Sashe 25
A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
haka ? Ba kuka nayi ba wani abu ne yafada min ido. Tace "ina ummi ? Tace "ta fita ban san ina taje ba. Tace "ke ina za ki yanzun ? Tace "gida za ni yanzun xan dawo. Kamar zata hanata tafiya sai tayi tunanin bai dace ba batasan abin da za tayi ba don haka ta kyaleta tatafi tadawo falo tazauna. Dr. khalifa yashigo cikin shirin fita yazauna suka gaisa tace "ba za kaci abincin bane naga ka yi shirin fita ? Ya girgiza kai"ba zan iya cin komi ba xuciyata tana ckin damuwa bansan mafita ba a cikin halin danake ciki. Mama tayi murmushi tace "khalifa Allah (SWT) daya halicce mu cewa yayi "ban halicci mutum da aljan ba sai don su bauta min, to ni dai a ganina ba wani abinda zai dagawa mutum hankali akai in dai ba bautar Allahn nan ba, to ita kanta bautar Allah ba zafafa mana akai ba, Allah ba ya daurawa wata rai sai abinda za ta iya, in kuwa haka ne bbu abinda zai zamo mai tsanani a cikin wannan rayuwa ko meye shi kuwa, musanman ida mutum yana la'akari da rayuwar duniya, wadda fararriya ce kuma kararriya, duk wani abu dakasani dayake a cikin duniyar nan a dayan biyu yake, ko dai ka kare kabar shi ko shi yakare yabarka, to meye dalilin damuwa. Khalifa yayi ajiyar zuciya yace "mama na san za ki yi min shaidar hakuri da kau da kai a cikin al'amarin rayuwa idan yataso min, mama a wannan karon na samu kaina a yanayin dana kasa mallakar kaina, don na sa hakurar da zuciyata tayi hakuri da abinda take nema. Wallahi ji nake k ; ar zan mutu sbda ciwo fmda radadin da nakeji a zuciya ta. Mama tayk mai zumu da ido tana kallon fuskarsa, tabbas yanayin fuskarsa ta nuna tabbatar da abinda yake fada haka ne, tausayin sa yakamata amma tjure don kada ta dada karayar mai da zuciya tace "khalifa daman akwai abinda ba za a iya hakura dashi ba a duniyar nan ? a matsayin mu na musulmi munyi imani da cewa dukkan abinda yasa me mu haka Allah ya kaddara mana kuma ba mu da ikon kaucewa abinda Allah yakaddara mana ,kadaure kayi hakan mana. Yace "mama ba zan iya hakuri da fatima ba, don Allah ki taimake ni duk yadda za kiso alheri a gdan wanda za a ba auran fatima ba kamar a gdan nan ba. Mama ta jima kanta a kasa tarasa abinda za tace, Dr. khalifa yaci gaba da fadin "wlh mama babu abinda zan iya aiwatar wa a rayuwa ta in dai ina cikin wannan yanayin ni dai kisha min kan yarinyar nan da iyayanta ina matukar kaunarta. Tace "khalifa wace irin son zuciya kake son mu aiwatar ne ? don Allah kayi hakuri. Ya tareta dasauri yace "don Allah kada ki ba ni umurnin yin hakuri ina son fatima dayawa zan iya kowani irin hali idan ban mallaketa ba, ke za kiyi hakuri ki taimakeni ba wai ni zanyi hakuri ba waye zai iya hakuri da abinda yake so mama" Tace "ahi ke nan kabani kwana biyu zanyi tunani. Nan take mama tgano dalilin kukan da fatima ke yi knan, to kuma meye dalilin fitar ummi da safen nan ba tare da ta sanar dakowa inda za ta ba, ta kira wayar ummin a kashe takira hajiya hauwa ita kuma tana ringing ba a daga ba, ta aje wayar a gefe tayi tagumi tunani ya sha mata kai, shin yaya za ta yi da wannan al'amari, tana bukatar shawara, ko dayake duk wata shawara ba ta wuce ta lallashi khalifa yayi hakuri ba domin wannan son zuciyar ba yiwuwa zaiyi ba. Takira sadiya kanwarta dake tayata zama a gdan a dalilin mutuwar auranta tashaida mata abinda ke faruwa. Sadiya tace "tabdijam wannan ai babbar magana ce. Tace "to sadiya nima haka nagani, na rasa ta ina zan gano mafita. Sadiya tayi murmushi tace "to amm fa mama so so ne sonkai ya fi, tun kafin khalifa ydawo kasar nan idan nakalli fatima nakanji sha'awar ina ma itace khalifan zai aura, hakan yasa ba na so ma in ji ana hirar auranta me zai hana tunda dai khalifa ya nuna wannan damuwa ta sa mu san yadda za muyi ya aureta dama ance matar mutum kabarinsa wani bai auran matar wani. mama tagirgiza kai tace "kai anty sadiya anya wannan maganar ta yi daidai kuwa ? Sadiya tace "ta yi dai dai mana mama abinda yasa nace dake haka, idan khalifa bai samu auran fatima ba ba zai maida kansa kan aure ba sannan tunda ita yakeso in ya aureta hankalinsa zai kwanta sosai, yarinya ce mai hankali da natsuwa, gskiya mama kada muyi wannan sakacin daga karshe mu zo muna nadama. Mama takwantar da kanta bisa kujera idonta na kallon silin, sadiya ma ta zo da maganar daya cancanta a duba, abin ne da nauyi dole kam tsan abin yi in banda wannan matsalar ta fi kowa son khalifa ya auri fatima sbda fatima mace ce tagari to ya ya za tayi tadubi fati tace tafasa auren musbahu ta auri khalifa ??? ****** Tunda fatima tashiga gdansu bayan gaisuwa datayi da iyayanta bata kara cewa kowa kmi ba tashiga dakin innarta takwanta tana ci gaba da hawaye. Inna ta tambayeta damuwarta tagaya mata komi tace "tabdijam abin da malam ke gudu ne yafaru kin san shi Alhaji baban khalifan ya taba cewa yana son malam yaba dansa auranki yace ya riga ya ba da ke. Fatima tace "to ai inna ko da ba a bayar dani ba bazan taba amincewa khalifa ba, sbda aduniya dai banga da namijin da ummi ke so irin sa ba, ummi ba ta da burin daya wuce mallakarsa, ta kwallafa rai a kansa tana matukar so da kaunarsa. Matsayin ummi gareni ya wuce in yi mata haka, don Allah inna kada ki saurari maganar khalifa ba shi da tausayi bai da adalci. Tace "to ina ma za ayi haka ? dole yahakura. Fatima tadinga nacin kiran ummi a waya wayar a kashe take, dole taje ta lallashi ummi, ummi ta fi komi a gareta. Bayan sallar azahar tashaidawa inna za ta gdansu ummi tace sai ta dawo, ko ganin gdansu dr. khalifa ba ta son yi ,sbda takaicin ya cuceta ya hadata da babbar aminiyarta abokiyar shawararta. Tana tsaye bakin titin kan layinsu tana neman adaidaita sahu kawai sai ganin mota tayi ta yi fakin a gabanta, bakaken gilashin da aka zuge yabata damar ganin wanda ke ckin motar. dr. khalifa ne gabanta yafadi tsmatsa dasauri tana masa wani irin kallo, yace "ina za ki ne fatima. " Tayi shiru kamar ba da ita yake ba, yace "don Allah kigaya min inda za ki in kaiki. Anan ne ta hasala tace "ina ruwanka da inda za ni, ni ba neman taimakon mota nake ba. Yakashe motar yafito yana kare mata kallo daga sama har kasa, yana murmushi a wannan lokacin ne yadada tabbatarwa kansa yana son fatima kuma ba zai iya sakacin dazai rsata ba insha Allahu wannan yarinyar matarsa ce ta sunnah. Kwatsam adaidaita sahu ta tsaya a gabansu, ummi ce tafito idanunta fes akansu bata ce komi ba tabiya dan adaidaita kudinsa tawuce za ta tafi, fatima tabita tana fadin "ummi ai gdanku za ni Allah ne yataimaka bamuyi sabani ba. Ummi tajuyo suka hada ido ,kallon datake mata yana dagawa fatima hankali, tawuce dasauri tabar gun, ta tsaya sororo tabi ummin da kallo. Dr. khalifa ya iso gabanta yace "fatima don Allah ki tsaya ki saurareni, zuciyata tana matukar so da kaunar ki don Allah ki tausaya min. A fusace tace "ai kai ba abin tausayi bane, babu wani dalilin dazaisa a tausaya maka, tunda kaima ba ka tausayin mai sonka, tun yaushe ummi take fama da ciwon sonka a zuciyarta amma ka ki kadubeta kake walakanta ta sbda kawai tana sonka ? Yazuba mata ido yana murmushi wai shi yarinya kamar fatima ke wa tsiwa haka, son da yake mata ya yi tasiri da isarsa ta namiji ba zai yi komi a kanta ba, a iya rayuwarsa bai taba samun kansa a yanayi irin wannan ba. Tayi tafiyarta tabarshi a gun yana binta da kallo, gumi yana yanko masa har ta bace sannan yashiga motarsa yaja zuwa gdansu. Baiyi tunanin nan gdan na su fati za tazo ba sai yaganta za tashiga yayi murmushi kawai ,tafizge kanta tashiga ckin gda tayi sa'a mama ta fita anguwa sai 'yan aikin gdan suna hidimomin su, ta iske ummi a daki tana hada kayanta . Ta amsa sallamar fatin ba tare da ta kalleta ba, fatima tazauna a bakin gado muryarta a kasa kasa takira sunan ta, ta waiwayo tace,"na'am fati. Tace "ummi meye laifina akan wannan al'amarin lokaci daya za kijuya min baya ki tsane ni ? shin ni na budi baki nace ina son khalifa ? ko zuwa nayi sashensa naja ra'ayinsa don yasoni ? Ummi tayi mata wani lalataccen kallo tace "ke ki kama kanki, kin san dai ban tare ki dawata magana ba akan khalifa, don haka ba na bukatar kiyi ta nemana dawasu maganganu. Fatima tadaga murya tace "wlh ummi ko kusa bakiyi min adalci ba, na yi zaton a gun ki zan fara samu shaidar wani da namiji va zai taba samun masauki a zuciyata ba, ko ina son khalifa ko babu maganar musbahu a kaina ba zan taba ba, dr. khalifa fuska ba sbda na san waye shi a gunki, ballantana kwanaki suka rage a daura min aure, hakanan ba na son shi ba na ra'ayin shi to meye na damuwa, don Allah ummi kada kidauki alhaki na kada ki watsa mana zumunci ki kwantar da hankalinki insha Allahu ta hanya ta za ki iya mallakar dr. khalifa in dai Allah ya kaddara mijinki ne zan yi amfani da damar dana samu a kansa in ja ra'ayinsa gareki amma fa sai in na samu hadin kanki. Ummi tayi dif tan juya maganganun fatima wadanda sukan saurin fisgar hankalinta tadawo natsuwarta, idanunta da zafin kishi yasa suka rufe suka bude domin ta fara jiyo kamshin nasara a maganganun fatima. Ta taso tadawo kusa da fatin tazauna muryarta a hankali tace "kiyi hakuri