← Book details A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 50

Sashe 27

A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yatsaya mata a rai shi ne hawayen khalifa da kyakyawan murmushinsa,dr.khalifa ya zamo namijin farko dataji lallai tanason taji ta a jikinsa sbda burgetan da yyi. Ta kwanta bisa gado tayi luf, a lokacin ne ummi tashigo dakin da zumudin jin yadda sukai ganin kwanciyar da fatima tayi da yanayin jikinta yasa gabanta yafadi sosai. Ko dai khalifa ya fara wa fati tasiri a zuciya, a sanyaye tzauna daf da ita muryarta cikin wani irin yanayi tace "fati yaya akayi naga kin zama wani iri. Fati tayi firgigit tamike zaune idnuwanta a waje tana kallon ummi tace "an samu nasara domin kuwa ya fara amsa min zai min duk abinda nake bukata. Ummi tayi ajiyar zuciya "fatima lallai idan kika ceci zuciyata daga halin da take ciki kin yi taimako. Tadafa kafadarta tace "ba komai kidaina yawan damuwa. ****** Tsakiyar dare ummi takira jidda dake londn ta fayyace mata abubuwan dake faruwa, jiddah tace "Dr. khalifa na son fatim Tace "kwarai kuwa jiddah soyayya kuma ba gama garin soyayya ba original one, domin kuwa tunda yadora idonsa a kanta gaba daya ya rikice ya rasa sukuni, kin san dai yadda khalifa ba ya sakar min fuska ko ? To a halin yanzu sbda in masa kamfen a gun fatima za kiyi mamakin yadda yake ja na a jiki ko kunyata ba ya ji. Jidda tayi ajiyar zuciya tace "anya kuwa umi ko dai dr. khalifa tsammani yake son wasa kike masa. Tace "haba jiddah wani irin wasa kuma, da dai ace mun saba wasa ni dashi to zaiyi tunanin haka, mutumin da bai min ko kallon arziki za kiyi mamakin yadda yasauya akan son fatima abin har tsoro yake ba ni jiddh. Ta jinjina kai tace "to yanzu wani mataki kika dauka akansu ? ko kin hakura dashi ? In hakura jiddah ? Tabdijam ai idan kika ga na hakura da khalifa to numfashin karshe nayi a duniya, ma'ana rayuwata ta kare amma idan ba haka ba matukar ina numfashi ba zan hakura da doctor ba. Jiddah tace "to ummi ta wce hanyar za ki mallakeshi bayan kin san ko da akewa maza auran dole a wani lokaci ba za ayiwa dr. khalifa ba. Tunda kinfi kowa sanin cewa mahaifinsa yana fifita shi akan komi yana kara akan komi banda khalifa. Ummi tace "eh nima bance za ayi mai auran dole ba kawai dai ba zan bar ma wata shi ba. Jiddah tace "ko da fatiman ta ki ta aura ? Tace "wannan ne abinda yafi daga min hankali ban so yakasance dr. khalifa fatima yake so ba sbda kaunar da nakewa fatima ba na son wani abu na bacin rai ya sameta, in da nake dan samun natsuwar zucia shi ne fatima ba son dr. khalifa rtake va, bayan kasancewar saura kwanaki kadan a daura auranta, fatima tanada burin biyayya ga iyayanta shi yasa bata kula kowanne da namiji, wannan yanuna kwanciyar hankali. A DAREN FARKO 22 Gaban abban yafadi ras yayi wa dr. khalifa wani irin kallo yace "ai an kusan bikinta da musbahu. Yace "na sani abba ai aaure nufi ne na Allah idan matata ce sai kaga.... Ya katse shi yace "kai khalifa wannan abu ne da ba xai yiwu ba nima na so auranka da fatima domin yarinya ce mai hankali da sanin ya kamata,to amma ta