Sashe 5
A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya 'kare mutuwa zakiyi fatima. Barrister kallon fatima kawai yake yarasa yadda xaiyi da tausainta a zuciyarsa, yamatso daf da ita muryarsa 'kasa 'kasa yace "fatima 'karfe nawa aka kaiki gidan Dr. khalifa? Ta amsa 'karfe biyar da rabi Zuwa shida a wannan d'an tsakanin ba'a wuce haka ba. Gaba d'aya sai da fuskokinsu suka nuna jin dad'in had'in kan data fara badawa, barrister yace a wace rana knan fatima? Ta amsa "A ranar lahadi biyar ga watan uku" Ya gyad'a kai yana murmushi yace "fatima suwa dawaye suke cikin motar da aka kaiki? Tayi d'an jim daga bisani tayi murmushi tana kallonsu tace "ummi za ta fini snin suwaye a motar da ka kaini sbda ni fuskata a rufe take ba wanda zan iya shaidawa a lokacin sai dai tabbas na san ina tare da manyan aminai na guda biyu kamar ita ummin da d'ayar aminiyar ta wa Jiddah. Barrister yace "yawwa ko za ki iya tuna 'karfe nawa kowa yawatse acikin gidan aka barki ke d'aya lkacin dakike jiran ango kamar yadda al'adar amare take a ranar da aka kaisu d'akunan mijinsu,? Tace 'lallai kam ba zan manta ba bayan an yi sallar isha'i wuraren 'karfe takwas nadare su ummi da maijidda dawasu 'kannan mahaifiyata biyu kad'ai suka rage a gidan inda mukai sallar isha tare dasu sannan sukayi shirin tafiya suka tafi gaba d'ayansu. Barristr yace "bayan haka waye yashigo gidan kafin zuwan ango dr. khalifa? " Tajima tsit tana nazari tace "gaskiya ba wanda yashigo kuma banji motsin kowa ba ni kad'ai nazauna. Barrister yace "zaman minti nawa kikayi 'kiyasi kafin dai zuwan ango ? Tace "tace ba'ayi minti sha biyar ba naji tsayuwar motarsu shida manyan abokansa guda biyu wad'anda sukayi masa rakiya. Barrister yace "kafin dai zuwan angon ba wanda yakiraki ko da awaya ne? Tagirgiza kai ba wanda yakirani in barda shi angon Dr. khalifa. Me yace miki? "Cewa yayi inyi ha'kuri suna hanya " Ke kuma me kika ce masa? Cewa nayi to Allah yakawosu lfya. Yace "dukda haka bakiji ko da alamar motsi a gidan ba har lokacin da dr. khalifa da abokanansa suka iso. Tagirgiza kai gaskiya babu wani alamun motsin danaji saifa lokacin dasuka shigo. "Su nawa suka shigo. " Barrister yaci gaba da tambayar har yanzu idanuwansa na kanta. Tace su uku wato shi da abokan na sa guda biyu. Yace "yaya sunayensu.Ta amsa "daya sunansa Dr. Mustapha kura d'aya Kuma Dr. Hafiz. B. Muhammad. " Yace kafin auranku yaya ala'karku dasu abokan na sa? ina nufin sun amshe ki a matsayin matar abokin su ko kuwa ba sa yi dake? Fatima tace "Nikam alhmdlh Dr. khalifa da iyayansa da abokansa da yan uwansa ko sau d'aya babu wanda yata'ba nuna min wata 'kyama ko wani abu wanda zai sa ince lallai wane ba ya 'kaunata, daidai gwargwado ina samun had'in kai daga garesu to sai shi kuma abinda yake na nasani mutum yakeda masaniya akai abinda yazamo na bad'ini Allah kad'ai ke da masaniya akansa sa sai dai mubarwa Allah ikonsa". Barristr yace "to fatima za ki iya gaya mana maganar dasuka yi lokacin da za suyi sallama daku a wannan dare? Tace "eh gaba d'aya tunda sukazo nasihohin zaman lfya suke mana bayan hka sun mana addu'o i na neman zaman lfya bayan haka sukayi mana sallama suna mana barkwanci irin na abokan ango ranar siyan baki