Sashe 32
A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
baiyi ba numfashinsa yatsaya cak, abba yafita dagudu yakira mai gadi yace yazo sudauki khalifa ba lfya, mama da anty sdiya ma suka fito daga daki ganin yanayin khalifa yatashi hankalin kowa sun shiga dimauta, suka nufi wani asibiti mai zaman kansa har suka isa khalifa ko motsi abba salati yake yana fadin "shike nan Khalifa ya mutu akan son ftima na ga takaina. Likitoci suka amshe shi ckin gaggawa suka kaishi wani daki suka fara ba shi taimakon gaggawa, dakyar suka lallashi abba y tsaya a waje dan cewa yayi sai ya shiga dakin, gani yake kamar khalifa ya mutu, mama datake mace ma ta fi abba karfin hali, itatadinga ba shi baki tana nuna masa cewa ba mutuwa khalifa yayi ba, yadinga kai komo a kofar dakin ba likitan daya fito, yagaji yashiga buga kofar yana fadin "ku fito min da gawar khalifa na san ya mutu. Wani bakin likita dogo siriri yafito yaja hannunsa suka shiga dakin yaba shi kujera yazauna daf d gadon da aka kwantar da dr. khalifa yace "Alhaji duba kagani yana numfashi ko? Anan ne abba yayi doguwar ajiyar zuciya, ashafi fuskar khalifa zuwa wuyansa yaji sanyi kalau, numfashinsa yadawo normal amma lokaci daya yarame fuskarsa takara haske. Likitannan mesuna dr. mansur yadan rusuna kusa da abba yace"ka gamsu bai mutu ba ko? Yace "hakane amma nikam likita jikina na ba ni mutuwa zaiyi, khalifa ba zai yi dogon kwana ba a duniya... Dr. mansur yarufe me baki yace "haba alhaji ya za kadinga wadannan maganganun a matsayinka na musulmi? mutuwa daban ciwo daban, kayi hakuri mun sha kan matsalar khalifa dimuwa ce kawai takai shi ga shiga wannan halin in dai ku? yi kokarin magance masa damuwarsa shi knan komi zai tafi yadda yakamata. Su mama ma an ba su damar shigowa ita da anti sadia, gaba daya suka zubawa khalifa ido cike da damuwa jikinsu ya gama sanyi da al'amarin . Abba yagirgiza kai yace "hajiya wani irin tsari ne haka, shi knan akan mace mutum yadaga hankalinsa kamar zai bar duniya,ni wallahi har na rasa yadda zan bullowa al'amarin na khalifa tunda ga wanda iyayanta suka yiwa kawari na yi na yi yayi hakuri ya ki fahimta,ban taba ganin abinda khalifa ydga hankalinsa akan sa ba sai akan fatima, wacce irin soyayya ce wannan, daga ganin katin daurin aure. Mama tagirgiza kai tace "wallahi abba nima tunda khalifa yafara maganar yana son fatima hankalina a tashe yake, sbda yanayin daya ke nunawa abin fargaba ne, in an yi magana yace wai a kyale shi b a san abinda yake ji bane, to rayuwa za tatafi a haka, wani abun idan mutum yana so yana samu wani abun kuwa duk maitarsa da kaunarsa da abin ba zai same shi ba sai hakuri. To shi khalifa ji yake kamar ba zai ci gaba da rayuwa ba idan bai mallaki yarinyar nan ba,. Suka yi shiru kowanne idonsa kan khalifa, daga bisani abba yaja numfashi yace "wai yaya za mu bullwa lamarin nan ne? Mama tace "to yaya za muyi kuwa abba in barda muyi hakuri dole fa khalifa yahakura da fatima. Abba yace "kai hajiya a irin wannan yanayin, dubi fa yadda yake. Tace "to idan bamuyi hakurin ba ta karfin tsiya za mu ba shi fatima? ***** Ga dai lokacin biki ya zo gadan gadan amma gdansu