ina xanje in ce a fasa ba musbahu aure a ba ka, gskiya sai dai kayi hakuri Allah yabaka wata. To shima khalifan ya san abun da nauyi soyayyar dayake mata ne yasa yarufe idonsa yakeso ya mallaketa kota wani hali, bai ka ra cewa ko ; i ba, abba ya bishi da ido jikinsa gaba daya yai sanyi ba ya son dan na sa yanemi wani abu yarasa a rayuwarsa. Nan da nan yanayin abba ya sauya ganin damuwar da ke tare da khalifa, yamike yashiga dakin mama, tamike dasauri daga kwanciyar da tayi tace "daman ka fito Alhaji ? Fuskarsa ba walwala yace "na fito, khalifa ne yazo min da maganar data dagan hankali. Mama tace "uhm Allah yasa ba maganar fatima yakawo maka ba",. Ya dada bata rai yace "af daman kinsan da zancen baki fada min ba ? Mama tace "to Alhaji idan na fada maka me za kayi !? abinda zai yiwu ahi ake, ta yaya khalifa zai samu auran fatima idan kuwa ba zai samu ba meye amfanin tattauna maganar. Alhaji yazauna gefen gado yana fadin "to haka za mubarshi a ckin damuwa hajiya ? gaskiya ba zai yiwu ba. Mamaki yakama mama ganin yadda abba ke neman rufe ido kiri kiri yayi son kai, tace "alhaji gskiya sai dai hakuri domin ni da kaina naroki yarinyar tanuna min gskiya ba zai yiwu ba,ni abinda ke hadani da Khalifa shi ne idan yakallafa ransa kan son abu ba zai iya hakura yabi abin a hankali ba, sai dai ydga hankalinsa yadaga wa wani hankali. Abba yace "ba dole yadaga hankali ba, in bai gaya mana damuwarsa ba wa zai gayawa, kin san zafin soyayya kuwa ? Tace "hakane ban sani basai ka nema mai auran nasan dai sai da amincewar yarinyar da iyayanta za ayi ko ? Abba yace "Gaskiya ba zan bar yaron ckin damuwa ba, dole in bi duk hanyar dazan bi don ganin na samar mai dafarin ciki a rayuwarsa. Yajuya yafita yayin da mama tabishi da kallo cike da takaicin yadda abba ba ya son nunwa Khalifa yadda rayuwa take. **** Fatima ce zaune a runfar innarta ta yi tagumi ta kasa cin abincin dake gabanta, innar tana dakin malam, sauran kannanta duk sun tafi makaranta, musbahu yashigo da sallamarsa, tadaga ido ckin ladabi ta amsa muryarta a sanyaye tace "ina kwana. Idanuwan daya kafa mata yasa tayi kasada kanta yazauna kusa da ita yace, "fatima a kwana biyun nan kin sauya kamar ba ki da lfya sai ramewa kike ko dai fargabar auran ne ? Ya fada yana dan murmushi a kokarinsa na kwantar mata da hankali, itama murmushin tayi tace "lafiya kalau. Yajawo abincin gabanta yafara ci yana fadin "kai abincin nan yayi dadi da yawa na san ke kikayi. Bata ce komi ba, yaci gaba "gaskiya fatima Allah ya yi miki baiwa da yawa shi yasa zuciyata ke kara sonki don Allah nima ki soni kuma kidinga tausaya min wahala zan sha idan nasamu sauyi daga gareki. Anan ma shiru tayi masa don bata san abinda za tace dashi ba, wani iri takeji a jikinta ko kallonsa ba ta iya yi, yace "ftima don Allah kiyi min magana ko zanji dadi mana kin san ina sonki. Fatima bansan abinda zai same ni ba hakanan nake jin zuciyata tana cik e da fargaba idan nakwanta bacci kuma sai in ta mafarkai barkatai marasa dadi wanda yafi daga min hankali shi ne wanda nayi yau da asuba wai wani ya kwace min ke ta karfin