← Book details A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 50

Sashe 24

A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bai damu da lallaba mama ba ya san tana sonsa da tausayinsa, ummin ce dai matsalarsa kuma ya amince ta hanyar ummi zai iya cimma nasara.. Wannan shi ne dalilin dayasa da gari yawaye yanufi kitchen ya san ummin ce ke dafa abincin safe a gdan ga mamakinsa sai yaga gimbiyar ce a kicin din... Yakatse tunaninsa anan yadawo da ganinsa ga ummi wadda tayi tagumi tana goge hawayenta wadanda tayi kokarin tsaida su suka ki tsayuwa takyalesu suyi ta zubar lokacin su ne. Ummi" Muryar dr. khalifa ya ratso kunnanta da sassan jikinta tadago kai suka kalli juna tace "Na'am". Ina son ki yi min wani taimako daya za ki iya ? Idan bai fi karfina ba insha Allahu zanyi maka, fada min inji" Ummi "inason kawarki fatima. Inason in aureta za ki iya taimaka min ki ja min ra'ayinta a fasa ba musbahu auranta a bani ? Wai shin mafarki ne wannan ko gaske ? Dr. khalifa datake tsananin so ne yake gaya mata da bakinsa cewar fatima aminiyarta yake so ya aura har yana neman ta taimakeshi. wane irin raini khalifa yake mata, wani irin cin fuska ne wannan ? Hawayen idanuwan ummin suka kara ballewa tashiga kuka kamar ranta zai fita, Dr. khalifa yace "ummi idan ba za ki iya taimako n ba kitashi ki ban guri. Tace "ya ya khalifa ba ka da tausayi kuma baka san darajar soyayya ba, baka san ciwon so ba, da ka san zafi da dacin rai dake cikin ciwon so da baka nufeni da wannan maganar ba, ka san yadda nake ji a zuciyata kuwa ? tamike tsaye idanunta tazuba kansa wadanda suka kada jawur tana huci tace "khalifa na sani ba ka so na, ba zan yi maka dole kaso ni ba, kuma ba zan taba bin wata hanya don kaso ni ba,, ni kam ina sonka son da ba zan taba dainawa ba, abu daya nake son tabbatar maka wanda shi ne ba zan taba barwa wata kai ba sai dai kowa yarasa ni kam na ami ? ce na rasaka.... Amma ba zan hakura ba. A fusace tabude kofar tafita, yabiyota dasauri yasha gabanta ya sausauta murya yace "haba ummi kitsaya ki fuskance ni da kyau mana na yi miki alkawarin zan miki duk abinda kikeso matukar na mallaki fatima. Murmushi tayi masa tace "ka yi kuskure babba doctor daka fuskance ni da wannan maganar. Ta zagaye shi tashige cikin gida. Abba da mama ne kawai a falo suna breakfast, tashige dakin dasauri dan ba ta son sukalli idonta. Ba karamin faduwar gaba fatima tayi ba ganin ummi ta shigo tana kuka, tamike tariko ta tana tambayarta lafiya ? me khalifan yayi miki ? Ta ja hannunta suka zauna tana goge mata hawaye, ummi tace "ummi babu abinda dr. khalifa yayi min fyace ya shaida min cewa yana sonki yana son in taimake shi yasamu auranki. INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. fatima kefadi muryarta na rawa tace "bai san an kusan bikina bane, ke ko ba a kusan biki na ba ina ni ina shi. Wani irin abu ummi taji ya tokare mata zuciya, kirjinta yamata nauyi, kanta ma yashiga sarawa nan da nan taji jiri ya fara dibarta, tadaure tatashi tadauki hijjavinta tayi sa'a abba da mama sun shige daki tafice daga gdan taja mota sai gdan mahaifiyarta. Hajiya Hauwa na barci ummi tafada jikinta tana kuka mai tsanani, a rude hajiyar tatashi tana tambayar lafiya lafia ? Wa ye yamutu ? Tace "hajiya na ga takaina na shiga uku, wai khalifa ne yau din nan yakirani yana shaida min cewa ba macen da yake son aura sai fatima. Yana son in taimake shi yasamu hadin kan fatima. Hajiya tace "yawwa abinda nake gayan miki ya auku ko ? ai lokacin da muke gaya miki gani kike ba zai taba yiwuwa ba, bayan mu munsan faruwarsa abu ne mai sauki, idan kika kalli fatima da tsarinta mace ce da maza ke burin mallakar irinta, ta yaya khalifa yana ganinta a gdan zai hadiye maitarsa. Ummi kuka take tana karawa fargaba da takaici sun sa ta kasa samun abinda za tace yayin da hajiya ke ta fadace fadacenta inda take shiga ba nan take fita ba, takira hajiya saude a waya tace "kinga abinda muke gudu saida ya auku, taurin kan yarinyar nan zai ja mana asara. Bayan saude ta saurari abinda ke faruwa daga bakin hajiya hauwa tace "kujirani za mu yi maganinsu dukkansu wannan karon sai mun bude musu wuta duk tsawon lokacin da muka dauka ya tashi a banza knan ? wannan abu ne da ba zai taba yiwuwa ba. Ba afi minti daya ba hajiya saude tayi dirar mikiya a gdan tadubi ummi tace "kukan banza da wofi idan mutum bai aiki da shawarar na gaba dashi yana tare da nadama, gun malam za mutafi yanzun ba za mu rangantawa khalifa ba. Hajiya hauwa ta tabe baki "ba sai in za tayi abubuwan da aka ce mata ba. Tace "to kada ma tayin batayi ba ta isa tazo tana mana kuka anan ? Har suka isa gdan malam din kuka