fatima yanayin babu dadi domin kuwa ango da amaryar suna cikin damuwar dataja jikin kowa ya yisanyi babu mai walwala,Fatima ce zaune kan kujerar zaman tsakar gida da wayarta ta hannu ta kurawa sakon daya shigo wayarta ido zuciyarta na azalzala sako ne daga khalifa yace. Fatima soyayyarki xa ta hallakani bbu wani taimako daza kimin don Allah kiji tausayi na kada ki bari iyayanki su bawa musbahu ke wallahi na fi son ki fatima. Tagoge hawayen dasuka gangaro mata tayi ta maimaita sakon tana girgiza kai, ta tashi tashiga dakinsu tacimma katunan gayyata na biki da musbahu yakawo mata da la'asar din dazu, ganin idon katunan sun tsaru sun yi kyau amma ita bakin ciki ne yakara turnuke mata zuciya data gansu, ganin katunan yakara kusanto mata lokacin bikinta knan kuma lokacin rabuwarta da masoyinta dr. khalifa, kuma idan tayi wasa wankin hula na daf da kai mata dare. Shi kansa musbahun lokacin daya kawo mata katin sai da yabata tausayi, tana sallah yashigo yatsuguna bakin kofa kamar me neman gafara, data idar bata kalleshi ba tajawo pillow ta kwanta, a sanyaye yace "fatima ga katinan gayyatar. Tadube shi wani iri tace "to ajiye anan. Ya matso daf da ita ya ajiye, uace "ko kina bukatar wani abu daya danganci bikin? Ta ki magana sai da yayi ta mata naci sannan tace "Ni fa ba abinda nake bukata. Yace "shi knan sai anjima. Yamike yafita yayin da tabi bayansa da ido cike da takaici. Gabadaya dr. khalifa ya sauya mata yanayin rayuwarta, kafin dawowarsa tana zaune lafiya ba ta damuwa da komi babu abinda yake tayar mata da hankali sai daya dawo. Tun randa dr. khalifa yafara cewa yana snta bata kara samun kwanciyar hankali ba, gabadaya ya jefata a ckin damuwa da rudani kullum tunani, ta zamo abar tausayi akan kanta domin yanayin da zuciyarta ke ciki ba dadi, ba ta jin dain halin data sanya musbahu sbda babu abinda yayi mata, ya rayu yana tattalin abin da take so tun tana yar karama yake tattalin rayuwarta har maganar aure ta bullo a tsakaninsu, ya dauki son duniya ya daura mata kullum kamar zai lashe ta, ba ya son abinda zai daga mata hankali, kowa ya shaidi musbahu da kyawawan dabi'u ababan so ga kowacce mce, dari bisa dari ta amince da batun auransa, shi yasa bata tava kallon wani da namiji da sunan so ba, sbda ita dai yardar Allah kawai take nema a rayuwarta, bata taba damuwa da kyale kyalen duniya ba, bbu kwadayi ko son zuciya tsarinta, shi yasa tafiyarsu da musbahu yaxo daya svda shima akan wannan tsarin na ta yake tafiya. kowa yana kyautata zaton za su zauna lfya a dalilin kowannen su ya dauki rayuwa dasauki, iyayanta suna cike da murnar auran ba su da fargabar komi, sai da abin yazo daf dr. khalifa ya bayyana cikin rayuwarta shi knan zuciyarta tasauya. ***** A DAREN FARKO 28 Tana cike da jin nauyin musbahu, soyayyar dr. Khalifa ce take da karfi a zuciyarta shi yasa takasa tuna komi. A bangare guda da ummi, ummi ta taka muhimmiyar rawa a kanta ta hanyar nuna mata kauna da aminci na gaskiya takuma haifar da cigaba a rayuwarta, a daidai lokacin datake kokarin taimakon ummi don ta cimma kufurinta a kan dr. khalifa soyayyar khalifan yakama zuciyarta, wanda a wannan