← Book details A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 50

Sashe 36

A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

b a yi maka akan wani abin ba sai an yi a wani abin shiyasa idan mutum yagane to yasa*i ransa yayi komi kansa tsaye kawai yahuta, mutum ya fuskanci Allah a cikin al'amarinsa to karya damu da surutun mutane. Mama tace "kai sadiya duk fa yadda za ki kare abin nan ba zan fasa cewa Khalifa yayi son kai ba. Tace "to mama shi yace sai an ba shi ta karfin tiya? muna zaune fa aka ce an bashi to sai ya ki karba don kada mutane su ce ya yi son kai? A bisa dole mama tahakura don bata samu goyon baya ba ta kowanne fannin, dayake harka ce ta masu kudi duk da kasancewar baa gayawa yan uwa ba tun auran da wuri ba amma daga lokacin da aka fara bada sanarwar daurin auran gdan yafara cika da mutane maza da mata yan taya murna. Ummi tana gdansu tun lokacin da dr. khalifa yafito daga asibiti ta tabbatar za a yi auransa da fatima ta karasa rikicewa hankalinta a tashe tajewa hjiyarta da labarin, ta bayyana mata duk yadda abubuwan suka faru tace "Hajiya mama da abba babu abunda suke sosai farin cikin dansu, Abba da kansa yaje ya sanar da mahaifin fatima halin da dansa ke ciki a kan yarsu, suka taho asibitin da niyyar dubashi lamarin dayasa musbhu yace ya barwa khalifa fatima sun manta ina son khalifa tun kafin yaso fatima, bbu wnda yadamu da hlin danake ciki ana nan an fara shirye shiryen auran gadan gadan. Hajiya tashare mata hawaye tace "Daina kuka ummi in dai ina raye a gdan duniya nan zanyi miki maganin damuwarki, ba zan taba cewa kidaina son khalifa ba don ita zuciya ba a rabata da abinda take so a zauna lfya, idan har muka hakura da khalifa to mata muka rako duniya, wannan dogon lokacin damuka dauka muna nemansa ba zai tashi a banza ba, tashi mu koma gun malam. Ummi tadanyi jim sannan tace "hajiya bai dace mucigaba da wahalar da kammu a gun zuwa gdan mlami ba da wahala idan hakan zai amfanar damu tun da a baya bai mana amfanin kmi ba. Hajiya tafiddo ido tace "ke saurara nsara a hankli samunta idan lokacin samuwarta ya zo za kiyi mamakin aikin malam, ke de muje muji ta bakinsa, motsi ai yafi labewa, bari in karasa miyar can yunwa nake ji.A DAREN FARKO 30 A wannan rana aka sallami dr. khalifa daga asibiti duk da ba jin sauki yayi ba ko a ganin ido idan ka dubeshi ka san yana fama da ciwo irin na zuci wanda fuska ke bayynar da shi, bbu wanda ya samu bakin tattauna wata magana sai da suka dawo gida gaba daya. Jikin fati a sanyaye ta bi iyayanta zuwa gdansu gaba daya a razane take domin fuskokin iyayanta sun nuna mata akwai babbar magana wadda ba za ta taba yi mata dadi ba, ta zauna lakwas a rumfar inna tana jiran abinda za ace mata musamman ganin yadda malam musa yazauna ya lankwashe kafafu yace "fatima ai kamata yayi tunda kin zabi khalifa sai ki koma gdansu da zama a yi bikin na ku a can ko? Inna tace "Ni ma haka na gani malam. fatim tace "Don Allah baba kuyi hakuri kada kuyi fushi dani, ba ni nace musbahu yafurta ya hakura dani ya barwa khalifa ba shi yayi niyyar kansa. Inna tace "ke da Allah rufewa mutane baki waye sa'anki a nan da za ki zo mana da wannan maganar ta bnza da wofi, da ace ba ki nuna ra'ayin khalifa kike ba musbahun zai fadi haka, misbahu ya san ciwon kansa kuma yana kishin kansa dole yace ya hakura domin ba zai zauna a walakanta shi a banza ba. Malam yabude baki zai yi magana wani kanin fatima me suna ibrahim yashigo yashaidawa malam cewa ga abba can a waje yace yana son ganinsa. Tsaki yayi yamike yafito, ya umurçi Abba daya shigo zaure, ibrahim yadebo kujerun zama na roba suka zauna suka ka ra gaisawa. Alhaju mahammadu yace "malam na yi wa khalifa iyakar nasihar dazan masa Alhamdulillahi kuma ya fahimceni ya amince da nasihata ya hakura da fatima, na yi hakane sbda dogon nazarin da nayi a kan al'amarin don Allah malam kuyi hakuri kada kuyi fushi da fatima, fushin iyaye ba ya taba gyara sai illa, a bata goma daya bata gyaru ba, idan kukayi fushi da fatima al'amarin ne gaba daya zai lalace ba za asamu mafita ba, idan dai za muyi hakuri mu klli rayuwar yadda take tafiya cikin yaran bbu wanda yake da lifi face haka Allah yakaddara, kowane mutum da Allah ya halicce shi yarubuta abinda zai faru dashi a rayuwarsa kuma babu wanda zai kaucewa wannan kaddarar tasa. Kan malam na kasa nauyin maganar Abba sun masa nauyi aka har sai da yaji kunya ta kama shi sosai wato Abba ya fahimci ba sa son ba wa khalifa auran fatima shi yasa yadanne damuwarsa duk yadda yake son khalifa