sosai ummi takeyi ita takaicin ta ace dr. khalifa yarasa wa zai so sai aminiyarta fatima, tunda su hajiya suke gaya mata abin da zai iya fruwa ganin take bazai taba yiwuwa ba ashe kuskure tayi babba, hajiya hauwa da hajiya saude ke ta tattaunawarsu kan matsalar ita kam ta sunkuyar da kanta tana tunanin yadda za takasance in har fati ta amshi soyayyar dr. khalifa koda yake abu ne da take ganin kamar zaiyi wahala sbda koyaushe fatima na tabbatar mata da cewa bbu abinda zai hana yi ma iyaynta biyayya, tanayin wannan magana ne idan wasu daga kawayensu suna cewa"kyaun halittarta ya fi karfin ta auri malami almajiri irin malam musbahu wanda ba wayewa a tare dashi, to anan ne take tabbatar musudacewa "malam musbahu ya fi kowanni namiji a gunta tunda shi iyaynta suka zabar mata dole tayi iyayya gasu sbda yardar Allah take nema a cikin al'amuranta ba wai kyale kyalen duniya da abinda ke cikinta ba. Ummi tana cigaba da gasgata abubuwan da fatin ke fada ne ganin yadda bata kila kowani irin da namiji duk matsayinsa, hakan ne yasa ummi ta tabbatarwa kanta cewa ko dr. Khalifa yadawo ya ce yana son fati bazata amince da batunsa ba, sbda akidar biyayyar iyayanta data sawa zuciyarta to in dai haka ne ma me zaisa in daga hankali na ? Ta tambayi kanta in dai fatima bazata amince da dr. Khalifa ba me zaisa ta tayarwa kanta hankali, to a daidai lokacin da wannan tunanin ke tasiri a zuciyar ummi har tafara jin saukin zafin da zuciyarta tadauka sai kuma dai wani gdfen na zuciyarta yafara tunasar da ita cewa fa dr. Khalifa kyakyawan namiji ne ga ilimi ga naira, mata kuwa ba abinda suke so a gun da namiji wadanda suka wuce kyau da naira ballantana abin yahadu da ilimi da wayewa, kadan ne suke la'akari da addini da kyawawan dabi'u, fatima kam tanada banbanci da sauran matan zamani, iya zaman ta da ummi ta tabbatar za ta mata wadannan kyawawan shaidar a ko ina fatima ba ta da kwadayin abin duniya don da tanayi da dr. khalifa bai dawo yasa meta, wannan tunanin duk yake kara kuna a zuciyar ummi sunada tasiri mai karfi don ta tabbatar da hakan. Ummi na wannan dogon tunani ne kafin malam yabasu damar shigowa, hajiya suka shaida masa abinda ke tafe dasu, yajawo wani rairayi dake bayansa yafara zane zane yana tambayarsu wasu abubuwan dasuka shafi dr. khalifa da fatima da iyayanta. Malam yajinjina kai yace "hakika khalifa ba karamin so yakewa fatima ba, kai hasalima bai taba jin son wata diya mace a ransa kwatankwacin yadda yake son fatima ba, kuma ya yi dammarar auranta ko tawani hali. Wannan bayanin na malam yasa ummi tunani kamar kirjinta zai tarwatse sbda faduwar gaba, hajiya hauwa tace "to malam yanxu knan khalifa ba zai auri ummi ba, kuma kana ganin auransu da fatima mai yiwuwa ne dukda cewa an kusan bikinta ? Malam yace "to ni dai na gaya muku abinda nagano tar da khalifan ne, batun yiwuwar auransa da ummi idan kun bi abubuwan dazan tsara muku anyi an gama, fatima kuwa zan fatattaki soyayyarta ne daga zuciyarsa, amma gskiyar magana ba aiki ne mai sauki ba. Hajiya saude tace "malam indai za asamu nasara wahala mai sauki ne kuma me wucewa ne me ake bukata ? Malam ya gyara zama yace "dafarko kamar yadda nagaya maku a baya za ku kawo min kasar da khalifa ya taka, za ku kwao gashin kansa da hankicinsa da hularsa da hotonsa, za ku biya kudin fararan raguna guda uku, jajayan akuya guda uku, jajayan zakaru bakwai, sauran abubuwan kuma mu za mu samo su, kudin aiki dubu dari, ku zuba ido za kuga aiki da cikawa. Suka tsaya akan cewa bayan kwana biyu za akawo duk abinda aka bukata har kudin, suka dawo gda da shawarar yadda za asamu kudin dasuka kama har kusan dubu dari biyu, a karshe dai Alhaji muhammad mahaifin dr. khlifa aka buga wa waya suka mai karyar cewa asibiti za su yace zai aaiko musu da kudin dama sun saba dahaka duk abinda suka bukata zai musu iya ikonsa amma ba sa gani, su dai matarsa da dansa ne ba sa so dashi kansa sai dai dukiyarsa A DAREN FARKO 20 Fitar ummi yakara dagawa fatima hankali sosai takifa kanta a cinyarta tana sharar kwalla, meyasa dr.khalifa zai mata haka, ya ya za ayi yarasa wadda zai fadawa cewa ma yana sonta sai ummi wannan ba karamin cin fuska bane da walakanci, duk abinda zai sa ummi tayi hushi da ita abin ya yi yawa ko da yake ta san dole ne ummi tayi fushi da ita akan dr. khalifa, ba wanda ummi ba za ta iya juyawa ba sbda son datake masa ba kadan bane, ta gaji da kukan bakin ciki da takaici tatashi a sanyaye. zata tafi gda taci karo da mama a harabar gida tana magana da ado me musu wanki da guga, yanayin ta da mama tagani yasa tayi saurin matsowa daf da ita tace " 'yammata lafiya ? kukan me kikayi
Chapter 24 · 0% Book details