Sashe 29
A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
magana? Fati tayi shiru takasa magana, inna ta jinjina kai tace "tabdijam amma kina da jan aiki fatima, da can wani namiji bai ja ra'ayinki ba sai yanzu, yau din nan fa za a fara rabon goron bikinki, to karkace kunnuwanki da kyau kiji idan ma son khalifa kike to kishiga taitayinki, kisan abinda kike, kinsan dai mu ba kwadayayyu bane duk abinda iyayan khalifa suka mana mun gode ba za muce bamu gode ba amma dai ba rokonsu mukayi ba ba za mu kai kammu inda Allah bai kai mu ba, dan mu tsira da mutumcin mu, ni kaina na gamsu duk abubuwan da iyayan Khalifa ke mana sunyi ne don Allah to amma mutanan dake gefenmu kallon kwadayi suke mana, kin ga dai su suka ja mu a jiki amma yanzu da zarar an ji wata magana ta fito fassarar kwadayin nan za a yi mana, sbda haka kisan abinda kike kada ki soma daukar dabi'ar da ba ta ki ba ki sa wa ranki wahala, kitsaya a matsayin da Allah ya ajiye ki sai ki zauna lafiya. Bayan fitar inna, fati tayi shiru tana tunanin maganganun inna, wadanda akan hanya da gaskiya suke, sai dai kash zuciyarta ta kamu da soyayya farat daya hankalin ta da tunanin ta sun dawo kan Khalifa, tana jin sa a ko ina a jikinta. **** Ummi da hajiyarta da hajiya saude sun dawo gida zuciyarsu cike da tabbacin abinda malam yagaya musu zai auku har tadinga jin kamar ma ta mallaki khalifan ne, sai fatima ce dai a ranta ita ke daga mata hankali. Takira jiddah a waya ta gaya mata abinda ke cigaba da faruwa. Jiddah tace "ummi in tambayeki mana" Tace "Allah yasa na sani. Tace "wai shin dama a baya khalifa bai taba wata budurwa ba sai fatima? mesa za ki daga hankalin ki haka akan fatima? bayan kina sane da cewa duk inda yake "yammata natare dashi. Ummi tace "ke jiddah tsaya kiji duk wata 'ya mace dake tare dashi ita ke nace masa bai damu dasu ba fatima kuwa shi yake sonta, tarihin rayuwarsa ba macen daya ke nunawa zai shiga kowani irin hali a k anta sai fatima, wannan al'amari yana matukar daga min hankali da ba ni tsoro jiddah. Jiddah tace "kai wani irin soyayya ce wannan? ko da yake fatin da khalifa duka ababen so ne, hakika ba abin mamaki bane dan namiji ya shiga kowani irin hali akan fatima, wannan yarinyar Allah ya hore mata kyau me shiga zuci, sannan khalifa Allah ya hore masa kyau na daukar hankali, fatima za ta iya kamuwa da son khalifa haka Khalifa zai iya kamuwa da son fatima fiye da duk yadda kike kwatantawa, amma shawar da zan ba ki itace kiyi hakuri kiyi hakuri idan Allahyakaddara fatima matar khalifa ce kiyi hakuri kiyi hakuri Allah yabaki wanda za kifi so fiye da son da kikewa dr. Khalifa. Tace "jiddah idan nahakura ya ya zanyi da son danake wa dr. khalifa? Tace "ummi tun a fari ni ce na sa ki a hanyar ki so khalifa, amma hakan bai hana a yanzu in ba ki shawarar kiyi hakuri da Khalifa ba sbda maslahar zuciyarki, ummi yanada kyau kisani duk abinda Allah bai kaddara makasamunshi ba ba za kataba samun na sa ba har abada sbda Allah ya kaddara ba rabonka bane, kitsaya akan wannan don ki zauna lfya. Ko kusa shawarar jiddah bata samu karbuwa a zuciyar ummi ba, domin abu ne da ba zai taba yiwuwa ba, ji take har gwamma ta sallamawa wata khalifa in da za ta iya yin hakan akan ta sallamawa fati. Su hajiya ma sun tsaya tsayin daka akan sai ummi ta mallaki dr. Khalifa ko da yake su dukiyarsa kadai suke kwadayi. Dab da sallar magriba ummi ta iso gdansu khalifa, ta iske shi suna alwala tare da dr.bashir ,ta tsaya suka gaisa abin mamaki fara'a ce karara a fuskar khalifa yana fadin "yawwa kanwata daman ina son ganinki, bari in dawo daga masallaci. Ta shige gida cike da zargi iri iri a zuciyafmrta, musamman ganin yadda fatima tadaina neman ta ko da a waya ne, tabdijam ckin dakin mama tafara shiga ta iske ta ta tayar da sallah ita dayake ba sallar za tayi bata watsar da jakarta da mayafinta tazauna gefen gado tayi tagumi. Mama ta idar da sallah tazuba mata ido tace "sai yanzu ? Ta sauko kasa suka gaisa tace "mama yaushe rabon fatima da gdan nan ? Tayi murmushi tace "ai fatima ta dauke kafarta daga gdan nan ne sbda mun zamo surukanta. Tace "kamar yaya mama ? Tace "uhm kina nufin baki san meke faruwa ba ? Tace "mama idan ma na sani ina bukatar karin bayani daga gareki. Mama tace "ummin hankalina a tashe yake domin abbanku ya goyi bayan son zuciyar da khalifa yazo dashi karara bayan ya san hakan bai cancanta ba. Bakin ummi na rawa tace "mama kina nufin abba ya goya ma khalifa baya ya auri fatima. Tace "wannan shi ne damuwata. ina tsoron kallon da mutane za suyi mana musamman