Sashe 7
A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ina son kadinga Tunawa wannan yaron maraya ne kuma maraya ne a gareka, idan kaci amanarshi Allah ya tambayeka kamar yadda yazo acikin hadisin ma'aiki(SAW) ,sai ya tambayi kowa akan abinda yaba shi kiwo, maigida mai kiwo ne Allah sai ya tambaye shi akan iyalansa ya yatafiyar dasu.......... Ya katseni cikin hushi yace "Ni bance kayi min wa'azi ba tunda nan ba makaranta bace, ka ce za ka iya rike musbahu, ka ga gashinan kuje kukarata idan yagwada maka mugun halin sa za ka koreshi ne, da kai ka kama da sannu zan ganku a rana. " Nace "Insha Allahu ba za kaganmu a rana ba, kai ne dai za kayi nadamar abinda kayi masa, da sannu za kaga sakayyar da Allah zaiyi masa kuma da sannu za kagani watarana zai zama abin taimako gareka da iyalin na ka ma wadanda kuka hada kai dasu kuka walakantashi. A lokacin kawun musbahu yashiga dakin da musbahu yake kwana a zaure yadinga watso masa kayansa yana masifa a haka nataya shi mu*a kwaso kayan, wannan shi ne dalilin zaman muśbahu a gidan nan lokaci lokaci dangin iyayansa na uwa dana uba sukanzo guna suna yi mini godiya shi ma yana ziyartarsu. malam musa yaci gaba dacewa fatima lkcn dana gama tunasar da musbahu wannan lbri kansa na kasa nakara da fadin "musbahu lkci ya yi dazakayi aure shekararka ashirin da bakwai a duniya, kana bukatar ajiye iyali tunda kke baka taba cemin ga wata mace dakakeso ba sbda kunya dakake da ita da kawaici. Musbahu ka rayu kana hidima gareni vakin iyawarka, allah kadai yasan kaunar danake maka, wannan shiyasa nadauki diyata mafi soyuwa a zuciyata nabaka ita dan tazamo matarka uwar yayanka. Yayi saurin fadin fTima yana me dafe kirji da fiddo idb stories A DAREN FARKO 7 A babban falon alhaji aka sauki iyalan malam, falon da ba kamarsa a gdan duk wani kasaitaccan bakon da zai gana dashi a gidan nan yake sauke shi, aka kawo musu abubuwan ci dana sha na alfarma. Alhaji da hajiya maijidda suka fito aka gaisa, malam yagabatar dasu ga iyalansa aka shiga yi musu godiya mai yawa, alhaji hace "malam kwarai dagaske na ji dadi matuka da zuwanku gidan nan, sbda dama wannan gda ne na mutane ba mu da 'ya'ya in banda d'a guda d'aya da Allah yabamu amma idan kashigo koyaushe za ka iske mutane da yawa a gdan ko da yaushe muna godewa Allah kalar jama'a kam ba wadda ba ma gani a wannan gida sai dai a gefe guda banji dadin wannan zuwa na ku ba da sunan godiya don banga abinda nayi ba, wlh da ace malam za ka baiwa 'dana khalifa auran 'yarka da na yi murna duk dan kusan d'aya muke da kuwannan dukiyar da Allah yabani ba ta gabana ballantana har in ga wai na fi wani. Malam yayi shiru yana tunanin maganganun Alhaji muhammadu, shi kam vai taba burin kai diyarsa irin gida na aljahi muhammadu ba hakan yasa hnkalinsa yatashi sosai jikinsa yayi sanyi. Bayan sun dawo gida suna zaune a tsakar gida da da daddare zainabu tace "malam ai kuwa a dazu rukayya take ce min tunda alhaji yanemi aure a gdan nan mai zai hana abashi fatima. Sai ya bata rai yace "shi yasa hnkali na yatashi lokacin da alhaji yafurta wannan magana a gabanku, sbda ku mata ne karamin tunani gareku, tunanin ku ba ya wuce karan hancinku, ko da yaushe kyale kyale na