← Book details A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 50

Sashe 39

A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yarikice. Jikin fatima kawai yake bukata, yashiga dakin mama tana zaune tana hada wata zuma da tsimi da za taba fatima. Tayi mai wani irin kallo ganin yanayin daya shigo dashi tace "kai kuwa lfya? Yace "Mama ina fatima? Tayi tsaki tace "wai kanka daya kuwa? da tsakar daren nan kake nemanta me za tayi maka? Ya dan langabar dakai yashiga in ina yarasa abinda zai cewa mama, karshe yace "wai da indomie za tadafa min. "To da basu dawo da ita nan gdan ba fa? Wa zai dafa maka? ta watso mai tambayar tana harararsa tace "to bace min da gani kaje kace ummi tadafa maka. Zaiyi magana tace "Allah idan kana matsa mata xan hanaka ganinta. Yafice zuwa falo abinda yasawa ransa shi ne ba zai iya barci ba sai ya rungumi fatima a jikinsa ko ta halin kaka. Anty sadiya tafito daga dakin dasu fatin suke za tashiga dakin mama ganin shi a tsaya yasa tace "yaya akayi boy? Ya tsareta da ido fuskarsa ba walwala yace "ina fatima? Tace "wanka take. Bai ce komai ba yasa kai dakin ummin, ta bishi da kallo tana jinjina kai tashige dakin maman tazauna kusa da ita tace "in kin gama ki ban in ba ta tasha ba za tasaki jiki tasha a gabanki ba. Mama tamika mata a sanyayae tace "kazar "yar sokoto ta kawo ma yana kitchen idan za ta iya ci ki hada ki bata wannan fitinannan yaron za a sha matsala dashi dole sai an gyara fatima, sai dai ni kam jikina ya yi sanyi wannan soyayyar da khalifa ke nunawa fatima ta yi yawa, kada fa idan sun je aun zauna tayi amfani da wannan damar tadinga juya shi kamar waina. Anty sadiya tace "don Allah mama kada ki sawa ranki irin wannan damuwar kowa da lokacinsa kuma a yanayin fatima ba za tayi haka ba yarinyar ta samu tarbiyya me kyau. Mama tace "uhm sadiya mutum ba a shaidarsa mace tana da wani irin hali yayin da da namiji yadaga hankali a kanta yana sonta dayawa shike nan tasamu damar yi mai yadda taga dama maimakon tayi amfani da wannan damar gun rikeshi da kyau sai tadinga murza kambunta yadda taso. Sadiya tace "mama ki yarda da Allah ki yarda shi ne me komi, addu'ar da kikewa khalifa ke da abbansa ba zai taba faduwa a kasa ba, insha Allahu bbu abunda zai faru da aurensu sai alheri, kidauki fatima kamar "yar dakika haifa sai Allah yakalli kyakyawan niyyarki yatsare khalifa daga dukkan wanda zai masa abin da zai gusar da hankalinsa, idan kaji tsrom Allah ka kyautatawa 'ya'yan wasu Alkah zai dubi na ka zuri'ar ko ba ka da rai. mama tace "Hakane anty sadiya ina kaunar fatima dayawa nima yanayin soyayyar da khalifa ke nuna mata ne yayi yawa ni na rasa me yakeji a zuciyarsa game Da ita, in dai akan fatima ne to fa zuciyarsa ba ta da sukuni, zai iya hakuri akn komi banda ita. Duk su mama na wannan tattaunawar ne dai dai lokacin da fatima tagama wanka tafito daga toilet daga ita sai dauri kirji sai ko dan tawul din data yafa a kafadarta bata san khalifa na dakin ba, ganin shi kawai tayi tsaye jikin madubi ya kuma zuba mata wadannan fitinannun idon na sa masu tsananin kyau da laushi, tatsaya sororo tana kallonsa kamshin dayaji yana tashi a jikinta yaji kamar ana fizgarsa zuwa jiki? ta, lamarin dayayi sanadiyar daya kasa rike kansa sai da ya isa gabanta yaja hannayenta biyu yahadata gam da jikinsa yasa harshensa yana lasar lebbenta, gaba daya jikin su yadauki rawa ita tsoro takeyi kada wani yashigo ya iskesu a haka yayin da shikuma jikinsa na rawa ne sbda wata fitinanniyar shawa data jefa shi a cikin yanayin da bai taba shiga ba a rayuwarsa, yakama kunnuwanta yana gaya mata kalaman dashi kansa bai san yana fada ba, har sai da fati taji tsigar jikinta na tashi tasa hannu tarufe mai baki. Kwatsam ummi taturo kofar dakin tashigo, khalifa yasaki fati yajuyo yayi wa ummin wani irin kallo yafice, ta ajiye abin cin data zubo musu kamar ba abinda tagani tashiga jan fatin da hira nan kuwa zuciyarta kamar za ta tarwatse sbda wani azababben kishi da taji ya tokare mata kirji, sama sama fatima ke iya magana, hira ta ki yiwuwa domin hankalin fatiman ba ya tare da ummin, Dr. Khalifa angonta ne kawai a gabanta shi take muradin kasancewa tarea dashi. ***** Tunda sassafe wasu yayyan innarsu fatima suka iso gdan duk da ba yau ne za a kai amaryar ba sai sati ya zagayo amma za su dafa abinci sbda 'yan'uwa maza daza su zo domin auran. Yaya kubura tace "Ina amaryar ne? Inna tace "Tana gdansu angon amma yanzu za tazo. Gaba daya suka rike baki sukece "wani irin tsarin banza da wofi ne haka? Yaya kubura ce tafi sauran fusata tace "Ni na taba jin irin wannan? yaya za ayi ace amarya na gdansu ango? Ke ba kya tsoron ace