← Book details A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 50

Sashe 4

A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dai inason kataimaka min fatima tadinga ba da amsa a kotu sannan xanje inganta kutaima ka min tayimin cikakken bayani duka tambayoyin da zan mata dan insan yadda zan 'bullowa al'amarin. Malam yace "To ni na rasa me yasa fati take tsuke bakinta komi sai tace ba za ta iya fad'a ba sbda rayuwar ta fita Daga ranta. Barrister yayi murmushi yace "bako mi tsananin damuwa ne yasa take fad'in haka, matsayinku na iyayenta ku yadace kulalla'bata tafad'i yadda akayi. Malam yayi masa godiya mai yawa bayan tafiyarsu malam d'in barrister na xaune a motarsa shi kad'ai yana nazarin alamuran fatima tausayin ta har ya yi masa yawa a zuci.,daurewa kawai yau yayi ya zo kotun tun a wancan zaman da akayi hankalinsa yatashi sosai gameda al'amarin yarinyar, tun lkcn abinda yake d'aga masa hnkali matsalar d'aya matsalar kowama ita ce shirun da fati tayi tana neman mutuwa ido rufe ta 'ki ba da had'in kai ballantana a samu mafita. ********************************************* A hankali ummi tafito daga motar tabi bayan mama zuwa cikin gida, kowanne zuciya ba dad'i , a falo suka zauna gaba d'aya yayin da ita ta dawo dabaya zuwa ainihin d'akin Dr. khalifa na gidan har yanzu mukullan d'akin yana hannunta ita kad'ai take bud'ewa tashiga tunda ga lokacin daya mutu zuwa yanzu, komi na nan yadda yake wani irin 'kamshi mai dad'in gaske yana tashi a d'akin, gaba d'aya kayansa nasawa suna jere a cikin wardrobe gwanin ban sha'awa manyan hotunansa da akayi enlargement d'insu guda biyu na gefe da gefe na gadon ya yi kyau ba na wasa ba. Tazauna a gefen gadon tanasa hannu tad'auki hoton tarungume kam kam idanunta a rufe hawaye wasu na bin wasu zuwa chan ta ajiye tashiga bud'e durowowin jikin madubin hotunan bikinsa da fatima ne birjik musamman ma gun lunching da dinner dayawa yarungume fatin ne 'kam 'kam a 'kirjinsa wasu kuma tare da abokanansa maza da mata. Kan cinyar ummi yaji'ke dahawaye kamar ruwa aka zuba mta a cinya tun ranar da aka kashe Dr. khalifa take kuka amma bata ta'ba kuka irin na wannan rana ba, har sai dataji numfashinta kamar zai d'auke. Ba za ta ta'ba mantawa da abinda yagya mata ba a yammacin lahadin daza akai fatima gdansa wanda kuma a wannan rana ce aka kashe shi bai sake kwana a gidan duniya ba. Yana tsaye a harabar gdansu tare da manyan abokansa biyu wad'ana baida aminai kamar su. Manyan likitoci Dr. Hafiz Bala Muhammad da Dr. Mustapha Abubakar kura, yana tsakiyarsu suna hira, sai ita ummi tafito daga cikin gida tana ganinsu tahau yimusu hoto a wayarta, Dr khalifa yaharareta yace "wai meyasa kike daraina mutane ne ummi ni kikewa hoto? Sai Dr. Mustapha yace "kaima kanada saurin hushi khalifa ko wacce rana idan an maka abu za ka 'bata rai banda wannan rana wadda tazamo ta auranka da matar dataza mo allura cikin ruwa kaine kaxamo mai rabon daka zu'kota. " Dr. khalifa yarausayar dakai yana murmushi tare da lumshe ido yace "ka fad'i gskiya Dr. Mustapha tabbas ni ne na cafko wannan allurar data zamo tamai rabo ce, a daidai lokacin dana fidda rai da ita sai najita kawai a hannuna ,tabbas wannan rana ta dace tazamo ta farin cikina, ranar dazan sadaukar