duniya kan dauki hankalinku ku aikata abinda zuciyoyin ku suka raya muku sai daga baya azo ana nadama sbda haka ba na son wannan magana daga yau, shi yasa ko amsa ban ba wa alhaji ba lokacin da ya fada, ba na ra'ayin diyata tayi auran dukiya, idan alhaji ya kasance mutumin kirki mai taimakon talakawa sai akace muku shi dan na sa da sauran danginsu haka suke? da zaran mun dauki fatima mun ba su shikenan kowa ma cewa zaiyi kwadayi yakaimu ba za ace su suka nemi auran ba cewa za ayi ni ne nanemi khalifa ya auri fatima duk gorin da akanmu da duk walakancin da akayi mata mu muka jawo. Goggo Abu tace "kuma hakane fa malam bbu wanda yayi wannan tunanin acikinmu kowa kirkin Alhajin yake kallo. ************ Tun daga wannan lokacin aminci mai karfi da zumunci yashiga tsakanin mutanan da iyalansa da alhaji da hajiya maijidda a lokacin nan shi khalifa yana kasar germany inda yake karatunsa na likita. Alhaji bai da abokin shawara sai malam haka hajiya maijidda ta dauki goggo Abu kamar yar uwarta tajini, dukda cewa alhaji muhammadu bai ka ra nuna wa malam yana son yabawa dansa khalifa auran 'yarsa fatima ba tun daga wannan lomacin hankalin malam bai kwanta ba ba wai don yana kin alhajin ba, malam yana matukar kaunar alhaji har cikin zuciyarsa kamar yadda shi ma alhajin yake nuna masa kauna ta tsakani da Allah, auran fati ne kawai ba ya son yabawa khalifa sbda abinda zai je yazo. Bayan shi kansa alhajin akwai mutane wadanda suke da kima a idon malam suna nuna sha'awarsu akan malam yaba 'ya'yansu auran fatima sbda kamun kai na yarinyar da uwa uba kyawun halittarta bai taba furtawa wani ya ba shi ba, sai dai yayi dariya kawai yace aure nufi ne na Ubangiji. A ranar da alhaji yazo wurin malam da daddare bayan sun gama karatu da addu"o i yace dashi "malam idan Allah ya nuna mana rana itayau khalifa zai dawo daga kasar germany. Gaban malam yafadi amma bai bari alhaji ya fahimci fargabar da zuciyarsa ke ciki ba, ya fadada fara'arsa yace "masha Allah ya kammala karatun knan. Alhaji yace "kwarai kuwa karatu ya kammala lfya don ya samu cikakkiyar takardarsa ta shaida ya kammala karatun sa a matsayin cikakken likitan mata. Malam yace "mun godewa Allah, Allah yasa anyi a sa'a kuma Allah yadawo dashi lfya. " ***************** Shi kansa malam baisan dalilin dayasa hankalinsa yatashi sosai da maganar dawowar Dr. khalifa ba, tun da alhaji yashaida masa zancen dawowar yashiga damuwa sosai ko goggo Abu bai gayawa ba, shi kadai yake tunani a ransa karshen tunaninsa shi ne ba abinda yadace yayi wanda yawuce yaba auran fatima kafin dawowar Dr. khalifa ko da alhaji ya tada maganar idan yagaya mai ya bada ita shikenan an huta. Wannan ahi ne dalilin dayasa yadauki fati yaba amintaccan almajirinsa kuma d'ansa wanda yayarda dashi fiye dakowa,a 'ko'karinsa na ganin iyalansa sun zauna lfya a gidajan mazajansu, tun ranar daya shiga gdan alhaji yatabbatar wannan rayuwar ta fi 'karfin fatima ba za ta iya ba me zaisa yada'u d'iyarsa yakaita inda za tashiga wani hali rayuwar da mutum ya sabayi ita yake iyawa,idan yaje inda aka fi 'karfinsa wahala zai sha. ***************'Karfe bakwai daidai na yammacin litinin jirgin IRS yasauka dasu Dr. Abubakar Assadiq wanda