kasancewar musbahu talaka khalifa me kudi abin da kowa zai ce shi ne anyi amfani da dukiya gun dannewa musbahu hakki don ba shi da dukiya, ya kamata abba ya takawa Khalifa burki yanunamasa jan ido tunda ba shi za ya daurawa kansa auran ba, dole yahakura amma ya ce ba xai hana shi yin abinda ba ya so ba ina jiyewa khalifa rayuwar da abba yasa shi bai san bbu ba bai san yanemi abu yarasa ba sai dai duk abinda yanema sai ya samu, wace irin rayuwa ce wannan ? idan khalifa bi san rayuwa ba yanzu sai yaushe zai sani ? Cikin nauyin baki da takaici ummi tace "mama to ke kin amince ? Ta amsa "to yaya zanyi ummi ? ina da ikon yiwa abba musu akan wani abu daya tsara akan khalifa ? Ummi tajinjina kai a zuciyarta tace "gaba dayanku kunyi kuskure wato cikinku babu wanda yadamu da damuwata sai damuwar danku ? Hakika son zuciyarku da kanku ya zame muku damuwa daman ance son zuciya bacin ta. Tabude baki za tayi magana wayarta tafara ringing, khalifa ne tadaga yace da ita "taho mana da abinci mana dakina. Ta tambayi mama abincin na su tace yana kan tebur. Wani iri ummi take jin zuciyarta kamar ba ita ba, tadauki abincin tanufi dakin na sa, bayan ta zauna Khalifa yace "ina kawar ta ki ? Tace "fatima. Yace "eh. Tace "ai ina zaton a halin yanzu ka fini sanin inda take tunda ka fi ni kusa da ita. Yace "um um ummi ba haka bane kina da matsayi babba a gun fatima koyaushe tana maganarki da kokarin ganin ta nema miki mafitar da za ta haifar maki da kwanciyar hankali,kada wani abu yarufe miki zuciya ki zargeta da abinda bai dace ki zarge ta dashi ba. Gaba daya taji takaici da bakin ciki sun kara rufeta maganganun sa kara mata damuwa suke, meye amfanin abunda yake fada mata kan ftima, tamike da niyyar tafita yakira sunanta yace "zauna. Takoma ta zauna tana kallon sa yace "ummi ya zamo dole in miki godiya domin kin taimaka min akan fatima, zuciyarta ta karkata a gareni ta amince ta amshi soyayya ta duk da cewa wasu abubuwan suna firgitata wadanda sune suka hanata sakin ranta sosai tabani hadin kan daya dace, ina miki godiya ne ummi sbda kin taka muhimmiyar rawa akan hakan. Tayi masa wani irin kallo cike da mamakin abinda yake gaya mata, ba ta son tayi kuka sbda lokacin kuka ya wuce gareta, ta dade tana kuka akan khalifa lokaci ya yi da za ta daina kuka, don da ace kukan zai mata maganin damuwarta da ya yi abinda yadace da ita shi ne tanema wa kanta mafita kawai ko ta wani hali, tadubi khalifa tace "a takaice daikwalliya ta biya kudin sabulu fatima ta amince da soyayyar ka ko ? Ya amsa "eh hakane abu guda daya zuwa biyu ne damuwarta ke da musbahu tana jinjina yadda za ku kalleta, shiyasa nakiraki yanzu dan in roke ki kinunawa fatima ba komi kuma kisaki ranki sosai da ita kamar yadda kuke rayuwa a baya, yin hakan ne kawai zaisa ta kwantar da hankalinta tabani hadin kan danake bukata. Kai khalifa da wauta yake. Abinda ummi ke fadi a ranta knan ko da yake gani yake ya fi karfin komi tabbas khalifa ya rainata, shi yasa ko wani irin danyar magana sai ya tareta da ita to kuwa za ta shayar dashi mamaki daga shi har fatima da iyayansa masu son zuciya. A fili kuma dubansa tayi tace "karka damu zanyi yadda kace. Yayi murmushi yace "nagode ummi zan miki kyauta mai ban mamaki". A DAREN FARKO 25 Tsakiyar dare ummi ta kasa barci tana tuna abubuwa iri iri ta saka wancan ta kwance, tun tana ganin auran fati da khalifa ba mi yiwuwa bane har nesa tafara matsowa kusa, abinda ya faru da karfe goman daren yau ne yatabbatar mata da haka. Wato ta zo za ta shiga dakin mama ta tsinkayi muryar mama da anty sadiya suna hira da daga murya soai, anty sadiyance take fadin "to wai mama idan Allah ne yakaddara fatima matar khalifa ce fa ? kin san dai babu wanda ya isa ya shirya wannan al'amarin sai Allah ko ? tunda ita kanta yarinyar ta amince to meye na damuwa ? kin san babu yadda za a yi abba ya sauya ra'ayinsa, kada ki jawo abin da zai zamo na rigima. Mama tace "haba sadiya yanzu ko a hankalce wannan ya yi dai dai, da kunyar son da ummi ke masa zanji ko da malam musbhu. Anty sadiya tace "duk ki kwantar da hankalinki ki kaddara cewa Allah ne yakaddara faruwar hakan ki toshe kunnuwanki daga duk wani surutun mutane idan kika biyewa mutane babu wani abun alherin dazaki kulla a rayuwarki, ki kyaleshi ya aureta Allah yasa haka shi yafi alheri itama kuma ummi Allah yabata wani haka shima musbahun. Abin da ummi taji mama tafada ne takara tsinkewa da al'amarin cewa tayi "sadiya ni ma na fi son Khalifa ya auri fatima fiye da kowacce mace, sbda tarbiyyarta da nagartarta, na san inaha Allahu