Sashe 45
A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kuma yayi min karin bayani don ba karamin rikitani yayi ba. Yace "Babu wani bayani dazan kara miki, jin sunana kuma ba ya da amfani gareki a yanxu tunda dai kikaji nafadi haka kin san wannan memorin yanada amfani gareki, kiyi hattara ki kiyaye kada ki bude shi sai bukatar hakan ta taso. Iya abinda yafada min knan yafice yabarni tsaye da memory card a hannuna jikina na rawa. Jidda tayi shiru. Kowa ma a kotun shiru yayi ana kallonta, masu rubutu na yi masu nazari na yi. fatima na tsaye kyam inda aka tsaida ta ko motsi ba ta yi ba, kallon dakowa yake wa jidda itama shi take mata. Ummi kuwa da kai tsaye ita abin yake shafa tana zaune tadaura kanta bisa cinyarta itama dai bata motsa ba, mutanan da basu sn ita abin yashafa ba basu kalleta ba iyayan marigayi dr. khalifa da iyayan fatima fatima da wadanda suka san itace umin da ake nufi sun dawo da kallonsu kanta, ina zaton shi ne dalilin daya sa ta sunkuyar da kanta bata dago ba, to ama dayake hankalin mutane na kan jidda da mahukunta suna son jin yadda al'amarin ya kaya sai basu motsa da wani abu ba suka fuskanci jiddah don jin yadda za ta kasance cikin wannan al'amari mai ban mamaki, aka ba ma jidda umarnin taci gaba bayyana labarin datake bayyanawa, tadora da fadin. Bayan tfiyar wannan mutumin nazauna shiru ina tunanin al'amarin nayi shawarar in bude wnnan memory a wautata in ga meye a cikinsa, haka kawai sai naji tsoro ya kamani, kamar wadda akayi wa dabaibayi nakasa budewa kuma nakasa bayyanawa kowa al'amarin, nayi masa ajiya mai kyau har zuwa lokacin danaji gabaki daya na kasa samun natsuwa idan nakwanta bacci sai bacci ya gagareni, in kuwa nasamu barcin zan yi ta fama ne da mafarkai masu ban tsoro, dole tasa nabaro london ina ckin karatu na nadawo, a ranar dana dawo din nasamu lbrin an kashe dr. khalifa lamarin daya tayar mini da hankali sosai, nana da nan natuno hirar da mukayi da ummi a waya wanda tun daga wannan rana ban sake samun ummi a waya ba sannan itama bata sake kirana ba, a wannan lokacin ne nadakko wannan menoryn nabude naga abinda ya kunsa. Jidda takara tausasa lafuzanta cike da ladabi tace "ya mai shari'a wannan memorin shi ne shaidata dukka abinda nafada yana ciki. Mai shari'a yabada umarnin akawo na'urorin dazasu haskawa dukkan jama'ar da ke gun abin da ke cikin memorin, nan da nan aka kawo jama'a suka baza idanuwa cike da mamaki, har lokacin ummi bata daga kanta ba kuma babu wanda yayi mata magana. Abinda allon talabijn din yafara nunawa shine ummi ce tsaye a wani guri ita kadai, ta sha ado tayi kyau dayawa ,wani matashi yabullo ta bayanta yace "ummi gani na zo. Ta waiwayo tadubeshi tana murmushi tace "sannu dazuwa yaya. Yayi murmushin shima yace "yauwa ummi ya akai naga fuskar ki ckin damuwa ? Daga gani wani abu yana damun zuciyarki, gaya mim ko meye zan taimake ki in dai zan iya. Tayi murmushi tace "na san za ka taimakeni yaya shi yasa na fiddo maka damuwata, duk da cewa magana ce nazo maka da ita mai tsananin nauyi. Yabushe da dariya yace "kada nauyinta yadameki maganar dakika iya dauka nikuma sai ta gagreni ? Dubeni da kyau fa ummi. Ta jinjina kai. Yaci gaba da fadin "ummi tun lokacin dana ganki zuciyata take bala'in son ki, kina ta shareni kin ki ba ni hadin kai, kin sha walakantani a gaban yarana ina kyaleki, kowa na mamakin yadda naki tsayawa in dauki kwakwaran mataki akan ki, na san ke da kankikin san kina yaudarar kanki ne kina ganin kamar kinfi karfi na ne shiyasa ban dauki mataki akan ki ba, ba haka bane ummi da ace na yi niyyar rabaki da rayuwarki gaba daya da yanzu na gama dake, da ace na yi niyyar dauke ki in boye da yanzu na yi, amma dayake duk ba wannan manufar ce a zuciyata ba na sa miki ido duk dacewa kullum kwanar duniya azabtuwa nake da soyayyarki, Allah ne yasa min sonki a zuciyata ba tare da manufar komi ba face in aure ki, ban taba sha'awar auran diya mace ba sai ke, tun daga ran da na ganki sai naji kawai ina sha'awar ace na gina gda na ajiye matar aure nima ta haifa mini 'ya'ya yadda maza keyi sai gashi ban samu hadin kanki ba. Aka hasko fuskar ummi tayi murmushi tace "ba komi ka kwantar da hankalin ka yaya lokaci ya yi da za kasamu hadin kaina yadda kake bukata. Yace "Za ki aureni ummi ? Ta amsa "zan aureka in dai kai min wani aiki shi ne sharadin aurena da kai. Yace "wani irin aiki ne wanann ummi gaya min shi komi wahalar shi zanyi in dai zai sa ki aureni, aurenki shi ne cikar burin rayuwata a duniya, ba