da komi na wa sbda Fatima. " Ummi tay murmushi tace "shiyasa nima nake maka hoto domin ka yi min kyawun daban ta'ba ganin ka yi shi ba a duniya dukda cewa kai d'in me kyau ne kullum kyau kake da ado. " Dr. Hafiz Bala yace "har bayan hoto yanada kyau ma yayi miki kyauta ta musamman ummi." Dr. khalifa yayi murmushi yace "ko shakka babu a wannan rana ina cikin farin cikin daban ta'ba samun kaina a cikin shi ba, sai dai kasan tun safiya gabana ke fad'uwa bansan dalili ba wannan yayi sanadin dayasa tun ruwan shayi danasha rabin cup d'azun bayan d'aurin aure ban iyacin komi a bakina ba. Ummi tayi wal da ido tace "fad'uwar gaba kuma Dr. a irin wannan rana? ni dai na san ko kusa bakayi kama da wanda mace za ta ba wa tsoro ba ballantana ince firgita kayi sbda fatima. Dr. Mustapha ya bugi kafad'arsa yace "wa wannan? ni tunda ake ma gwargwadon bud'ewar idanuna ban ta'ba ganin namijinda yayiwaa mata farin sani irinsa ba, farin ciki ne yayi masa yawa sbda soyayyarshi yasa ma gabansa yake fad'uwa....... " Tunanin ummi yakatse a nan lokacin da mama taturo 'kofar d'akin tatsaya tana kallon ummi kukan datake yabata tsoro ta'karaso dasauri ta kamata takwashe hotunan dasuka ji'ke da hawaye ta mayar, takamo hannunta tafito da ita tarufo d'akin takar'be makullin tace "daga yau ko 'kofar d'akin nan ba na so kisake zuwa, haka kada ki 'kara zuwa kotu ba xa muyi biyu babu ba, mun rasa Dr.khalifa muna cikin ba'kin ciki mai tsanani kema damuwa na neman xama ajalinki to B xai yiwu ba. Cikin kuka ummi tace "Don Allah mama kada kiharamta mini shiga d'akin likita, yin hakan ne kad'ai zaisa zuciyata ta sassauta daga damuwar danake ciki, na rasa d'an uwana ga aminiyata na cikin matsancin zargi na bi duk hanyoyin daya kamata inbi don ganin fatima ta ba lauyoyi had'in kai ta 'ki burinta akasheta meyasa ba zanyi kuka ba mama? mama tayi tsaki tace "ina mamakin yadda ke Da Alhaji kuka d'auki damuwar duniya kuka d'orawa kanku akan fatima shin dakuke cewa batace komi ba me za tace, fatima ba ta da abin cewal shiyasa tai shiru, ko a hankalce kun san 'karyane ace akwai. mutumin da ake tuhuma irin hka ya'ki amsar taimako daga lauyoyi don kawai yana burin mutuwa. kinta'ba ganin wanda yazauna yana jiran mutuwarsa kuma yana maraba da ita, saidai fa in ta zo a kar'beta don ba yadda za ayi da ita. Ummi tasaki hannun mama tazubla mlatla ido muryarta a dashe tace "mama shin kina nufin kin amince fati za ta iya kashe likita? Mama tayi murmushi tace "ummi ummi kiji tsoron duk wanda kika taimakawa. Akoda yaushe idan za ki taimakawa mutum to kitaimake shi kai tsaye don Allah ba wai don zai saka maki da alherin dakika yimasa ba, shi dama mutum bbu abinda yake cika cikinsa sai 'kasa shi. mai butulcewa mahaliccinsa ne ma ballantana ace wani gama garin mutumin don hka ba abin mamaki bane ga mutumin daka d'auko shi daga rana kadawo dashi inuwa shi kuma yaturaka ranar,a cikin mutane mutumin dayake salihi ko mai shiru shiru irin fatima mutane ba sa zarginsa da mugun abu sbda yanayinsa amma Allha (SWT)daya halicci zuciya shi yasan abinda ke cikinsa. Ummi tayi shiru na lokaci mai tsawo daga bisani tace "Mama kina nufin kin amince akashe fatima akan kisan likita? " Tace "ummi ba ni da masaniyar abinda shari'ar za tahaifar, sbda