← Book details A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 50

Sashe 26

A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fatima a cikin gaba daya al'amura na ba na wasa da dr. khalifa sbda soyayyar danake mishi, ban taba jin za a wayi gari watarana inji ba na san na budi ido in ganki ba sai ranar da dr. khalifa yabudi baki yace min "ke ce mace daya dayake so ya aura a duk fadin duniyar nan, a wannan lokacin ji nayi na tsaneki fatima duk da na san ba laifinki bane ba ke kika sa yasoki ba amma wannan baiyi tasirin daya Hana inga laifinki ba. Fatima tayi murmushi tace "ke ma ba ki da laifi ummi domin ba laifi bane don mutum ya yi kishin abinda yake so, ballantana soyayya irin ta ki ga dr. khalifa, hnkalina ya tashi don sabon danayi dake ta ina zuciyata xa tasake kin juya min baya, ummi inason ganin kin mallaki dr. khalifa don haka zn daure shi da jijiyoyin jikinsa tunda ya ce yana sona to ya kawo kansa garemu, kiyi hakuri da duk abinda za kiga yana nuna mini na so, kafin mu cimma burimmu, kuma kibashi hadin kai a duk maganar dazai miki a kaina ki nuna mai kin goyi bayansa, xai kasance yana son magana dake sbda hirata da kuke. Nan take ummi taji zuciyarta ta yi mata wasai, kaunar fatima takaru a zuciyarta, tafasa hada kayanta tabar gdan kamar yadda tayi nufin yi, bayan tafiyar fatima gda takira wayar hajiyarta tashaida mata yadda sukayi da fatima, hajiya tace "anya kuwa dagaske take ummi ? kada fa tayaudare ki, sai wahala ake awai wata manufa a zuciyarta. Hajiya tace "to ki dai yi taka tsan tsan kuma kisan yadda kikayi kika kawo mana abubuwan da malam yace a kawo wadanda suka shafi khalifan. ****** Cikin dacin rai fatima tadawo gida tana takaicin son zuciyar dr. khalifa duk da ta san ba zaiyi nasara a kanta ba amma abin yana ba ta haushi sosai, ga mamakinta sai ta iske mama da anty sadiya a gdan na su suna hira da inna ga zogala a gabansu suna ci. Ta fadada fara'arta tace "lah mama dama nan kika shigo. Tace "eh amma mun biya kasuwa kafin mushigo nan din. Inna tatashi tace "bari in tuka tuwon nan in hada miya in dawo. Mama ta ji dadin fitar inna tace " 'yammata na zo ki zauna anan kiji wata magana. Daf da ita fati tazauna tace "wannan zuwan na ki ne don gunki muka zo. Tace "ni mama. Tace "kwarai kuwa fatima ko baki kai matsayin daza muzo gunki ba. Tayi kasa da kanta tana girgiza kai, mama tace "fatima munzo da kanmu ne nan dan kidauki abinda mukazo miki dashi da mahimmanci, a wani lokacin idan za kagawa mutum abu mai muhimmanci to kadubi yanayin dazaka fada masa dan yafi kama batun da daraja. fatima na san matsayin uwa nake a gunki ckin gdan nan na san bbu abunda xan nema in rasa shi sai fa in ba ku dashi. ko da yake maganar danazo miki da ita mai nauyi ne amma duk da haka nauyinta ba zai hana in gaya miki ba, sbda na san wacece ni a gunki, ba kuma ina nufin yin amfani da wannan damar bane in tursasa ki ba a'a alfarma ce nake fatan kiyi min. Fatima dan uwanki khalifa ne ke neman alfarmar ki amince mai ya aureki sbda ke kadai ce zuciyarsa ke so, kuma ta aminta ya aura. Tunda mama tafara magana fatima tasan inda tadosa, dataji ta