irin wannan. To daga nan sai me yafaru? Tace "saiya rakasu" Ke kuma kina ina? Ina zaune akan gado ko motsi banyi ba kamar yadda suka sameni, bayan ya rakasu saiya dawo yazauna kusa dani yana d'an zolayata. Barrister yace "dukda haka a lokacin ba wani motsi a gidan sannan shi d'inma bai nuna miki ya ji motsin wani abu ba ko kuma ke kin fahimci wata razana a fuskarsa? " Tace "gaskiya banga komi ba yana cikin nishad'i sosai yadda yakamata ango yakasance a irin wannan dare. " Daga nan fa? Sai yace dani kinga hayaniya tayi yawa a kaina ko sallar isha'i banyi ba nayi 'ko'karin inyi kafin mutaho su mustapha suka daman akan inyi sauri su garin za subari a daran. "Garin za subari? inji barrister yafad'a yanayinsa yasauya. Tace "haka dai yace daganan kuma bai 'kara fad'ar wata magana wadda tashafi wad'annan abokai na S ba yatashi yafita bansan ina yaje ba saiya dawo. Ya yi kamar minti nawa dafita kan yadawo? Tace zaiyi kamar minti goma saiya dawo yacire babbar rigar jikinsa ya Ajiye kan gado yace ya kamata inyi sallar nan dashi kuma inajin yunwa tun d'azu anti take ce min ga abinci na ka sa zama inci sda jama'a gaba d'aya na ji abincin ya fita daga raina ba na sha'awarsa sai yanzu nakejin yunwa,amman bari inyiwa mama waya tasa akawo mana abincin hatta kazar amarcinki ma tana gun mama ita tace za tagasa dakanta akwai tanadin datayi miki a ciki. Duk yayi wad'annan maganganun ne a tsaye yana murmushi tare da daddana wayarsa tahannu yakira maman bayan sun gama wayar sai ya ajiye wayar akan madubi danufin yashiga toilet sai aka kirashi yayi magana mai tsawo dawanda yakirashi d'in sannan yakashe yadubeni yace "idan mutum yana harka da jama'a sai ha'kuri, tashi kema kiyi alwala idan nayi sallar isha'i sai muyi Nafila ko bari inyi tawa a d'akina sai intaho da littafina daganan saiya fice waje Nikuma nashiga toilet na idar da alwala na fito ne na iske gawarsa akan gado. Barrister yagirgiza kai cike da tausayi yace "fatima. " Yanayin fuskarta ba d'ad'in gani sbda tamkar lamarin datake bayarwa yana fama mata wani gyambo nazuciyarta wanda yake mata tsananin zugi a zuci yake rabata da duk wani zaman lfya da walwala a zuciyarta, hatta kallon datayiwa shi barristan lokacin daya kira sunanta ya firgita shi zuciyarsa tabuga yayi mata tsai da ido don yana son taci gaba da bashi amsar tambayoyin dayake mata. Yace "fatima kin kai minti nawa a toilet d'in lokacin da kika shiga danufin yin alwala. Tace "minti kamar goma don na d'anyi wasu abubuwan kafin in gabatar da alwala. To sai kika fito inda kika ga gawar mijinki Dr. khalifa shimfid'e akan gado, haka ne? Tace "eh ina daga band'aki naji motsin bud'e 'kofa sau biyu dakuma motsin bud'e kwaba ko me zan kawo a rainadon na ji wannan motsin, d'auka zanyi shi ne tunda ba kowa a gdan a iya sanina dagani sai shi. Yace "kuma ba motsin gudu? Tace "Gaskiya banji wani motsi wanda yake tabbatar da rashin gaskiya ba ko kusa. Yace "to bakiji 'karar mijin na ki ba ko wani abu da yayi kama da haka a lokacin da za a kashe shi? Tace "nidai banji komi ba yadda nagaya maka naga gawarsa haka nagan shi ba wani abu da na sani bayan wannan. Yace "dame aka kashe shi? Ta amsa "wu'ka ce 'karama. kin ta'ba wu'kar? Tace "eh lokacin danafito