Sashe 30
A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
za yi alfahari da auranta, Allah yasa haka shi yafi alheri. Anty sadiya tace "to Alhajin ya yiwa mahaifin fatiman magana ? ni na fi son ayi komi a gama hankalin kowa yakwanta. Mama tace "eh da magribar dazu ya ce idan yafita masallaci zaiyi wa malam maganar zan tambaye shi in ji yadda sukayi, na san dai da wahala in za su ki. A hankali ummi taja jikinta tadawo dakinta zuciyarta na azalzala mata tamkar za tafashe, tabude wayarta ta binciko wani kyakyawan hoton khalifa data faki idonsa ta dauke shi bai sani ba tadauke shi a falo, yana sanye da kananan kaya dasuka matukar karbar jikinsa, murmushin da yayi ya dada kayatar da kyaun hoton. wata rana tazauna tazubawa hoto ido, fatima ta iso kanta bata sani ba, ta jima tsaye tana kallonta ganin bata motsa ba fatima tazare wayar tana fadin "wa ki ke kallo haka ? Ummi tamike takwanta bisa gado tana dariya tace "wa kika san zan kalla in banda sahibi na. Fatima tadubi hoton tace "yayi kyau kam amma zan ba ki shawara. Tace "tame fa yar kawata ? Tace "ummi ina matukar jin tausayinki game da al'amarin khalifa, kina sonsa da yawa kada ki ja wa kanki wahala yayin da so ya tsananta a zuciyarki don Allah ki dinga bi a hankali yadda za ki iya daukar duk abun da zai faru me dadi ko akasin haka. Murmushi ummi tayi tace "hakane fatima amma za ki iya fada min dalilin dayasa kika min wannan nasihar ? Tace "ba wani abu ne yasa nace haka ba illa la'akari da yanayin khalifa anya wannan zai tsaya kan mace guda daya ? idan ma bai ce yana so ba sai ance ana son shi, wata rana idan bai amince ba watarana zai amince amfanin shawarar dana ba ki itace idan kin bi komi a hankali sai komi yazo miki da sauki. Ummi tace "fatima wai don Allah kina ganin zan samu dr khalifa. Tace "ummi wannan lamari ne na Allah babu w ? da ya isa ya yanke hukunci sai shi, za ki iya samun sa za ki iya rasa shi, ba komi mutum yake nema yasamu ba Ummi ta rausayar da kai tana dan murmushi tace "fatima don Allah idan ke ce xa kiyi hakuri da khalifa akan soyayyar danake masa ? Fatima tayi dariya sosai tace "ummi kin ganni nan wallahi har yanzu ban san meye so ba. Ummi tafiddo ido "fati wace irin magana ce kike haka ? meye matsayin musbahu a gunki knan idan dai baki san meye so ba. ? Fati ta tabe baki tace "musbahu zabin iyayena na, ba na fatan ganin ranar da zan sabawa umurnin su, shi yasa na tallafe shi hannu bibbiyu kuma na yi damarar rike shi da kyau in dai batun so za ayi to ban san me akeyi idan ana son mutum ba. Ummi tace 'Don Allah dr. khalifa ya taba birgeki ? Tayi mata wani irin kallo tace "ni dai na yarda har zuciyata khalifa ya isa namijin da za a so shi, ko da nace bn san so ba, na san cikakken namijin kuma na san namijin dazan kalla in ce ya hadu, shi yasa ba ni ganin laifinki don kina damuwa da khalifa face ina jan hankalinki don ki dauki komi dasauki... Ummi ta buga kwafa, lallai ba abin mamaki bane don fatima ta amince ta amshi soyayyar khalifa, sai dai ita tana tausaya mata don ba karamin kuskure tayi ba. A DAREN FARKO 26 Ba karamin tashin hankali inna tayi ba lokacin da fatima da kanta ta zauna tana yi mata wani mamaki wanda yabata mamaki, kallon fatin take kamar ba ita ba, tun tana fada har ta dawo yi mata nasiha amma fati ta murje idanunta kukan da take ma yau batayi ba don tsakaninta da Allah so take inna ta amince da abinda take fada mata. Inna tayi tagumi tana kallonta tace "maimaita min abinda kika fada. Fatima tace "inna kiyi hakuri ni na san wannan magana ba za tayi muku dadi ba amma kuyi hakuri ku karbeta a matsayin abinda Allah ya kaddara mana ni daku, inna don Allah kiyi hakuri kada kuyi fushi dani nima ban taba tunanin zan bijire wa auran malam musbahu ba sai a wannan lokacin dana samu kaina a cikin yanayin da ban taba tsammaninsa a gareni ba, tayi shiru ta kasa ci gaba da magana ganin yadda inna ta tsareta da ido kamar za ta shaketa. Fuskarta a tsuke alamun fushi da zuciyarta ke ciki, jin shirun ya yi yawa inna tace "kici gaba mana tunda bakiji kunyar fara fadar wannan maganar ba ba wani dalilin dazai sa kiji kunyar karasawa. Kan fati na kasa bakinta ya mata nauyi ga maganganu na cinta ta kasa karasawa bayan ta zauna a gaban innar ne cike da azamar fada din sbda ance barin kashi a ciki bai maganin yunwa. A daran jiya ne da barci ya gagari idanuwanta ta kwana tana juyi kamar zuciyarta xa ta tsage, ta yanke shawarar idan gari ya waye za ta tari inna da maganar duk abinda zai faru