ni da bukatar komi domin na mallaki dukiya, mace sai wadda na zaba in yi amfani da ita, ke kadai ki ka tsaya mina zuciyata ba na son bata miki rai na fi son in aureki in zauna dake a matsayin mata ta, yanayi ne daban taba fuskanta ba a rayuwa ta. Unmi tace "wannan damuwa ta ka ta zo karshe in dai kayi min abinda nakeso zan mallaka ma kaina a matsayin matar aure. Yace "To fada min meye wannan aikin ko zan rasa raina zan miki. Tayi murmushi tace "Akwai wani mutum mai suna Abakar ana cemasa dr. khalifa. Shi nake so kawai ka kashe mini in dai khalifa yabar duniya kazo a daura mana aure. Yavushe da dariya mai karfi yace "shi knan ko da wanda za akashe bayan shi ? Ta Girgiza kai "shi kadai ne ba na son gani a duniya. Yace "an gama yaushe kike son a kashe shi ? Tace "A DARANSU NA FARKO da amaryarsa kuma ina so a kashe shi ne ta sigar da za ayi zaton ita amaryar ta sa ce takashe shi, in dai kayi min haka ka biya dukiyar auran ummi. Yasake bushewa da dariya yace "in dai kisan kaine ko ta wacce hanya mun iya ta sai dai in bamu sa kammu ba. To daga wannan shafin sai aka hasko dakin da aka kai fatima, fuskar ummi ce ta bayyana yaya na binta a baya tabude mai murfin kwaba yashiga. Sai kuma aka hasko ummi t shiga daya murfin kwabar ta rufe. A wani shafin kuma an hasko fuskar dr. khalifa ne ya bude kofar kwaban da yaya ke ciki, sai ga yayan ya fito tsulum ya tsaya gaban dr. khalifa cikin zafin nama yadamke masa baki ya hantsila shi kan gado yasa filo yadanne bakinsa. Sai aka hasko fuskar ummi ta fito ta maida murfin kwaba ta rufe ta hau kan gadon da karamar wuka a hannunta ta nunawa dr. khalifa daf da kunnansa takai bakinta tace "Ni ce ajalin ka. An hasko fuskar khalifa yanata wutsil wutsil bashi da damar magana. Sai kuma aka hasko yaya ya amshi wukar hannun ummi ya chakawa dr. khalifa sau biyu, sai suka fice daga dakin suka rufe kofar shi da ummi. Bayan wannan, Sai akaga fuskar yaya a zaune kan kujera unmi na gefensa yace "Aiki dai ya kammala kuma ya yi kyau ummi ya batun aurammu ? Ummi ta harareshi tace "wai kai meyasa ba ka da hankali. Yaya yazaro ido "Ni ne ba ni da hankali ummi ? Tace "To ina kaga hankali. Yayi murmushi yace "Ni kuwa nake da hankali. Ta girgiza kai tace "babu rashin hankalin daya wuce kace kai dinnan kanada hankali kai daman ka yarda zan aureka ? Ya kura mata ido yace "ummi ni kikawa haka ? kin san waye ni kuwa ? ki guje shiga cikin hadari. Tamike tsaye tace "shi yasa nace ba ka da hankali kamar ni in rasa wa zan aura sai dan ta'adda, ko ka manta kai dan ta'adda ne, ka gaggauta fiddani daga zuciyarka domin bazaka taba samuna ba. Yayan yamike tsaye yanuna ta da yatsa yace "kin yi babban kuskure ummi sai kinyi da na sani da kika mini domin baki yaudareni ba illa kanki. Ta kyalkyale da dariya tace "yaya ba zan yi da na sani ba har abada domin ka mini aikina dr. khalifa dai ya mutu kuma ba zai dawo ba buri na knan yadda na rasa shi kowa ma yarasa ka ga zancan nadama ma gareni bai taso ba, in kuma za ka kashe shi ne to bismilla. Yace "Ba zan kashe ki ba sbda na yi alkawarin ba zan kashe ki ba ummi amma xan ba ki mamaki daman jikina ya ba ni za ki yi min wannan butulcin shi yasa na shiryawa hakan, kin z hannu ummi. Daga wannan ranar ba za ki kara yaudarar wani a duniya ba, idan ma kin ci gaba da rayuwa ni daman nawa ta kare. Iya abinda memorin ya kunsa knan TV tayi dif kamar yadda kotun tayi shiru kamar ba kowa duk da yadda tacika makil da mutane, abin mamaki har yanzu kan ummi na kasa bata dago ba. Bayan wani dan lokaci mai shari'a yadago kansa bayan ya ajiye biron da yake rubutu yace. "Kotu ta gamsu da bayanan da jidda tazo dashi tare da hujjojin dakowa yagani a zahiri, don haka ba tareda bata lokaci ba nan take wannan kotu ta sallami fatima kuma ta bada umarnin a kawo ummi da wanda yakashe khalifa, shari'a ta dawo kansu wannan yakawo karshen zargin da akewa fatima na kisan mjinta Dr. Abubakar Saddiku a bisa kwararan hujjoji na shari'a. A DAREN FARKO 38 Karfe takwas na dare agogo ya nuna, malam musa mahaifin su fatima na zaune kan tabarma da rediyo gefensa yana jin shirin iya ruwa fidda kai da akeyi gdan rediyon kano. Inna tafito daga dakinta tazauna dab da shi tce "malam ni fa lamarin nan na fatima ya dameni. Yarage sautin rediyon idanunsa na kanta yana mata kallon rashin fahimta yace "me kuma yafru ? Tace "ka ga yau satin ta biyu da fitowa daga kurkukun nan amma har yanzu ta ki daina kuka idan an tmbayeta sai tace wai babu komi, ni abin nata har