tsiya, shi ne jikina duk yakara sanyi. Ga mamakin ta sai taji hawaye ya taru a idonta, tatashi dasauri tashige daki tace dashi "ina zuwa . Misbahu yabita da kallo har yagaji dazama yatashi bata dawo ba bai san meke faruw aba baiyi tunanin binta ckin dakin ba yafice daga gdan. Itama inna data shigo dakin kallon mamaki tabita dashi ganin yadda take saharar kwalla tace "lfya fatima? Tace "ba komi inna Ba komi kike kuka? Takasa magana domin itama batasan dalilin kukan na ta ba ballantana ta bayyanawa inna, inna ta jima a tsaye tana kallonta daga bisani tadaga kai tafita . Wayar fatima tafara ringing tadauko ta bakuwar lamba ce, tadaga tare da sallama, daga can bangaran aka amsa mata "Khalifa ne. Gabanta yafadi "ko baki fahimci khalifan bane? "Na fahimta. "To ai na ji kinyi shiru. Tace!"bansan abinda zan ce bane. Yayi dariya "za kisani yanzu kuwa, so nake kizo mugaisa tun da natashi idanuwa na ke son ganinki zuciyata na azalzala min da yawa don Allah kidaure ki zo. Tace "haba khalifa meye ma'anar zuwana gareka? me ganin zai haifar maka, me yasa kke mantawa na kusa zama matar wani ne.... Ya katse ta. Don Allah kidaina gayamin wannan maganar ki daure ki zo muyi wa kanmu maslaha. Shi knan a ina zan sameka? 'Yawwa tawan ina kofar gdanmu ckin mota ta. Hijabi tasa wanda yazo har kafafunta ydda idanunta ke kode sunyi ja haka tafita bayan ta shaidawa innarta cewa za ta gun ummi.. Ta wuce musbahu a kofar gda tare da wani abokinsa mai suna Aminu, khalifa yana hangota ya bude mata kofar motar tarike kofar tana kallon sa tace "idan na shiga mota ina zamu? ko a cikin motr za muyi magana? Yace "inaso kiyi min rakiya wani wuri. ne ba nisa. Ta waiwaya tadubi musbahu ita yakafawa ido, ta dawo da idon ta kan khalifa tace "kn ganin hakan y dce? "Eh ya dace mana kowa ya sanba na satar mutane, Fatima maslaha muke nemawa kanmu ina bukata kema haka in haka ne ki shigo mutafi. Bbu abinda ummi ke kallo sai rayuwar ummi wannan ce damar da zatayi amfani dan tallafawa ummi, sai ta zuke fargabarta tshga motar tarufo. . Ta gabansu musbahu, kbalifa yawuce idon ta ckin na musbahu taji gabanta ya fadi an ya ta yi dai dai kuwa. Gdan dr. bashir yanufa da fatima, matar dr. bashi ta asheta hannu biyu zuwa falonta takawo musu abinci da shayi, dr. khalifa yahada tea yafara sha, dr bashir ya harare shi "wato haka Za kadinga son kai ko ita amaryar fa. Don Allah ku rufa min asiri ina tare da matsaloli ko yanzun ma na biyo shi ne domin in fahimtar dashi. Farida tahada mata shayin taja hannunta zuwa ckin daki tace "fatima don Allah dagaske ba kya son Khalifa? Fatima tawaro ido tace "me son na shi xai amfana min, a rayuwata bbu abin da na tsana irin in yi abu in dawo ina nadama. Farida tace 'dr khalifa yadaga hnkli akan tsananin sonki, da za ki amsa soyayyarsa xa ki mori rayuwar aure, irin su tsada garesu. Fatima tace kin san kyaun mijin daxan aura da halayansa? an masa adalci in nabarshi na auri Khalifa? aminiyata na tsananin son khalifa ya kamata in watsar da batunta in aure shi? abinda khalifa ke nunawa fa son kai ne kuma ba dabi'ar
Chapter 27 · 0% Book details