ya auri fatima ya hakura, ko kusa bai cancanta suyi wa Alhaji muhammadu haka ba duk yadda mutumin kirki yake mai son mutane da kula da hakkin makotaka yakai Alhaji sai son barka yana samun yabo a bakunan mutanan unguwar, su kam alhaji babu abunda bai yi musu ba ko kusa bai cancanta suki dansa ba. Ya daga ki yace "Don Allah alhaji kar kayi tsammanim hana khalifa fatima nake son yi. Abba ya katse shi da sauri yace "wallahi ba haka nake nufi ba, ko a baya damuwar da khalifa ke ciki tasa idona yarufe na shagala daga baya nayi nazari na sawa zuciyata hakuri. Malam yace "Alhaji na gamsu da bayananka na yi fatan Allah yasa haka shi yafi alheri garesu gaba daya, na bawa khalifa fatima. Abba yace "don Allah abba kada kayi hushi da ita albarkar auran nan ake nema in dai kuna fushi da fatima wannan albarkar ba samuwa za tayi ba. Sai a lokacin xuciyar malam ta dan sassauta daga damuwar da yake fama da ita, bayan tafiyar Alhaji ya dawowa inna da bayanin abinda abin da abba yazo mai dashi, inna tace "kai ni dai kam ba zan fasa fadar cewa wannan abu bai yi min dadi ba, to idan ma naboye ban bayyana a bakina ba Allah na gani xuciya b dadi . Malam yace "ba komi. mu barshi a haka Allah yakaddara din mu yi fatan alheri ,fushi ba namu bane. fushin mu ba zai yi maganin matsalar ba face yakara jagula al'amarin, duk yadda zamuyi ba za mu ba musbahu fatima ba tunda Allah bai kaddara matarsa bace. Tace "to malam yanzu ina musbahun? Yace "Ni tunda yafita daga asivitin nan ban kara ganinsa ba, ban san ina yayi ba wayarsa ma gashi a kashe take tun da muka dawo banganshi ba nake ta kiranta bata shiga ba. Inna tayi tsaki tace "Duk fatima ce taja tun farko in da bata ba khalifa fuskar yaso ta ba zai so ta? mutumin da ya san an yi masa baiko ina shi ina kula wani namiji. Fatima ta ban mamaki Allah malam wannan halayyar arota kawai tayi ba ta ta bace, ina matukar jin kunyar yaron nan yagama sawa ransa ba shi da mata sai ita lokaci guda ace yarasa? haba ai abin da ciwo. Fatima dai na daga dakinsu tana ji bata ji dadin abubuwan a ranta amma soyayyar da takewa khalifa tasa tashare komi in dai za ta samu cikar burinta akan dr. khalifa xancen ya kare. Yawan kuka datayi ya haifar mata da zazzabi da ciwon kai, tasamu babban zani ta kudundune kanta a ciki tana wasi wasi wayarta tafara ringing ganin nomban khalifa yasa tadaga dasauri. Muryarsa a sanyaye yace "Fatima me ki ke yi yanzu? Tace "A kwance nake zazzabi ne yarufeni. Yace "Subhanallahi *in sha magani? Tace "yanzu dai zan sha. Yace "zan iya zuwa in ganki? Tayi shiru, yace "ko akwai matsala? Tace "Gani nayi ba ka da lfya. Yace "na ji sauki tunda na sameki dama rasaki da naga da gaske zanyi ne yaja min ciwo, lokacin danaga wannan katin na tabbatar na rasaki sai naji gaba daya duniya ta min kunci, abin cikinta ma ya min kunci, hankalina ya tashi gaba daya na kasa mallakar kaina, ,na yi kokarin in daure damuwa ta ta kai matakin data kai amma da yake ba ni ne nasa kaina a damuwar ba hakan bai yiwu ba gareni dole sai da kowa ya fahimci matsalata da farko na yi zaton mfarki nake ashe gskia ne don Allah fatima ki nemar mini iso gun inna da malam su amince in ganki zuciyata ba ta da juriya a kanki ba zan iya jurewa rashin ganin ki ba. Fati ta runtse ido tabude tace "Ba komi kazo gdan kuma zan fito zaure kaganni. ***** A gdansu Dr. khalifa xanceb da ake ta nanatawa knan za a daura auran khalifa da fatima nan da kwana biyu masu zuwa, reshe ya juye da mujiya ,nan da nan Abba yashiga kiran abokansa da yan uwa a waya yana shaida musu batun daurin auran dan lelen dansa biki daisai bayan sati daya domin ba abu ne na wasa a tare dasu ba, auran khalifa abin alfahari ne a tare dasu sai kowa yasan ana yi, mama ce dai bata nuna farin cikinta sosai sbda ta tsani abinda za ace ta yi son kai ko son zuciya wanda tabbas ta san sai an fada,anty sadiya tai ta tsaki a ranta. Ko yushe tananuna mata cewa aure nufi ne na Allah babu wanda za ya auri matar wani, Allah yayi fatima matar dr. khalifa ce dole shi zai auri matarsa, surutun mutane ba karewa yake ba duk yadda kaso da taka tsantsan dinka sai an yi surutun, idan b a yi maka akan wani abin ba sai an yi a wani abin shiyasa idan mutum yagane to yasa*i ransa yayi komi kansa tsaye kawai yahuta, mutum ya fuskanci Allah a cikin al'amarinsa to karya damu da surutun mutane. Mama tace "kai sadiya duk fa yadda za ki kare abin nan ba zan fasa cewa Khalifa yayi son kai ba. Tace "to mama shi yace sai an ba shi ta karfin tiya? muna zaune fa aka
Chapter 36 · 0% Book details