kwadayi ne yasa ta tattare a gdansu angon? Yaya rabi tace "ke kike wannan xancan kubra tun yaushe ake cewa kwadayi ne yasa ciki sati daya aka fasa bawa musbahu aure aka bawa khalifa don kawai babanaa yanada farcan susa, to ballantana yanzu ace tan gdan wai acan ma takwana, in barda zuvarwa kai daraja meye wannan? Inna tace "Ai ba wani abu yasa taje ba sbda kunshi ne da gyaran gashi. Yaya kubra tace "duk wani gyara ita batasan inda za taje ayi mata ba sai ta tafi yawon tallan kanta a gdan surukan, To Allah dai ya sawwake amma gskiya kidinga lura kuna jan mutuncin ku irin wannan abu ne ke sawa a dinga wa mutum gori daganan mutumci yazuve. " Inna dai tana jinsu bata sake cewa komi ba, itama kanta ba a son ranta fati takwana gdan su Khalifa ba mutumcin mama ne yasa ba ta iya musu da ita, sun nuna suna son fati daywa, hakanan fatima tasauya ra'ayin ta gaba daya akan Khalifa. Wuraren karfe takwas da rabi su fati suka shigo tare da ummi, tun kafin matar da aka dauka musamman dan tayi mata kwalliya tazo fati har ta fara daukar ido abin gwanin ban sha'awa, kowa yakalleta sai ya kara, fuskarta dai ce ta dan kumbura sakamakon rashin barcin da bata samu ta yi sosai ba a daren jiya, tsabar tunanin khalifa da kaunarsa da asuba ne bayan sun idar da salla tazauna jugum tayi tagumi. Ummi tajanye hannun na ta tace "haba matar yayana tunanin yayan ke damunki? Tayi mata wani irin kallo tadauke kai bata ce komi ba, ummi tayi murmushi tace "Ba kiyi laifi ba dan kin kasa sukuni akan dr. khalifa, ni na san tabaki yake yana dandana miki zuma a baki, shiyasa hnklinki ke tashi dayawa, fatima ba ki da laifi don kin damu da yaya Khalifa, bai dandana wa mace irin wannan zumar ba ta rikice akansa ballantana ke da yake nuna miki so irin haka har yana hada jikinsa da naki'. ***** Karfe goma sha dayan safiyar lahadi daruruwar alummar musulmi suka shaidi daurin auran Dr. Abubakar Saddiki Muhammad da Fatima Musa, daurin auran daya samu halartar manya manyan mutane tun daga kan manyan yan kasuwa da sunan su yayi fice a fadin kasar nan zuwa manyan yan siyasa da kusoshin gwamnati da jiga jigan malaman da ake ji dasu a jihar mu ta kano, hatta bangaran sarauta sun halarci daurin auran ballantana likitoci da abin yazama nasu maganin a kwabe su, maroka suka rinka yayata sunan ango da amarya da iyayansu yayin da gdajan rediyoyi ke ta bayyana yadda abubuwan ke gudana, sai shiga ake ana fita da nau'ikan abubuwan ci da na sha na alfarma daga gidansu dr. khalifa da gdansu inna. Angon ya sha ado ya yi kyau daya wuce misali, abin sai wanda yagani shadda ce mai tsadar gaske fara kal riga da wando da babbar riga sai akayi aikin babbar riga da blue din zare, hula kansa ma ya kasance fara da blue takalminsa blue, a ckin gda amarya fatima irin shigar ango aka mata fari da blue, ba a iya tantance wa yafi kyau tsakanin angon da amaryar kowanne ba baya bane ko ina masu hoto ne da bidiyo ke daukar ango da abokanansa sannan suka shigo gda tare don gaida iyayan amarya.. Gdansu fatima ma cike yake da mata anata rangada guda d sanya albarka, fatima ta zamo matar dr. khalifa rana ba ta karya sai dai uwar diya taji kunya, farar tukunya mai fidda farin tuwo, kirari iri iri maroka suke tayi musamman a gdansu khalifa inda anan ne ake facaka da kudi kamar ba nemansu ake ba. Abba yadinga kyautar muhimman abubuwa yana fadin "ai wannan rana ce ta farin ciki garesu ranar auran dansu daya. To fa. Ina su hajiya hauwa da hajiya saude kannan abba iyayan ummi? wadanda duk wani burinsu a wannan rana bai wuce ace da diyarsu ummi aka daura auran ba, amma hakan bai yiwu ba, khalifa da iyayansa basu damu da damuwar kowa ba sai ta su. Da farko basuyi niyyar zuwa gdan ba a yau daga bisani saude tace gara suje karshe a zo anayi damu ai idan baka iya kama barawo ba kai sai ya kamaka. Ba za ka iya shaida bacin ran dake tare dasu ba amma zuciyarsu fal bakin cki da takaici, da isowarsu a safiyar abba yaraba musu sabbin kudi rafa rafa yace suyi liki, duk da haka ransu ba dadi tunanin su shi ne da da ummi aka daura auran nan ai sun more irin wannan dukiya haka. Bayan gama daurin auren suka kebe a ckin wani daki, saude tadubi hauwa tace "ke wadannan mutanen ba na wasa bane sun fi mu shiri. Hauwa tace "Yo ba kiji abin da malam yace jiya ba? yace ai uban fatima ne yahada wani gagarumin asiri ya dabaibaye zuciyar khalifa yadda b ya son kowacce mce si yarsa fatima shiyasa muke tayin aiki aikin ya ki kama khalifa, yace. a wani lokacin yana so ya so ummi sai asirin yayi tasiri a zuciyarsa yakasa katabus yaji kamar ba ya da iko a kansa sai son fatima. Hajiya saude tace "Haba ko da
Chapter 39 · 0% Book details