lokacin ne ta fahimci meye so tasan zakinsa da dacinsa kusan wahalar da zuciya ke sha akan ciwon so, tausayin ummi ya yawaita a zuciyarta domin ta dade tana fama da ciwon son khalifa, alhali ba ta da tabbas din komi a kansa, ga misali itama dayake son ta tanayin ciwo me zafi a rayuwarta na son sa ina ga ummi da ta tabbatar ba ya sonta ,kowannansu kam abin tausayi ne, ama dai ita ta fi zama abun tausayi tunda ita tana sa ran samun khalifa wani abu ne yake neman yi mata shamaki dashi, ummi kuwa dama tana sa rai ne tana cire ranta, tunda ta san bai karbi soyayyarta ba. Wannan shi ne tunanin fatima. ***** A bisa wani dan benci dake kofar gdansu fatima,musbahu ne zaune ya yi tagumi lokaci lokaci yana fidda nannauyar ajiyar zuciya wadda ke cike da damuwa da dacin rai,idanuwansa sun kada jawur ,yau so yake yi ma yayi kuka ya kasa, wai shin me ke faruwa dashi ne, da can bai fuskanci matsala da fatima ba sai yanzu, an ya ba mafarki yake ba, fatima ce tadawo ko ganinsa ba ta son yi, a baya ko yaushe in suna magana idan ya kutso mata maganar rayuwa takan bata rai tace ita kuwa me za tayi da wani namijin bayan ga zabin da iyayanta suka yi mata, ta kance k kwantar da hankalinka ba ni da abin da yafi iyayena in dai zuciyarsu za tayi haske to ni burina ya cika ba ni da damuwa . Ire iren wadannan maganganun suke ba shi cikakkiyar natsuwa da kwanciyar hankali, musamman a bisa la'akari da rayuwar fatima ba mai tsada bace in ban da haka kallonta kadai ya isa hnkalinsa yayi ta tashi sbda kyawun halittar da Allah yayi mata zai dinga jan hankalin mazan zamani kanta, to kuma si gashi abubuwa sun sauya a lokaci guda fatima tajuya masa baya khalifa take so, yadinga jin wani azababban kishi da takaici yana tafarfasa zuciyarsa kamar zaiyi hauka, iyakar tunanin sa bai san yadda zai bullowa al'amarin fatima ba haka zai aureta hankalinta na kan khalifa ya girgiza kai, inama sai da akayi auransu khalifa yadawo, da ba zai ganta bama ballantana yace yana sonta har yadaga mata hankali yadagawa kowa. Yashiga harar kwalla, sai yanzu yaji zuciyarsa ta yi masa dama dama daya samu hawayensa suka zubo, tabbas yana son fatima amma yanzu fati tsoro take ba shi "kukan me kake musbahu? A firgice yadaga kansa yadubi malam wanda yake tsaye a kansa yana kallonsa, yaci gaba da sharar hawayensa ba tre da y ce komi ba, malam yace "Biyoni ckin gida. Ckin sassarfa musbahu yake tafiya suka shiga dakin malam din suka zauna, yakara maimaita mai tambayar "kukan me kake? Muryarsa a dashe yace "baba ban san yadda za ayi in shawo kan fatima hankalinta yadawo kaina ba, ina jiyewa kaina tsoron abubuwa da dama game da fatima. Malam yace "musvahu ni ne fa na haifi fatima ni ne na yarje ma auranta, har a halin yanzu ina dada tabbatar maka da cewa in dai ranar daurin auran nan tazo ina raye ba zan daurawa fati kowa ba sai kai, to meye na tayar da hankalinka kan fatima in dai in dai tana ckin gdan nan tana karkashin ikn mu za a kaita gdanka kuma dole ne tayi biyayya gareka in har tana son zaman lafiya damu, ita kanta ta san ba na kwadayin abun duniya bana son zuciya a kanta kuma ba zan fa ra ba. ***** A son ran ummi tayi