yafaru, itama a halin yanzu tasan meye so ta san abinda ake nufi da ciwon so. Bayan tayi duk sallar asuba tazauna shiru tana tunanin ta yadda za tadubi tsabar idon inarta ta shaida mata cewa su yi hakuri su bata khalifa shi take so, ba wata manufa data wuce hakan amma akwai tashin hankali mai yawa a cikin al'amarin da ban tsoro, iyayanta suna matukar kaunar musbahu kamar su suka haife shi, ba sa wasa da abinda ya shafe shi, kamar yadda shima yake matukar sonsu da kula da al'amarinsu, ko da su suka haifeshi ba zai yi musu biyayyar da tafi haka ba ko da yaushe malam yashiga yafita maganarsa musbahu, duk abinda za ayi a gdan musbahu ne zai ce yayi, shi kuma ba ya kasa a guiwa gun aiwatar musu da abin da suke so ko meye shi kuwa, in dai ba wanda yasani ba ba mai cewa musbahu ba dan gdan bane, ta ina iyayanta za su amince da damuwar musbahu, damuwa kuma irin wannan. Idan fatima takalli girman son da takewa Khalifa sai ta tuna matsayin musbahu a gun iyayanta ba karamin tashin hankali bane a yanzu tace zata juyar da ra'ayin iyayanta daga auran musbahu zuwa khalifa. Tana cike da wannan rashin kwarin jiki da karayar zuciya taci gaba dakulla shawarwarin yadda za ta tunkari inna da maganar kafin ma malam yaji wanda yafi kowa son musbahu. Da gari yagama wayewa tafito tsakar gida duk sanda suka hada ido da inna sai gbanta ya fadi, lokaci lokaci takan faki idon inna tagoge kwallar dake taruwa a gefen idonta, innar ce tagaji takira ta daki tazaunar da ita tace yau sai ta gaya mata abin dake cin zuciyarta wanda yasa tadaina walwala. Ta mayar da kanta kamar bakuwa a gdan, da farko shiru fatin tayi tana sharar kwalla, inna tace "uhum ta yaro kyau take ba ta karko, babu abi ? da zai sa ki tashi a gun nan sai kin min bayanin abinda ke rufe min zuciyarki.... A kofar gdan malam musa, Alhaji muhammadu mahaifin khalifa ne zaune kan tabarma, shima malam din suna hira, musbahu yafito musu da kunun ayar da inna tahada musu yayi sanyi sosai yana ta kamshin kayan yaji, suna sha suna ci gabada hira. Abba yana son gayawa malam abin da ke tafe dashi kunya ta kamashi yarasa ta ina zai faro maganar, bai yi tunanin zaiji nauyin maganar da take ta damun zuciyarsa ba, bai san me xe ce da Khalifa ba idan yakoma gda a haka har suka gama hirar yabar gurin zuwan gdansu, ai kuwa khalifa ya iske shi a falo tare da mama ta tare shi da tambayar "Abba ya kuka yi da malam din!? Ya fidda babbar rigarsa da hula ya ajiye yazauna. Khalifa naje na kasa gaya masa, ban san dalili ba naji bakina ya rasa yadda zai furta maganar khalifa me xai hana ka daure kayi hakuri komi na Allah ne. Mama tayi farat tace "yawwa abba don Allah kadinga nuna masa hakan irin wannan son kan ba shi da dadi. Khalifa ya kwantar da kan shi a jikin kujera yace "abba ni zanje dakaina in sami mala.m din in gaya masa, ni bakina ba zai ji kunyar fada ba, wannan yarinyar ba zan taba iya hakura da ita ba a rayuwata don Allah kuyi hakuri ku ci gaba da tayani addu'ar Allah yasa auran fatima alheri ne a tare dani. Yamike zai fita abba yace "kayi hakuri kar kaje zan kara yin tunanin akan al'amarin. Murmushi yayi yafice. Yana fitowa harabar gdan yakira fatima a waya yanayin dayaji muryarta ya tabbatar itama tana fama da damuwa. Bayan sun gaisayace "a ina zan ganki? "kazo gdammu kawai ina son kowa yatabbatar ina snka kuma na amince dakai. An gama gimbiyar mata. Inna da malam, zaune a tsakar gida suna hira ,khalifa yayi musu sallama, cikin fara'a sosai suka amshe shi ya tsuguna suka gaisa nan da nan kamshin turaransa ya game gdan, farar shadda ce a jikinsa sai walwali yake, yace "inna yaya naganku a duhu? Tace "khalifa ai ka san ba kullum suke kawo wutar ba? Yace "ba injin a gdan nan? Sukayi shiru, yace "idan Allah ya kaimu gobe za a kawo muku injin. Malam yace "Don Allah khalifa kudaina mana hidima haka abin ya yi yawa. Yace "haba abba meye amfanin arzikin da ba za a taimaki al'umar musulmi dashi ba, mu dai a dinga sanya mu cki? addu'a yanzu ma bukata nazo da ita gareku. Malam yace "in dai bata fi karfinmu ba insha Allahu za muyi maka kai da mahaifinka kunfi karfin komi a gdan nan. Kansa na kasa yace "baba dazun abba ya zo gdan nan da nufin isar da sakon dana turo shi dashi gunka amma ya koma yace min ya kasa gaya ma, shi ne ni nazo in fada maka kuma in roko alfarmarku. Malam musa yayi murmushi, "amma alhaji ya ba ni. mamaki yanzu har akwai abinda zai ce yaji nauyin gaya mana, ni dashi ai mun zama daya fada min khalifa ko meye in dai mallaki na ne zan maka