daga band'akin hankalina yayi mugun tashi natafi dagudu nad'aga wu'kar daga cikinsa domin wu'kar tana kan cikinsa ne bayan an luma masa sai aka zareta aka d'orata akan cikin na sa nikuma danazo saina d'aga wu'kar shi ne dai dai lokacin da 'kaninsa isma'il ya 'kwan'kwasa 'kofa jin ina ihu innalillahi wa inna ilaihir raji'un saiya danno 'kofar yashigo da food flask d'in abinci a hannunsa wanda mama tabashi yakawo mana. Barristr Abbas yace "fatima lokacin dakika iso kan mijinki dr. khalifa yanada sauran rai ko ya mutu? Tace "dasauran ransa don kuwa har yana d'an juya kansa yana cewa ta kasheni ta kashe ni har lokacin dashima isma'il yashigo d'akin yana magana ganin yanayin da ya iskemu aciki yasa isma'il d'in yawatsar da abincin hannunsa ya isa kan d'an uwansa a gefe ana fad'in, ya ya wa yakashe ka, yakasa hannuwansa daidai bakin dr. khalifan yana cewa don Allag gaya min wadda takashe ka nima yanzu inkasheta. Ban san yaya akayi ba ko shi Dr. khalifan a lkcn bansan waye a kansa yake masa magana ba ne ban sani ba naji Da kunnena dai lokacin Da dr. khalifa ke cewa Fatima ta kasheni, fatima ta kasheni. Fatima tayi shiru zuciyarta na bugawa kamar lokacin abin yafaru, daga barrister har malam da ummi dashi kansa d'an sandan dake tsaye a kansu sun ji'ke sharkab da gumi sbda tsananin tausayi da tashin hnkali. Idanuwan fatima sun 'kafe ba zancan hawaye sai tsananin zugi da rad'ad'i dasuke mata 'kirjinta kuwa kamar zai 'balle dan azabar zafin da yake mata numfashi na fita da'kyar. Tunda al'amarin yafaru yau ne ta iya bud'e baki tabada labarin yadda abubuwan suka wakana. Sun jima zaune shiru tuni lokacin daya dace sufita yawuce shi kansa d'an sandan ya kasa cewa sufita hnkalinsa shima a tashe yake.. Barrister abbas tagumi kawai yayi da tambayoyi a bakinsa, bakin ya yi masa nauyi la'b'bansa sun bushe da'kyar yake iya numfashi tare dacewa, shi cikakken lauya ne Kum 'kwararre mai cin gashin kansa don tuni ya jima da 'kasaita akan aikinsa sbda matakin daya ta ka nakaratu, irin wadannan abubuwan ba bakin al'amura bane gareshi, aikinsu nako yaushe jin abubuwan tashin hnkali amma bai ta'ba fuskantar alamarin dayake tsananin d'aga hankalinsa da ba shi tausayi irin wannan ba, ya damu da mGanar 'kwarai dagaske. Kafin ma yayi mata tmbaya taci gaba da fad'in "Abinda bakinsa ke furtawa knan har yabar duniya, wato ta kasheni fatima, takasheni Fatima. Isma'il yana ihu akansa yana cewa "yaya fatima ce takashe ka? fatima ce takashe ka? bai 'kara motsi ba yaci gaba da jijjigashi ko shurawa baiyi ba, tuni jini yayi faca faca akan gadon. Wu'kar tana hannuna ina tsaye har izuwa lokacin da isma'il yasake shi yafita baice min komi ba, ban ajiye wukar ba sai lkcin da yan sanda suka shigo d'akin wani acikinsu yalulku'be hannunsa da safa yakar'bu wu'kar daga hannuna. Tayi ajiyar zuciya tace "ba wani abu dana sani bayan wannan ,bbu kowa a gidanmu lokacin da aka kashe Dr. khalifa sai mu biyu a gidan ni da shi ni kaina na shaida banji motsin kowa ba, idan ba ni nakashe shi ba wa zance ykashe shi? Idan nace ba ni nakashe shi ba dole inyi bayanin wanda yakashe shi to waye? sannan ni akazo aka iske da wuka a hannu haka nan bakinsa gana furta takasheni ,idan akace wa sai yace