yi shiru tace "mama duk abinda kika fda haka yake, kuma alfarma kowace iri zan yiwa kowa a gdanku amma a wannan karon sai dai in ba ki hakuri mama abu guda daya ne zai hana in amsa wa yaya khalifa soyayyarsa itace ummi. Ummi kuma fatima ? Me ya kawo ummi ckin wannan maganar ? Fatima tagyara zama tace "mama ummi itace za tayiwa yaya khalifa shamaki dani domin kuwa ta fi karfin in auri wanda maitar so da farautar nema, ummi tana tsananin so da burin auran dr. khalifa ,da wani ido xan dubeta in na aureshi,in banda haka da a yau dinnan xan tabbatar miki da matsayinku a gareni mama ta hanyar amsar bukatar dr. khalifa, kiyi hakuri mama ki taimaki rayuwar ummi ki ceto zuciyarta daga halin datake ciki ta hanyar sa khalifa ya aureta, mama kin zo gdan nan ne nasan sbda ttausayn sa di kikeji da gudun fadawarsa wani hali idan bai samu yadda yake so ba, mama to kisani ummi ta fidr. khalifa kuncin zuciya don shi a cikin kwanaki kalilan yake fama da ta shi damuwar yayin da ita tadade tana fama da damuwa, akwai daran datake kwana kuka akwai ranakun da ko abinci ba ta iya ci, ,kullum ciwon rai ke damunta akan dr. khalifa, in dai akwai abin tausayi ta fannin soyayya to ummi ce, kiyi hakuri mama kituno hadisin manzon rahama (SAW) da yace imanin dayanku ba ya cika har sai ya kasance yana sowa dan uwansa abinda yake sowa kansa. A DAREN FARKO 21 A cikin uwar dakin mama ita da anty sadiya ne ke zaune suna fama da magana daya dai dataki karewa, khalifa yashigo fuskarsa ba walwala yazauna kan stool yana fuskantar mama yace "gani" Tace "khalifa don Allah kayi hakuri da batun fatima ba za ta amince da batun auranka batunda dai har nataka kafata har ckin gdansu na roki alfarmarta bata amince ba, karshe ma tashiga kawo min wa'azi wai yadda naji tausayinka a matsayinka na da na har nake fafutukar ganin ka samu abun da kake bukata to itama ummi in tausaya mata in taimaketa ta aureka. Khalifa yaja dogon numfashi yace "wlh mama ni ma bansan abunda ke damuna ba, na kasa hakuri da yarinyar nan wani irin abu nake ji a cikin zuciyata kamar idan ban samu auranta ba mutuwa zanyi, ina jinjina wannan yanayi danake cki mama, a ni kaina ba na ra'ayin auran zumunci ba zan auri ummi ba, fatima kuma yanzu nafara sonta ki ci gaba da kokarin taimakona da addu'a da duk abinda za ki iya mama. Wayarsatafara ringing yatashi yafita, mama taja tsaki tadubi sadiya tace "to yanzu me za muyi, nikam ban san abinda za a zarge ni da son zuciya, ba na son in ja wa kaina zagi. Sadiya tace "kidaina damuwa mama in fa fati matar khalifa ce sai ya aureta, dole muci gaba da jan ra'ayin fatima tunda ita yakeso itace farin ckinsa. Bayan dr. khalifa yagama wayar da aka kira shi dakin ummi yanufa tana zaune tana duba wani littafi, ta amsa mai sallama cikin fara'a, yazauna gefen kujerar dake gaban madubi ya amsa gaisuwar tayi masa yace "ina fatima? Tana gdansu. Ya gyada kai "ummi" Ta amsa "na'am yaya khalifa. "Ba ki da wata hanya daza ki iya ja min ra'ayin fatima, ina sonta dayawa fa. Ba karamin namijin kokari ummi tayi ba gun shanye damuwarta da tsananin kishi? ta tace "yaya khalifa tunda dai kana son fatima