← Book details A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 50

Sashe 33

A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zamanta a gdansu kada takoma gdansu khalifa wai a tunanin ta hakan zai sa hankalinta yakwanta, ta huta da bakin ckin dr. khalifa da fatima ke haifar mata amma ina lokacin da dare yayi dare sai taji hankalinta ya tashi sosai khalifa kawai take bukatar gani. Tabdijan ashe dai tana da jan aiki a gabanta ace duk sanda ba ta gdansu hnkalinta ne zai ding tashi haka, knan va za ta iya rayuwa ba sai tana ganin khalifa? ta mike zaune zaman ya gagara tamike tsaye anan ma tashiga sunturi ta dauki wayarta tayi kiran nomban khalifa bai daga ba bata san abinda za tace masa ba amma dai in taji muryarsa watakila tasamu tayi bacci ta huta, in dai a haka xuciyarta za ta tafi tana da babbar matsala. Takira nomban fatima bugu daya fatima tadaga tayi mata sallama da siririyar muryarta, tace "fatima bakiyi barci ba? "Eh banyi ba. "Meya sa? Tayi shiru. Tayi murmushi tace "na san tunanin dr. khalifa ne yahanaki bcci, don Allah haka ne. Fatima tayi ta maza tace "Na san kin san haka ne unmi shiyasa kika fada. Tayi ajiyar zuciya tace "fatima da ma na san ba za ki iya kaucwa soyayyar dr. khalifa ba duk da cewa a baya na mi? ce har ckin zuciyata za ki taimake ni a kan dr. khalifa to sai ga shi kema.... Haushi yakama fatima ta tabbata soki burutsun na rashin abin yi ne yasa ummi ke mata wannan shiriritar dan haka takashe wayarta. Mamaki yakama ummi ta jima tana kallon wayarta wai yau ita fatima ke ma haka, bata ma da lokacin saurararta, hakika ya zamo dole ta dauki mataki mai kwari akan fatima. Da gari ya waye da sassafe ta tashi tayi wanka ko tunanin cin abinci batayi ba tashirya tace da mahaifiyarta "na tafi gdansu khalifa. Hajiya na zaune a kicin tana suyar wainar fulawa tayi mata wani irin kallo tace "wai me ke daminki ne ummi, abin ci ma ba za kidinga tsayawa kina cinsa ba sbda khalifa? wannan wainar ma sbda ke nake yinta na san kina sonta amma ki ce tafiya za kiyi? Tace "don Allah hajiya barni in tafi hankali na a tashe yake ko barci banyi ba jiya. Tana tuka mota tana wasi wasi a haka har ta iso gdan masu aiki suka tarbeta da mummunar labari a asibiti dr. khalifa yakwana ba shi da lfya, tayi saurin kiran nomban mama tayi mata kwatancen asibitin dasuke tafigi mota ta nufi can. Hankalin ummi yakara tashi ganin yadda taga dr. khalifa mike isa gado, yana wani irin bacci wanda ga duk alamun bai san a inda kansa yake ba, mamane zaune bisa dadduma a kasa sadiya a gfenta abban na zaune kan wata kujera dake gefen gadon khalifa yazuba masa ido kawai. Ta tsyguna ta gayar dashi tare da jajanta masa ciwon khalifa ta zauna kusa da mama tana tambayarta "me ye musababbin ciwon ne? Mama ta tabe baki tace "katin daurin auren fatima yagani. Ummi tafiddo ido gabanta na faduwa tace "don ya ga katin daurin auran fatima yashiga wannan halin? Mama tace "kwarai kuwa tunda muka kawo shi asibitin nan bai farka ba har yanzu, nasarar da akaci dai nu; fashinsa ya dawo dai dai sabanin lokacin da muka kawo shi dan ko numfashi bbu, ni zatona ma ya mutu. Jikin ummi yakara mutuwa murus takoma jikin bango itama tayi shiru har tarasa abin da za tace. Wato wannan soyayyar har ta kai zafin haka, ina aikin da malamin su yace zai musu mai zafi wanda yaci musu alwashin zai raba soyayyar fatima da khalifa da ta duk wata diya mace sai ita ummin,. Amma abin mamaki kamar karawa dr. khalifa soyayyar fatima ake, me malamin nan ke nufi knan, aikain yake musu ko yaudararsu yake" Ta jinjina kai a baya kam ta san dr. khalifa yana son fatima haka yanayinsa yanuna, to amma yau ne yadada tabbatar da soyayyar nan ba ta wasa bace duk inda ake tunanin abin ya wuce nan,fidda soyayyar fati daga zuciyar khalifa abu ne mai wahalar gaske. Tadubi mama tace "to yanzu me likitocin suka ce? Mama tace "cewa sukayi a samar masa da abinda yasaka a ransa yana so din idan ana son rayuwarsa. Tace "to wani mataki aka dauka? Mama tace "har yanzu bamu san abinda za muyi ba. fatima dai tunda ba mu da ikon ba shi ita ai sai hakuri . Ta jinjina kai tace "To Allah ya sawwaka bari inje gda in kawo muku abinci ko zai farka ya bukaci wani abu. Mama tace "ga abin cin nan na asibiti an kawo. Tace "ai khalifa ba zai iya cin abincin asibiti ba bari dai in dafo wani abun. Lallai dr. khalifa ya yi nisa ba yadda za ayi yaji kira, gdansu fatima tafara shiga sai ita kadai a rmfar inna tana fama da waya, inna tana dakin malam suna hiran bikin fatima. Ta amsa sallamar ummi ckin fara'a tamkar ba wani abun, tukukin bakin ciki yakara turnukewa ummi zuciya, tayiwa fati kallon sama da kasa lokacin datake ce mata zauna mana anty ummi. Tace "ba zama nazo yi ba zuwa nayi in tamvayeki ina amsar taimakon dakika dauka za kimin a gun dr. khalifa.? Nan fatima tarasa abinda za tace tayi shiru, ummi tace "dama na san bbu abinda za ki iya cewa, tunda ba ki da abin fada din kinyi amfani da damar dakika samu kinja ra'ayin dr. khalifa har soyayyar dayake maki ta kaishi ga kwanciyar ciwo, to yana asibiti bai san inda kansa yake ba a dalilin ya ga katin daurin auranki da musbahu, sai kije ki duba shi kafin yakarasa mutuwa. Tajuya za ta tafi fati tajawo hannunta tace "Don allah ummi kar ki tai zauna ki taimake ni nasamu kaina a wani irin hali. Wani taimako zan maki fatima? ni van taimaki kaina ba wa zan iya taimakawa? in kura na maganin zawo me yasa batayi wa kanta ba?. Fati na kuka tace "ai rai ba ta rasa motsi ummi tasaya kiji. Ta jingina da bango tare da rungume hannayenta a kirjinta tana kallon fatima, fati tace "a wane asibitin khalifa yake? Tace "idan za ki wuce muje. Gaba dayansu sun rasa abinda za su cewa junansu kowacce tana neman taimakon 'yar 'uwarta ne ,unmi tace "tunda baki da abin fadi nima na rasa abinda zan ce miki kisameni a gda zan hadawa khalifan abinci sai muje asibitin, dasauri tfice daga gdan. Yayin da fatima tanufi dakin babansu ta durkusa tashaida musu cewa za su je karbar dinkin tada mama tayi musu na biki da ummi, sukace a dawo lfya. Ta sauya kaya ko wanka batayi ba tafice daga gdan, musbahu na kallonta tashige gdansu khalifa ba shi da ikon yi mata magana sai kallo, fatima ta fi karfin sa yanzu. Ummi na kicin tana ta hada abincin cikin gaggawa, fatima ta yi zaune a falo tana ta kallon hoton khalifa gabanta sai faduwa yake, wani babban hotonsa ne yakewa mutum maraba da zarar ka shigo falon, murmushi yayi a hoton murmushin dayayi matukar kayatar da fuskarsa, takagu ummi tagama su tafi taga halin da masoyin ta ke ciki. Bayan ummi ta kammala komi a mota tashiga dakinta da niyyar yin wanka ganin ta jima bata fito ba a fusace fatima ta bita ckin dakinta tashiga buga kofar toilet din tana fadin 'haba ummi wane irin jan rai ne haka? kinsan fa jiranki nake. Ummi tace "to don kina jira na ba zanyi wanka ba, karki dameni malama asibitin ma ganin damar kaina nayi ko kin sani ne ba sai da na gaya miki ba. Fatima tarasa me za tace da ummi don haushi, kuma karin haushi ne yasa bata kara ce mata komi ba sai da tagama abinda take a toilet,sannan tafito tafara shiryawa,fatima takara fusata a karo na biyu tace "ummi idan ba za ki rakani asibitin nan ba ki gaya min in yi tafiyata. Ummi tarausayar dakai tana murmushi tace "yi hakuri taso mutafi. A cikin mota tafiya suke kamar wasu kurame, kowacce da abinda take fama dashi a zuciyarta, da suka shiga harabar asibitin tasamu wuri tayi parking fatima ta tayata diban kayan abincin suka shiga dakin. Abba ne yakama fara'a yana fadin "fatima ke ce da kanki? Kunya da tausayi suka kamata lallai abba na cikin damuwa ta tsuguna tagayar dasu tare da tambayarsu mai jiki, Abba yace "to fatima mai jiki dai ga shi nan sai yadda Allah yayi, soyayya ce mai wahalarwa ya hdu da ita, sai dai hakuri. Mama dai shiru tayi tazuba tagumi tana ganin ikon Allah, magana in dai ta khalifa ce abba ba ya kawaici akanta, yaci gaba da fadin "fatima dubi halin da khalifan yake ciki har yanzu bai san wanda yake kansa ba, ni wlhi ban taba ganin inda akewa mutum irin son da khalifa yake miki ba, ga shi ba mu da ikon bayar dake gareshi, shin yaya za muyi da wannan tashin hankalim. Kukan fatima yafito karara tana juya kanta mama tace "Alhaji bai kamata kadinga fitowa da fatima irin wadannan maganganun ba sbda aikin gama ya gama alkalami ya bushe, hakuri dai khalifa zaiyi Allah yatashi kafadunsa. Cikin sanyin murya abba yace "ai nima ba wani abu nace ba. Fatima tace "Abba don Allah karoki babna ya janye mganar aurena da musbahu yana jin maganarka tare da girmama bukatarka, wlh nima khalifa nake so. Mama tarike hannunta tace "fatima mun san kina son khalifa Allah ne bai kaddara Khalifa mijin ki bane shiyasa duk abinda yafaru yafaru, wannan son zuciya ne karara idan har muka nacewa iyayanki da rokon su bawa khalifa ke,sbda shima musbahun yana sonki ba ya son yarasaki, idan mukayi amfani da wata dama da muke da ita muka rinjayi iyayanki suka ba khalifa auranki bamuyi amfani da hadisin manzon Allah dayake cewa imanin dayanmu ba ya cika har sai ya kasnce mun so wa yan uwammu abinda muke so wa kanmu, sannan na biyu mutane za su zagemu don a zahiri munyi rashin adalci mu mun san iyayanki basu hana mu auranki dan kiyayya ba sai dan girman alkawarin dasuka wa musbahu. Fatima takara rikicewa da kuka tana kallon dr. khalifa take cewa wallahi mama ba na son musbahu, khalifa
Chapter 33 · 0% Book details