ita shari'a macece da ciki ba wanda yasan abinda za tahaifa sai Allah mudai mun mi'ka kukanmu ga Allah yabayyanar da gaskiya. " Tayi gaba tabar ummi tana binta da ido jikinta yayi sanyi 'kalau, da'kyar tad'aga 'kafa tabita cikin gida. . . [5:08PM, 7/13/2017] ‪+234 706 196 7803‬: A DAREN FARKO 4 maganganu sunyi yawa a kan abubuwan dasuke faruwa a kotu, wasu sun fara yarda tunda tace takashe Dr. khalifa yayin dawasu har yanzu suna ganin ba'kin cikine yahanata magana dukda cewa su d'inma suana gnin fati ba ta da hujjar da za tasa taja bakinta tayi shiru ta 'ki cewa komi. Kwana biyu a zauna kotu malam musa da mahaifiyarsu fatima da da ummi da Barrister Abbas suka isketa a inda take tsare abisa alfarmar dom mahaifin marigayi Alhaji muhammad amma fa akwai sa idon 'yan sanda guda biyu. Fatima tarusuna tagaida mahaifinta ciwon rai ya'kara damunta sakamakon ramewar dataga ya dad'a yi ya fita hayyacinsa kaida gani ka san yana cikin matsananciyar damuwa da takaici, sannan tagaisa dasu ummi da barrister. Malam yace "fatima. Ta amsa 'na'am baba. Yace "fatima wannan shi ne zuwa na 'karshe dazanyi gunki akan in ro'ki kiyi bayani a kotu idan kinga dama kiyi magana fati idan baki ga dama ba kicigaba dayin shiru tunda kinfi 'bukatar mucigaba dazama cikin tashin hnkali darashin sanin abin yi. A yau na zo ne ba dan in ro'ke ki kiba lauyoyi da al'kali amsar duk tmbayar dsuka bu'kata agunki ba zuwa nayi in ba ki umurni a matsayina na mahaifinki idan ya cancanta kiyi min biyayya kiyi fatima idan kuma ban isa ba kici gabadayin shiru kamar yadda kika saba. Fatima tace "baba idan nayi bayanin zai sauya 'kaddara ne? ko kuwa bayanin na wa zai dawo da rayuwar Dr. khalifa izuwa gidan duniya, baba idan ni ce nakshe Dr. khalifa idan ma ba ni bace Allah SWT ya san haka tunda shi yake ganinmu a lokacin damuke kulle mu biyu acikin d'aki ni da Dr. khalifa, ni dai abinda nakeso ayi amfani dashi shi ne tunda naji na gani na amince ni ce nakashe shi na yi i'kirari da bakina a yi min hukunci dai dai da laifina shiknan shari'a sai a gaban Allah (SWT) wannan itace rana daza a tsage gskia ranar dakowa zaiyi bayanin abinda ya aikata da ga'bo'binsa bama da bakinsa ba kuma itace dawwamammiyar rayuwa wadda va za ta'kare ba har abada. Don Allah baba kayi ha'kuri kada kayi fushi dani akan hka bbu abinda bakina zai iya furtawa a lamarin kisan nan. Ummi tace "fati mahaifanki sun kasance suna masu alfahari dake a bisa biyayya da kike musu, baki ta'ba yin musu dasu ba, ba'a ta'ba samun wata rana da suka baki umurni kika sa'ba ba, meyasa a wannan karon za kisa'ba musu? Ba ki da hujjar dazakice rayuwarki ta zo 'karshe fati, ko kuma dan kina jiran mutuwa shiyasa kike ganin biyayya ga iyayankinya va ta da amfani? To bari in tunatar dake wani abu guda d'aya ance akwai mutumin dazai ta aikin alheri wanda yake share masa hanyar tafiya aljannan sai 'karshen rayuwarsa tazo sai kawai ya aikata wani abu wanda zai kaishi wuta sai ya shiga wuta. Yayin dawani zaita aikata aikin dazai kai shi wuta gab da mutuwarsa siya aikata abinda zai kaishi aljannan saiya shiga janna. Fatima ina ro'kon ki kiyi abinda iyayanki suka bu'kata ba ki da hujjar dazaki sa'bawa umarninsu, ba ki da tabbacin kwann ki
Chapter 4 · 0% Book details