aka fi sani da Dr. khalifa a filin jirgin saman Malam Aminu kano dake nan kano wanda yad'aukesu daga filin jirgin saman murtala muhammadu dake birnin ikko jihar lagos, bayan da jirgin da jirgin daya d'akkosu daga jamus ya ajiye su da asubahin wannan rana. Dr. khalifa dogon matashi ne kyakyawan gaske irin mazan nan da ko wace mace ke burin mallaka ba wai don shi da mahaifan sa sun mallaki abun duniya ba sai dan haduwarsa na gwarzon namiji wanda ya isa a kalleshi a san cewa shi d'a namiji ne abin kwatance acikin mazaje. Yana da madaidaiciyar 'kiba wacce tadace da tsawonsa ma'ana 'kibar da tsawon basuyi masa yawan dazasu sa shi muni ba. Babu inda yabar mahaifinsa alhaji muhammadu a kyau kamanninsu d'aya har tafiyarshi dai bambamcin halayyar abbansa mutum ne mai matukar kirki da sau'ki kai da son mutane yayin da Dr. khalifa yakasance miskili tun yana yaro bai da son magana sai dai 'kar'karfar mutum ne kuma gwarzo wanda ba shi da tsoro ko kad'an. Dr. khalifa ya taso cikin gata da kulawar iyaye bai san wani abu wai shi babu ba duk abinda yakeso shi akeyi masa, hakan ne yasa yagirma cikin izza da isa da raina mutane, sai dai yana raina wanda yashiga harkarsa ne, idan baka kalli inda yake ba ba ruwansa dakai, kuma bai ta'ba damuwa da yawan alherin dayake yi wa mutane ba idan ma Allah yayi mutum yana da rabo idan kazo neman abu gun abbansa sai yabaka abinda yafi wanda abban zai ba ka ma'ana dai shi kyautar sa taganin dama ce kuma sa'a ce. Bayan ya kammala karatun sa na secondary yafara karatu anan jami'ar bayero dake kano. Inda Allah yataimake shi shine dukda gatan da yakeda shi na iyayansa bai wasa da karatu kamar yadda sauran 'ya'yan gatan ke shagwaba suyin karatu sbda iyayansu suna da dukiya. Dr. khalifa tun yana nursery yake da kaifin basira wannan yasa yake da farin jini a gun malamansa har izuwa jami'a inda anan ne yazamo kamar jinjiri wata sha kallo sbda farin jinin dayake dashi, bayan dai tsabar kyau da iya dressing da Allah yahore masa. Kaifin basirarsa yana burge kowa sannan ga 'barnar dukiya dayake wa abokai maza da mata,shi yasa duk inda Dr. khalifa yake sai ka ga mutane ana wata irin shafta mai dad'i. A cikin Bayero 'yan matan dasuka shiga mawuyacin hali akan son Dr. khalifa Allah kadai yasan yawansu yayin dashi bai san suna yi ba, wasu suna ganin sbda dukiyar ubansa ne suke sinsa, kasancewarsa dan gata ahi kad'ai suka mallaka duk wannan tarin dukiyar da Allah yaba mahaifinsa shi ne mai mallakarta to kuma shi akwai 'ya'yan manyan masu kudi suna matkar sonsa, su ba abinda suke nema dashi sai shi kansa, shi mutum ne mai saurin d'aukar hankalin d'iya mace sbda Allah ya ba shi surar da mata keso wadda take burge su. Sai dai kash babu soyayya acikin ra'ayin Dr. khalifa, babi wata d'iya mace daya taba kallo yace yana ao da bakinsa wadanda suke nuna masa soyayyarsu ma share su yake kamar bai gane ba, a lokuta da dama har tambayar kansa yakanyi wai meye so? Ta yaya kake ganewa ka kamu da son wance? Shekarar sa hudu da kammala digiri dinsa nafarko a Bayero mahaifinsa alhaji muhammadu yace "yayi shirin tafiya germany inda yakeson yayi karatun zama cikakken likitan mata. Lokacin dayake gaya masa wannan magana suna zaune