Sashe 44
A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yawuce dr. khalifa ko ? Na amsa mata "eh na sani ummi. Tace "To dr. khalifa shi ne matsala ta ko kin san cewa zancen auransa da fatima ya tabbata. Nace "to kiyi hakuri mana ummi, ni dai na san duk abinda ke faruwa Allah ne yahukunta hakan zai faru sai dai kiyi hakuri domin kuwa lamari na Ubangiji yadda yakaddara haka zai faru, cikar imanin musulmi yadda da kaddara cikin abinda yayiwa mutum dadi ko akasin haka. Ummi taja dogon numfashi tace "Jidda kina nufin in hakura da dr. khalifa ? duk lokacin dana bata ina jiran dawowarsa daga grmany ya tashi a bansa knan. Nace "Bai tashi a banza ba idan har za kiyi aiki da shawarar dazan ba ki, abinda nake so kigane shi ne idan zuciyar mutum tadamu da son wani abu kuma bai samu ba yadan gana ga Allah yayi hakuri, yakaddara cewa Allah ne bai kaddara abin nan da rabonsa bane to Allah zai dubi niyyarsa ya musanya masa abin nan da wanda yafishi, don a lokuta da dama mukan so abunda ba alheri bane garemu, abinda nakeso inkaiki gareshi ummi shi ne ki kaddara dr. khalifa ba rabonki bane a bisa abinda Allah ne yakaddara ba wani ba, domin wani ko wata bai isa ya kwace maka abinda Allah yakaddara rabonka bane, in dai kin yarda da haka to saikiyi hakuri na san abinda ciwo amma in kin daure kin yi hakuri don Allah, zai miki maganin damuwar ki, ance idan so cuta ne hakuri magani ne. Ummi taja dogon numfashi tace "jidda hakika shawararki itace akan hanya anma wannan hanyar binta ba zai yiwu ba idan nabita mutuwa zanyi. Nace 'Haba ummi ya ya za ace wanda yabi hanyar gskiya yamutu. Tace "jiddah ba zan taba iya hakuri da dr. khalifa ba idan kuwa nace zan hakura dashi to mutuwa zanyi. Nace "To ni dai kuma ban san abinda zan ce miki ba ummi ba ni da abinda zance sai dai kiyi &akuri. Tace "Ba zan yi hakur ba jiddah na yarda na rasa dr. khalifa amma yadda na rasa shi sai dai kowacce mace tarasa shi, babu macen da za ta moreshi. Na ce "ummi me kike nufi da fadin haka ? Kai tsaye tace "Kashe shi zanyi. A nan ne jidda tayi shiru. Yayinda jama'ar kotu suka rude da hayaniya ana fadin "Lahaula" wasu na salati, sai da aka tsawatar sannan kowa yai shiru. Mai shari'a ya dubi jiddah yace "kotu ta ji abinda kikace, akwai karin bayani ko shi knan hujjar ta ki ? sannan kuma akwai shaidar da za ki tabbatarwa da kotu cewa kunyi wannan magana da wadda kika kira ummi. Ta gyda kai tace "Ina da kwakwarar hujjah ya mai shari'a. Cikin rudani na tambayi ummi "kashe shi za kiyi ? Tace "Abinda kunnanki yagaya miki shi nake nufi tare da kara tabbatar miki da hakan kar ki dauka da wasa nake...... Na katseta nace "ummi an taba irin wannan maganar da wasa ? Tace "Yawwa gara da baki wahal da kanki gun shakkar abinda nafada ba. Nayi ajiyar zuciya nace "ummi meye dalilin da yasa za ki furta wannan maganar mai tada hankali ? Tayi dariya tace "na gaya miki idan har na rasa khalifa to sai dai kowa yarasa shi har iyayensa da kowa nas. Nace "amma lallai yau ummi na tabbatar ba ki da hankali kuma ba ki da tunani. Tace "in dai akan son dr. khalifa ne ba damuwa duk abinda za ki kirani kinyi dai dai. Idanuwana a makance suke babu abunda zan hango illa abunda nasa gaba zan aiwatar wanda shi nake ganin zai bani mafita, haka kunnuwana a toshe suke ba zan iya sauraron kowani nasiha ko gaskiya ba da ace zan vi hanyar gskiya wannan hanyr da kika nuna mini ba zan kauce mata ba tunda hanya ce ta hakikanin gskiya. Na marairaice murya "ummi bakin ki ne ke furta wannan kalma na ta'addanci ki ji tsoron Allah kidaina fada ni har kin sa tsoro ya kamani. Tabushe da dariya tace "kidaina damuwa jiddah babu wanda nataba fadawa wannan maganar sai ke, kuma na gaya miki ne sbda ke din sirrina ce babu maganar da ba zan iya gaya miki ba duk nauyinta kuwa. Nace "meye amfanin gaya min din tunda na ba k8 shawara kin ki dauka, har da bakinki kince abinda nafada gaskiya ne kiyi wa Allah ummi kiyi hakuri da dr. khalifa kada soyayyarsa tasa ki haukace, don ni na fara zargin kin samu tabin kwakwalwa ne, lfya kalau kike ba za kidinga furta wannan mummunan lafazin ba. Tace "Lafiya ce ta sani furta wa kuwa jidda zan kuma aikata. Na ce "to meye laifin khalifa don bai so ki ba, ana soyayya dole ? ke yanzu za a tursasa ki son wanda ba kya ra'ayinsa ? Tace "Nima bance miki dr. khalifa ya aikata min wani laifi ba, zan kashe shi ne don kowa yarasa shi sbda sun nuna min rashin tausayi shi da iyayansa sun san ina son khalifa amma lokacin daya