zan taim*e ka kasameta, ko ba komi dai na godewa Allah dayasa kakejin irin abinda masoya keji a zuciyarsu yayin dasuka rasa masoyansu. Bata jira abinda zaice ba tamike tace "bari ma inje in zo maka da fatin. Ya bita da ido har tafita, ya ji ciwon maganar data fada masa na karshe amma babu yadda zaiyi soyayyar fatima ce taja masa, in bar da haka har ummi ce ta isa tagaya mai magana, yaja tsaki yayi tagumi. dr. bashir ne ke dada karfaf masa lallai yanemi taimakon ummi maganarta na da tasiri sosai a gu? fatima kada yadamu da abinda zaiji yagani domin duk abinda kake neman nasara a kansa sai ka yi hakuri, ba abi? da yatsana irin raini, Allah yasa ba alhakin 'yammatan daya wahalar ke bibiyarsa ba. Yana ckin wannan tunanin fatima da unmi suka shigo dakin idanunsa akan fatima yaji wani irin sanyi a ransa kamar yatashi yarungumeta nan take yakara sallamawa al'amari ummi a gun fatima, bai dada tabatar da haka ba sai da fatin tarusuna ta gayar dashi tace "ga ni yaya khalifa. Ummi tace "yawwa nikam na gama aikina, ke fatima kinsan dai yaya khalifa yayanmu ne. Ta gyada kai tace "na gane anty ummi. Bayan fitar ummi, dr. khalifa yakamo hannun fatima ya mikar da ita tsaye ya kura mata kyawawan idanuwansa masu laushi da daukar hankali, nan take yafara jefa mata wani bakon al'amari a zuciyarta, nan da nan tayi kasa dakanta tana jan numfashi dakyar, lamarin dayasa takasa cigaba da tsayawa ta janye hannunta ta zauna, yazauna daf da ita yace "haba fatima dago idonki kidube ni mana, wai meye aibuna da ba kya son kallona? Ta maraice murya tace "don Allah yaya khalifa kaji tausayin ummi ka amsa soyayyarta tana sonka dayawa, kayi hakurin fiddani daga zuciyarka, an riga an ba da ni kwanaki kadan suke rage nazamo matar wani.... Yasa hannu yatoshe mata baki yace "in kina son in a; hi batunki dago ki kalli kwayan idanuna. Ba ta son kallon idonsa sbda idon na sa daban yake dana sauran maza, amma bukatarta datake son tabiya yasa dole tawatsar da abinda takeji tawarware idonta ta dubeshi, ya lumshe ido yana mata kyakyawan murmushi, tamaida kanta kasa yace "fatima idan fa kina son in yi miki yadda kike so sai dai kiyi ta kallona har sai na ce kidaina. Tun fatima na zamewa kallon na sa har tafara rikicewa domin wani irin yanayi tafara ji a jikinta wanda bata taba jinsa ba, yakara matsowa daf da ita yasa hannayensa biyu yadafa kafadarta, "wlh ina sonki fatima inajin kihar ckin jijiyoyin jikina don Allah fati kada kibari kirasa ni kada kibari in rasaki, fati duk wanda yayi ceton rai... Yakasa cigaba da maganar sakamakon wasu siraran hawaye dasuka shiga zubo masa, lamarin dayasa fati tarude tana fadin "meye abin kuka khalifa ? Yace "ke ce bakiga abin kuka ba. Yasaketa yamike, tamike itama tatsaya a gabansa takasa magana, sun jima a haka daga bisani yafice daga dakin yana cigaba da sharar hawayensa, yawuce mama a falo yafita, gabanta na faduwa sbda ta ga yanayin daya fito nan take tsoro ya mamaye zuciyarta. A cikin dakin fatima sororo a tsaye tana tunanin khalifa, karo nafarko dataji tausayinsa ya kamata, ta yaya za tayi da wannan al'amarin, abinda
Chapter 26 · 0% Book details