba a magana, a tsaya bayyana tsarin kyau da Allah ya hore wa dr. khalifa bata baki ne, zuciyarta takara rudewa, sabuwar soyayyar data ninka ta bata ta karu akan ta da, ummi ta ji kanta tamkar tsawa tsawa yake mata. Da sassafe kamar yadda tasaba tashiga kitchen tafara hada abincin dr. khalifa na musamman, mama ta fita tace mata takira fatima a waya tazo tataya ta domin akwai wasu abokan dr. khalifa daza suyi breakfast tare nan da karfe takwas. An yi sa'a fati ba ta kashe waya, lokacin da ummi tabayyana mata bukatarta amsawa kawai tayi ba dan ranta ya so ba, hakanan take jin wani irin abu a zuciyarta jininta bai hadu da dr. khalifa ba, kallon da yayi mata ya firgita ta kwarai dagaske, ba ta da matsala da inna da babanta akan zuwa gdan mama, hijjabinta dogo har kasa tasaka tafito zuciyarta cike da sake saken abinda zai je ya xo. Aikin suke kowacce da abinda zuciyarta ke sakawa, karfe takwas komi yakammala a tebur suka debi na su sukayi dakin ummi. Kinga dr. khalifa ko fati ? Ummi tayi tmbayar tana kallon idon fatima wadda tagyada kai fuskarta a tsuke tace "eh na ganshi meye. " Ummi tasa gefen mayafinta tana sharar kwalla takasa cigaba da magana, zuciyar fati ta kuntata sosai yadda abincin yaki ciyuwa a gun ummi itama kasa ci tayi, tace "ummi ko zuwa zanyi in rokeshi yasoki. Tace "karki yi haka ya gargade ni akan kada in fadama cewa ina son shi, dole in kiyaye dokarsa in dai inason in zauna lfya. Fatima tace "to yanzu haka zamuyi ta zaman damuwa ? Ummi tace "damuwa ta kam ba zata gushe ba amma na ci alwashin ba zan bar dr. khalifa ba ba zan yarda in rasa shi wata tasame shi ba. Tunda ummi take irin wadannan kalaman jinta kawai fati take ta san me za ta iya ? hakuri ne yazame mata dole in batayi ba tayi tashan wahala idan so cuta ne hakuri kuma magani ne. ***** A wannan rana malam musa mahaifin su fatima yafidda bayanin cewa sati biyu rak za ayi bikin fatin da musbahu akai tagdansa, har inna tace "malam bai yi wuri ba har yaushe aka gama shiri. Yace "shi kam wannan lokaci yasanya kuma ba zai daga ba, fatima na dawowa gda malam musbahu yatare ta da zancen yana cikin farin ciki mai yawa, itama ta nuna gamsuwarta tare da fatan alheri garesu baki daya, yatambayeta abinda za tayi da kawayenta na shagalin biki tace ta fi sha'awar walima a ranar jumma'a da yamma amma dai za tayi shawara da antinta ummi. Data shiga ckin gda takira ta a waya tashaida mata, ummi tarangada guda tace "amarsu ta ango knan wannan sai mun zauna an tsara yadda za ayi, zanso ganinki ranar wannan biki za kiyi kyau na jan magana. Fati tace "fatana aure dai Allah yasanya mai alheri da albarka ba na na so inga anyi aure anyi shagali aure na soyayya amma auren bai je ko ina ba sai kiga ya lalace ko ayi ta samin matsala a rasa laifin waye mazan ko matan ? Ummi tace "kowa na da laifi fati a tsakanin mazan da matan ko wanne akwai rawar dayake takawa gun haifar da matsaloli ckin auran da rabuwarsa, amma dake insha Allahu za kuzauna lafiya da malam musbahu domin aure ne da aka gina shi a bisa kyakyawar turba, kuma za ayi shi ne don Allah,. Bayan ummi ta kashe waya tafito falo, ganin dr. khalifa ya hakimce bisa kujera wata lafiyayyar shadda a jikinsa maroon colour dinkin da matasan zamani ke yi yayi, ya yi kyau har ya wuce misali, farin gilashin idone a fuskarsa bai damu da zaman ummi a gun ba yaci gaba da fadin "mama kinsan maganar aure tana bukatar nazari da bincike, wlh a rayuwata bbu auran dana tsana irin je ka kadawo, ayi aure ana farin ciki da zarar an je an zauna a kasa fahimtar jin dadin dake ckin zaman auren, kullum kana ckin damuwa matarka na ckim damuwa meye amfanin hakan, amma idan aka natsu za asamu kwalliya tabiya kudin sabulu sbda na sani bbu wanda ya isa yakaucewa abinda Allah ya hukunta masa. Yayi shiru anan yana nazarin fuskar mama don ya fahimci yadda tadauki maganar, batace komi ba tajuyo tadubi ummi tace "'yammata yaya akayi ne yau fatin batazo tayin hira ba ? A sanyaye tace "batazo ba waya tamin yanzu tace malam ya ce idan Allah ya kaimu nan da sati biyu za ayi bikinta. Mama tatsuke fuska tace "wani irin sati biyu kuma ? Tace "haka dai tace. Tace "to je ki kiramin fatin har yaushe akayi mata shiryen shiryen amaren. Dasauri ummi tabar gun tafada daki don tasamu damar yin kukan data ke ta hadiyewa. A falo kuwa dr. khalifa ne yaji wani irin abu ya tsirga masa a cikinsa zuciyarsa takama bugawa. Fatima Za ayiwa aure nan da sati biyu ko kuwa wata fatin ce daban, nan da nan yanayinsa yasauya gaba daya yawaiwayo tare da zare space din sa yadubi mama yace "mama wace fatin za ayiwa aure ne ? Tayi murmushi "fatima yarinyar nan dai ta makotanmu daka gani jiya. Yace "doyar malam musa ? Tace "yawwa ita kuwa. Abinda yafito daga bakinsa shi kansa ya ba shi mamaki don bai san sanda yace "Lallai da sake". ****** A DAREN FARKO 19 Mama tayi masa wani irin kallo tace "me kake nufi ? Anan ne yadan shiga natsuwarsa yace "mama wannan yarinyar nakeso na aura don gskiyar magana ita neke ganin ta dace da rayuwata da tsarina haka nan zuciyata ta aminta da soyayyar ta dari bisa dari don... Ckin zafin rai mma tadaga mai hannu tace "kai ya isa haka, saita bakinka kasan abinda kake fada, fatima an yi mata miji tsawon lokaci mai yawa kuma ba za a fasa ba shi a ba ka ba. kada kasoma sanyawa zuciyarka soyayyarta wahalar da kanka za kayi don baza kasame ta ba. Bai ce komi ba yamike yabar faol zuwa daki ? sa yakira dr. hafiz yace "kana ina ? " Yace"ina asibiti yanzu muka fito daga meeting.. Yace "to ina ka dosa ? Yace "gida za ni akwai magana ne ? Yace "kwarai kuwa magana ma babba ba karama ba. Yace "kasameni a gida mana. Mota yadauka yanufi gdan dr. hafiz da ke hotoro ya iske ya rigashi isa, yace "matar gdan fa da yaran ? Dr. hafiz yatabe baki yace "ai mata ba su da matsalar data wuce biki, sunan wai kanwa ta ce data