dawo daga germany ya rikice akan cewa fatima yake so sai suka watsar da komi ba sa kallon kowa sai dansu suka fifita bukatar sa akan ta kowa aka bashi fatima sbda gata ana bukatar farin ckinsa, idan har khalifa zai kasance ckin fari ciki to basu damu da kowa ba da komi ba wannan ne dalilin dayasa zan kashe shi kowa yarasa. Nace "kai lallai ummi kin cika mara hankali, to na ji za ki kashe shi ba kya tsoron kema kar a kashe kin ? kinsan fa hukuncin wanda yai kisa kashe shi akeyi ko bakisan da haka ba. Dariya sosai tayi tace "na sani mana jidda ai ni mutuwa hutu ce gareni da akan rashin khalifa, ke bari in gaya miki wani abu matukar ina cikin duniyar nan ba zan bar khalifa yarayu da wata diya mace ba ne ko zan yi hakuri da auran khalifa ba dai fatima ba don fatima ta ci amanata ta yaudareni na gama gaya mata sirrin zuciyata da niyyar ta taimake ni tasama mini fada a zuciyar khalifa amma ina maimakon tayi min hakan ganin son da khalifa yake mata sai tayi amfani da wannan dama tabi hanyar data mallake zuciyarsa har yadinga nunawa tamkar zai mutu ne idan yarasat., duk fa fatima da khalifa sun san halin danake ciki basu tausaya min ba, jidda ko ke din nan bakisan sirrin zuciyata cikin abinda yashafi khalifa ba yadda fatima tasani, ta san ydda nake kwana ba na barci, ta san yadda nake kwana idona na zubar da hawaye, ta san yadda nake yini ba ci ba sha, duk sbda na rasa khalifa, amma fatima tashare tashiga fafutuka akanta, har sai data mallakeshi, ita kadai yake kallo, itace a gabansa, wannan shine dalilin dayasa nace yadda narasa shi itama tarasa shi. Nace "Don Allah ummi me zan gaya miki ki fuskanci cewa wannan kuskure ne babba za ki tafka ? duk wannan abubuwan da kike fada ba hujja bane wanda za tasa ki raba fati da khalifa ta wata hanyar m bllantana ta wannan mummunar hanyar, don Allah ummi kiyi hakuri. Tace "Jiddah karki bta bakinki da ace, zan iya yin hakuri da tuni na ba wa kaina hakuri. Nace 'na ji ki bi duk hanyar da za ki bi don ganin kin rabasu amma ba wannan ba. Tace "jidda kudimmu dayawa sun salwanta akan in raba fati da khalifa in ja hankalinsa sai yakasance ma kamar soyayyarta ake kara masa, babu wata hanya da za tayi tasirin rabasu sai wannan hanyar da zan bi, dole in bita kiyi hakuri kawai Nace "To naji tawace hanya xa kibi ki kashe shin ? ashe ke yar ta'addace ban bansani ba ? Tabushe da dariya tace "duk lokacin dakika samu labarin an kashe dr. khalifa, ni ummi ni na kashe shi, idan kin dawo kya ji bayanin hanyar da zan bi.... To nan ne takashe wayarta. Tun daga wannan rana ban sake samunta a waya ba, hankalina ya tashi sosai idan nayi yunkurin kiran wani sai in ji a jikina kamar ba da gaske ummi take ba ko kusa ban yarda za ta iya aikata kisan kai ba, to kada yakasance nafada ita kuma ba gaske take ba dana rasa yadda zanyi sai nayi shiru naci gaba da addu'a. Ba a dade dayin haka ba wata rana da safe wani matashi yazo gdan danake zaune a london yace sako ke tafe dashi yana son magana dani, nace "daga ina ? Yace "Daga kano, na zo miki da wani muhimmin abu amma na roki yazamo sirri a gareki. . **** Jiddah zaria,,, to ko wani sirri ne kuma wannan ??? A DAREN FARKO 37 Duk da cewa zuciyata bata kwanta da mutumin ba amma na daure nace ba kmai shigo muka zauna a falo yana duba na yamiko min wani memory card, nace "Na meye. Yace "karbi xan miki bayani. Na jima ina kallonsa sannan nace "kana tunanin zan karbi abinda ba ni da masaniya akan sa. Yayi murmushi yace "don Allah kar ki damu wannan abin ba zai taba zama abin cutarwa gareki ba face yazamo abin amfani na tabbatar ba za ki taba mantawa da zuwana ba yayin da kika fahimci muhimmancin wannan abin a gunki idan bukatar sa ta taso. Nace "to ai ni bansan daga ina kake ba, ban san meye a cikin sa ba ballantana in san dalilin daya sa ka ban shi, ka fada min mana idan kana son in karba. Yace "jidda kiyi hakuri dai ki karba wannan memorin ba wani ya shafa ba illa aminiyarki ummi. Yajefo min kan cinyata yamike tsaye yana cigaba da kallona yace "na daina lallabaki akan ki karba idan kin ga dama ki jefar dashi nidai ai na kawo miki, ina son kisani lokacin da ummi tayi miki wayatace za ta kashe dr. khalifa ina zaune duk wani bu da kuka fada yana ckin wannan memory daga bisani za kiga wasu muhimman abubuwa da xai miki amfani a ciki, in kuma har yanzu baki gamsu ba za ki iya jefar dashi. Yana gama fadar haka ya kama hanya zai fice, na dauki memodin jikina na rawa nabishi ina rokon yadawo yagaya min sunansa